NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 40 of 98

na dira ƙasa daga kan gadonsa, domin zuwa wannan lokacin dukkan wani tashin hankali ya gama bayyana a zuciyata da gangar jikina. Duk tsoro ya gama cika ni, idona ya taru da ƙwalla yana shirin zubar da hawaye, Dama ni Allah ya horen ruwan hawaye kamar ruwan famfo, sai na koma kamar wata taɓaɓɓa, kaina fa ko ɗankwali babu kuma ba a yanda nake ɗazu ba da rigar t-shirt a jikina, wannan riga ce doguwa aka zumbula min ta atamfa, bama ta ɓangarenmu bace, don ko Gwaggo rigar nan tayi mata yawa, sai dana ƙare ma ta kallo kana na tuna atamfar sallar bara da Baba yayi mana, kenan ta Umma ce ma, ƙofa na nufa gadan-gadan sai na jita a rufe da key. Zubewa nayi a wurin na ɗora hannu aka na kurma ihu ina faɗin, "innalilllahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga ukuna Gwaggo tah, wayyo Allah nah shikenan Yaya Haidar ya ɓata ni, Gwaggo kizo ki taimaka min, ya rufe ƙofar, kizo kar ya ƙarasa abinda bai cimma ba". Ihu nake sosai ina shure-shuren ƙafa kamar ƙan-ƙanuwar yarinyar da aka hana shan nono. Jin yadda nake kurma ihu ina buga salati cikin fizgar numfashi, shi ya farkar da Yaya Haidar, Ganinsa nayi a gabana a tsugune don ko tasowarsa ban sani ba, ƙoƙarin saita min yanayin da nake ciki yake, kallon da yake min sai naga kamar da tsoro a cikinsa, abinda yake kawowa a ransa daban, abinda nima nake kawowa a nawa ran daban. sai matsawa baya nake ina ƙanƙame jikina, shi kuma yana daɗa matsowa kamar zai shige jikina, amma fa gefe guda idan na gasgata abunda idanuwana ke gani cikin idonsa tausayi ne tsantsa, sai dana kai maƙura a mannuwa da jikin ƙofa kana na haƙura, jikina nata karkarwa, wallahi tsoronsa nake sosai, inda za'a auna jinina a wannan yanayin tabbas jinina ya hau, shima ɗin sai daya kawo gab dani numfashinmu na gauraya dana juna tukunna naji ya kamo hannu na guda ya damƙe, ya ɗaga kofin ruwan dake ɗayan hannunsa ya watsa min, ba shiri na rumtse idona tare da kurma wani sabon ihu ina roƙonsa. "wayyo Allah nah, Allahumma ajirni fi musibati waklifni kairan minha, don girman Allah Yaya Haidar karka kuma yimin komai, kaga dai ni ƙanwarka ce". Sakin hannuna da yayi shi ya dakatar da ni daga ihun da nake kwaɗawa, ban dai buɗe idon ba sai shashsheƙar kuka da nake ina daɗa faɗin, "Yaya Haidar babu kyau kaji tsoron Allah, duk wanda ya ɓata ƴar wani shima za'aiwa tasa bare ni da nake ƙanwarka, idan ka lalata min rayuwa kai kanka ba zaka sami kwanciyar hankali ba, ka saka rigarka bana son ganinka a haka, babu kyau kallon tsiraicin wani, ko riƙe hannuna da kayi haramunne...". Saukar marin da naji a kuncina ya katse sauran surutan da nake, a zabure kuma na miƙe tsaye ina rarraba ido ina neman hanayar fita, dan duk Yaya Haidar ya gama razana ni. kuma cikin abunda bai wuce sakan huɗu ba naji murya na fita da ɓacin rai yana faɗin,"wallahi idan ba ki rufe min wannan shegen bakin naki ba sai na zare belt na zane miki jiki a wurin nan, mahaukaciya kawai, an gaya maki kowa ɗan iska ne irinki". da ƙyar na iya saita idanuwana na tsayar dasu wuri ɗaya suka tsayar da kallonsu akansa, na gwame fuska zan sake fashewa da kuka, ina dukan ƙafana a ƙasa raina na sosuwa, naji haushin ƴar iska daya kirani, to amma babban baƙin cikina daya gama ganina, abunda ba nasa ba ya gama kallewa mai shi, kai Allah ya isan mai shi, nasa hannu na goge bakina kamar yace min yayi min kiss. Bani da tabbas ɗin abinda nake zargi, banda kuma wata hujjar kafawa akan hakan, kawai dai ganina da nai jikinsa nake jin kamar komai ya faru, dan haka kawai ba zai kawoni ɗakinsa ba, ɗakin ma kan gadonsa kuma ajikinsa. saina daɗa ƙanƙame ƙirjina wanda wuyar rigar yay min yawa, na zumɓuro baki gaba ina hararsa ta ƙasan ido, shi kuma ya saki wani munafikin murmushi daya tsaya iyaka leɓensa, ya juya yaci gaba da saka maɓallan rigarsa. "tsakani da Allah Yaya Haidar me kayi mini?". Na faɗa ina zubar hawaye. "ni me zanyi da wannan ƙazamin jikin naki?, Ki dai tambayi aljanun kanki dalilin da yasa suka zo min ɗaki". Na kalla jikina nace, "ni ba ƙazama bace, Kuma ba mai aljanu bace. Lafiyata ƙalau, kuma indai ba kaine ka kawo ni ɗakinka ba wane zai kawo ni". na faɗa ina hararan bayansa kamar yana gani na. rashin amsa min da yay naci gaba da cewa, "to ma babu abinda kayi min mene ya kawo ni ɗakinka? Bayan ni bana shiga ɗakin wanda ba muharramina ba, ɗakin naka ma wai a jikinka. Gaskiya ni dai ka gama cutata wallahi, duk tanadin dana gama yi sai daka kusa rusa min, kawai kasani a jikinka bayan jikina ba naka bane". Bakina ya matse min da ƙarfi cike da mugunta, na rasa yanda zanyi na ƙwaci kaina hakan yasa na bashi mintsini a bayan hannu, babu shiri ya sauke hannunsa yana yarfewa, yana ƙarewa jikina kallo ya taɓe baki yace. "iina abin yake da har kike wani banzan tunaninki, ni ko da kuɗi aka haɗani dake aina fi ƙarfin wannan ƙazamin jikin naki... kuma wanne dare ne jemage bai gani ba kike faman ɓoye-ɓoye, karki manta a gabana kika girma, hasalima ni na fara saya maki pad, to maye ne ma za ki ɓoye min wanda ban
🏠