a tsinci kaina ina rayuwa ne ni ɗaya kawai...dan haka bana son kuma jin maganarki anan wurin ki wuce ki bar nan". na kawar da tsoronsa ina kuma kamo hannunsa, roƙonsa nake kamar tsohuwar mayya ina cewa, "Yaya kar kayi fushi ka duke ni, na maka alƙawarin ba zan kuma tambayan sunanka ba tunda baka so. Amma yanzu ka zo mu tafi gida, zamanka anan zai cutar da kai, ga warin bola ga sigarin da kake sha, abun yayi yawa". cikin wata razananniyar muryar ya ƙara ce min. "shekaruna goma sha tawas ina rayuwa anan Wurin, anan nake yini nake kwana, sigari itace abincina kuma itace abokiyar rayuwata, Allah shi ke tallafe da rayuwata, maƙociyata da nake jin daɗin mu'amala da ita wannan bolar, warinta shi nake shaƙa naji daɗi. Duk tsawon wannan shekarun ban cutu ba sai a yau da kika zo?, to wace ke? me kika isa ki sauya a rayuwar da Allah ya tsarata a haka tuntuni?...kinga ki shige ki tafi ki bani wuri tun ban maki rauni ba".
Tsantsar tausayinsa naji ya kamani, da wani firgici da kalamansa suka haifar min, saboda ganin yanda damuwa ta kuma bijirowa a saman fuskarsa, har yana maganar tana rawa kamar zai fashe da kuka saboda ɗacin rai. saina sauke kaina ƙasa ina goge ƙwallar da ta tarar min, wucewar sakanni uku na ƙara kamo hannunsa naja shi da ƙarfin da Ƙafafunsa basu iya yin gardama ba. yayinda a lokaci ɗaya naji ihun kukan jariri na ƙwala ƙara acikin kunnena, ƙarar kukan da yasani saurin gimtse ido, tare da damƙe hannunsa da ƙarfi babu shiri, inda hasken hoton wani jariri ke giftawa acikin duhun idona, sai naji kaina na wani mugun sarawa da wannan tsala kukan da jaririn yakeyi...wani abu da ban fahimta ba a lokacin shine, wataƙila anyi amfani da gatari ne wajen sara shi a tsakiyar kaina ya rabe gida biyu, ta yanda yin gaba da komawa baya zasu gagara a tare da ni.
****
_Hey Guyz how are you doing, hope you are all doing fine. how was the first charpter? loving the story already bah? encourage me by comments and voting, thats the only way i will know my effort is beaing appreciated...it's not a new story buh an old story am updating, i just changed the story name, kuma no disappointment insha'Allahu☺....ina fatan zan sami haɗin kanku daga farko har zuwa ƙarshe. Allah ya bani ikon gamawa lafiya, amin Ya Rahman...mai karantawa kuma Allah ya cire shi daga sahun mugwayen da zasu karanta littafi suƙi appreciating, dan mugunta ne da munafurci ai karatu aƙi appreciating, mutum sai ya nuna kaman bai karanta littafin, honestly speaking babu daɗi irin hakan...promise you ba zanyi delaying maku posting ba, so you people ma karku ji ƙyashin yin vote da comment.👏👏_
#love you my readers😘
#mikiyawriter's
#2022.
#Share.*AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(2)*
kusan daƙiƙa huɗu kaina na juyawa kafin na iya sakin hannunsa na ɗan matsa gefe da shi na dafa jikin gini. sama-sama nake jiyo muryan Furhana na faɗin,"wai Sabina kin san shi ne?". ta faɗa tana ƙarasowa inda nake. na buɗe idona da ƙyar na dubeta ina cewa,"a'a ban san shi ba, ban ma san waye ba". cikin ƙarfin hali nai magana ina dafe da kaina, ta matso kusa gareni da tashin hankali tana dafa kan nawa da shiga jera min tambayoyin,"lafiya?". a wannan lokacin babu abinda nake so irin a cire min kaina a dire shi a gefe, in yaso a barni naci gaba da rayuwa a haka idan da yiwuwa kenan, idan kuma har cire kan zai zama silar rasa raina to tabbas zaifi min sauƙi a cire shi dan na rabu da wannan tsananin sarawar da yake min, da kuma amsa kuwar kukan jaririn da har yanzu ban bar jinsa ba. "na shiga uku menene naga kina dafe kai? innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...kinga abinda kike neman jawa kanki ko Sabina, ni uban me ma kika gani da kika yo cikin bola sai kace mahaukaciya". muryar Farhana na fita ne cikin faɗa sosai da kuma tsananin nuna kulawa gami da matuƙar nuna damuwa. magana nake so nayi amma na kasa, sai laɓɓana dake aukin yin rawa, ko idona dake buɗe kaɗan dishi-dishi nake gani da su, jiri ya ɗebeni na nemi na zube a wajen tai saurin riƙeni ta zaunar akan bulo ɗin da Yaya ya tashi. hawayen azaba ya shiga min sintiri a saman fuskata, Farhana ma ko da bana kallonta amma a yanda muryarta ke fita da rawa nasan kuka ta ke, ta kama kaina tayi min adu'a, sannan ina jinta ta miƙe tana surfa zagi da bala'i ga bawan Allah'n dana san bashi da hannu a wannan halin dana shiga. ta dage akan sai ya faɗa ma ta abunda yayi min ko kuma ta kira masa ƴan sanda yanzun nan, shi dai bai saurareta ba dan banji yayi ma ta magana ba...kuma haka ta ƙyale shi ta dawo kaina duk a ruɗe tana ƙara faɗa masa wallahi komai ya sameni sai inda ƙarfin shari'arsu ya ƙare ita da shi, dan ba zata ƙyale shi ba.
da ace tasan irin azabar da nake ji acikin kaina, da kuma hoton dake haskawa cikin duhun idona, da bata tsaya tana wannan jarabar ba, kamani kawai zata yi mu tafi gida a sama min lafiyar ciwon da nake ji. "na banu ni Farhana, ban san me kika shigo yi wajen nan ba, yanzu duba matsalar da kika jawa kanki...yanzu me zan faɗawa Gwa