taɓa zuciyoyinmu. Tausayinta ya kamamu duka, lallashinta muka shiga yi har tayi shiru. sannan tace da Baba ya tashi ya tafi dare yayi, Baba ya miƙe yay mana sai da safe sannan ya fita. Ranar dai ban kwana a ɗakina ba, saboda Gwaggo cewa tayi bata yarda ba, bata san me zai iya faruwa ba cikin dare, haka dole na bita ɗakinta, har kuka sai dana yi dalilin hayaƙin da ta saka min, ita wai so ta ke su barni tun abun bai yi tsamari sosai ba, ganin zan cutu na miƙe zan bar ɗakin da gudu, ta damƙo ni dalilin harɗewar da nayi. Hawaye na sakko min nace, "Gwaggo don girman Allah ki ƙyale ni, wannan hayaƙin fa yana cutarwa". "ke dallacan rufen baki, ɗazu da baki hayyacinki da Haidar ya banka miki ai ba ki ce komai ba". "to amma yanzu ai lafiyata ƙalau. Allah likitoci na bayani sosai aka shaƙar hayaƙi". ta taɓe baki, Bata tankani ba ta lakuto wani mai a cikin kwalba ta shiga mulka min, gaba ɗaya warinsa babu daɗi, hannunta nake turewa tasa hannu ta make ni taci gaba da aikinta. Bata ƙyaleni ba sai dana sha maganin islamic kusan nawa, sannan ta barni. sai bayan da muka kwanta kuma ta ke min maganar cewar. "ni Hannatu yanzu nazo na kori Haidar da shigowa ɓangarena, idan aka sami matsala ko me zanyi dan ya kawo agaji ba zuwa zaiyi ba saboda akwaishi da ƴar banzar zuciya, lamarinsa yafi kama dana mahaukata, ba zai gane a ɓacin raine yasa nayi masa haka ba don ya kiyaye gaba ya gyara, to Allah dai ya rufa asiri". Ni dai ina jinta bance mata komai ba, har bacci ya fara ɗaukata naji tana tambayana. "yauwa ke ɗazu ice ko a iya tsotse miki baki Haidar ya tsaya?". Nayi kamar ba zan ansa mata ba, sai ta miƙe zaune tace, "idonki fa biyu kuma nasan kinji me nace". Ina turɓune fuska kamar tana gani na nace, "ehhh, bayan shi bai yi min komai ba". "to gwara da Allah ya tsayar a haka. Kuma dai kina jina da faɗan dana saba yi miki kullum, ki kiyayi ɗa namiji a duk inda yake, Shi iskancinsa ado ne, kina gani dai ɗazu a gabana saboda bashi da mutunci bashi da kunya ya nemi ya kuma maimaita miki, to babu ruwanki da shi tunda mummunan halinsa ya fito fili, kinga ke dai ba halinki bane rashin kunya, karki ce za ki soma, Duk abinda yayi miki ki kawo min ƙararsa ni zanji da shi, kina dai jin me yace idan kika kuma masa rashin kunya abinda yafi haka zaiyi miki, to yana nufin ciki zai ɗirka miki don haka ki kiyaye wallahi, kuma ni fita zanyi a sha'aninki nama bar muku gidan, atoh ni gaskiya nake faɗa miki, ɗan uwanki ne ban isa na raba zumuncinku ba amma dai ki san irin mu'amalar da za ki dinga yi da shi". Na rungumeta ta baya ina kuka nace mata, "ai makamancin hakan ma ba zai kuma faruwa ba, tunda na lura rashin kunya ce baya so ba ruwana da shi, ina tare dake har abada Gwaggo ba za ki taɓa tafiya ki barni ba". Na ƙara ƙanƙameta tsam a haka har muka yi bacci.
*** Ɓangaren Alhaji Auwal kam tunda ya koma yakewa Munubiya faɗan yajin da ta saka a abinci, ya kuma ce kar a ƙara girki da yaji, kowa ya haƙura da cin yajin, ai sun san mahaifiyarsa bata so saboda rashin adalci suka tashi suka saka. aikuwa maganar tasa ta tada balli, nan da nan ta kawo wuya ta miƙe ta kama masifa. "haba Baban Alhaji, kowa fa acikin gidan nan da nasa ra'ayin. Ita da bata ci ta dafa nata mana, ko kuma ta saka wannan yarinyar ta dafa mata tunda ita girkin ne ta ke jin ƙyashin yi, kowa ba ɓangarensa daban ba, to da wama yake dafa musu, ni wallahi ba za'a takurani ba, abinda nake so shi zanyi, dan haka banga dalilin da zaisa ace dan wata bata son yaji ba nima ba zanci abinci da yaji ba". shima cikin hargowa yace da ita, "to shikenan kiyi son ran naki, ni kuma kiga yanda zanyi dake, kuma dole a duk sanda aka yi girki a kaiwa mahaifiyata...kuma in har kina ƙaunar Allah karki fasa girka mata abinci da yaji kiga yanda zamu kwashe dake acikin gidan nan". Ko haƙuri bata bashi ba, yana gama faɗan ta tashi ta bar masa wajen yaci kansa, itama ba cin yajin ta ke ba saboda Gwaggon ne dama ta saka, to kuwa duk bala'in da za'ai indai girki da ita ne ba zata fasa sanyawa ba.
*Please Vote and Comment and Share.*
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(12)*
Buguwar da nayi da goshin Yaya Haidar ashe ba ƙarama bace, dama ga kansa kaftarere, sosai kaina ya shiga juyawa nai sauri na dafe bango ina ganin wasu abubuwa na wucewa a duhun idona, na ɗaga ƙafana zan ɗora saman steps sai idona ya rufe gaba ɗaya, nayi baya zan faɗi sai gani na faɗo a hannun Yaya Haidar, caraf ya cafeni kamar wata ƴar Baby, to ni kam tunda na buɗe ido na kalle shi dishi-dishi na mayar da murfin idona ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai dai kamar na jiyo salatin Gwaggo. Shuɗewar wasu awanni na farka, na ganni shimfiɗe a ƙirjinsa Ya kewaye ni da hannayensa, kuma a cikin ɗakinsa, na rufe idona yafi sau ƙirgen hannu ina kuma buɗewa don tabbatar da abinda nake gani, ni ce dai a tsakankanin cinyarsa kuma kwance bisa ƙirjinsa, bacci yake ko mene oho, idonsa dai a rufe yake, da sauri kuwa na miƙe daga jikin nasa a zabure