NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 38 of 98

r munafuka Anty ta miƙe ta fice. tana fita kuma Gwaggo ta ɗauka da cewa,"ko kunnuwa duka jikina bazan taɓa yarda da waɗannan makiran matan naka ba. Sarai nasan wata acikinsu tai wannan aikin, Mugwayen banza insha'Allahu duk wani sharri sai ya koma kansu, ai kaf na gama karantar zuciyoyinsu". Baba ya numfasa yace, "haba Gwaggo ki bar wannan maganar, Zarginsu ne fa kawai kike, kuma zato zunubi ko da ya kasance gaskiya". "to Auwalu tunasar da ni hadisin dana manta, kai gaka mai Mata wato na taɓa Matanka shine zaka ɓata rai. To ni dai wallahi duk wanda ma yay silar cutuwar Jikata bazan yafe masa ba". tasa gefen ɗan kwalinta tana sharar ƙwalla,"Auwalu har mutuwata bana tunanin zan kuma son Matanka, sai dai kayita jin haushina, yanda basu da kyan gani haka zuciyoyinsu basu da kyau, yo akan mene zan so su, ina zaman dole ne da su kawai saboda Allah ya ƙadarta rabo a tsakaninku, amma da kowacce sai ka bata jan kati. Har yanzu bana manta baƙin sharrin da kowacce tayiwa marayun ƴaƴan nan, waccan shirgegiyar mara kyan fasali tace Sabina tayi mata sata, ita kuma Ƴar-wadar can tace Abba ya shigar mata ɗaki, ko me zaiyi da waɗannan zubabbun nonuwan nata oho, kai kuma ka hau ka zauna akan maganarsu saboda kana tsoronsu, kaci zarafin Yaranan, to ta ina kuwa kaima zan daina jin haushinka, da wani ƙaton kanka tun na haihuwa". Baba ya ɗago yana duban mahaifiyar tasa da ta ke ta matsar ƙwalla, yana mai takaicin abinda ya aikata mana a baya yace, "kiyi Haƙuri Gwaggo, ni kaina nasan nayi kuskure amma na tuba". ta galla masa harara tace, "ka riƙe haƙurinka kai zai yiwa amfani. Na gama maganar da zanyi da kai, sai ka tashi ka tafi kaje can ka ƙarata kaima". Ganin Baba yaƙi tafiya ita ta tashi tana cewa da ni, "ke tashi mu wuce". Ta juya ta kalla Baba tace, "idan ka ƙaraci zaman naka sai ka kashe min tv da fitilu, kuma ka rufe min ƙofa". Ni dai yanda naga jikin Baba yay sanyi sai na kasa tashi, jira nake Gwaggo ta wuce na samu zantawa da shi, har tayi gaba sai ta juyo tana dubana tace, "aufa na taɓa ubanki shine za ki nuna min matsayina ko, ina magana kinyi banza dani ga susu na magana, yo acikin abinda na faɗa ƙarya nayi masa ne, ba watsi yayi da ku ba akan matansa, kamar marasa gata haka ya watso ku waje, shine yanzu dan nayi magana za ki ɗaura gaba da ni". ina kallon gefenta nace, "ni fa ba wani abin kika ji nace ba Gwaggo. to ma dai ina ce mun yafe masa abinda yay mana, ba sai ki bar tuna bayan ba, tunda ba shi da laifi amma da an fara zance sai kice yay kaza-kaza, tsakani da Allah bama jin daɗi ki daina". tsawatar min Baba yayi, hakan yasa nayi shiru ina goge hawayena. ita kuma ta ɗora faɗanta, "da ka barta taci gaba ai, itama aljanun nema suke su koya mata fitsara, bakaga tana yi kamar zata watsa ni gefe ba, kuma fa wannan ba halinta ba ne, amma yanzu tana neman koyar mummunar ɗabi'a irin ta Abba, ni tsoro na ma kar naje cikin dare su tashi su rufe ni da duka, gashi mu biyu ne kawai ban san ya zanyi ba, ita Allah ya jarabce ni da sonta ba iya barinta ita zanyi ta kwana ita ɗaya ba a cikin wannan halin ba, yanzu dole dai a san abin yi". Ni kam fashewa nayi da kuka, na kifa kai da gwiwa, har ga Allah bana so naji tana ambatar min aljanu, yanzu nai magana ta kuma cewa nayi mata rashin kunya shi kuma Baba ya rufe ni da faɗa. Baba yace, "to Gwaggo ko yaran zan tado daga ɓangaren su, sai suzo nan su tayaku kwana". da saurin baki tace da shi,"su wa ka ke nufi kenan?". "su Aisha". Yace da ita. Da sauri Gwaggo tace, "a'a rufa min asiri, waɗannan ai da gayya zasu tashi su illata ni, kai baka san yanda suke jin haushi na ba musamman ma Aisha, dan kawai ina fifita Sabina akan su, to su akan mene zan so su bayan basu ɗauko halin ƙwarai ba. kaga in baka labari, Ɗazu fa yarinyar nan Amina kaɗan ya rage ta rufe ni da duka, saboda ta kawo abinci nace ta mayar da shi ba zamu ci ba, kuma fa ba walaƙanci ne yasa nace ta mayar ba, abincin nan nasu barbaɗe suke masa yana sani cikin wani hali, baka ji yanda suka tugunzuma masa yaji ba kuma sarai sun san bana so, abinci ya koma kamar na mayu, jiya kwana nayi ban runtsa ba ina fama da ciwon ciki, faɗa maka ne kawai ban ba gudun kar ranka ya ɓaci, amma har yanzu gani nan ban wartsake ba. Shi yasa ma nace zan faɗa maka wannan haɗakar girgin namu kawai a barshi bazan iya ba, haka kawai ina zaman-zama na lafiya lau a dinga ɗora min lalura". ran Baba a ɓace yace, "wace tayi abincin?". "wannan bunkusar matar taka mana, itama ɗayar shekaranjiya da ta kawo nata maggi bai ji ba. Abba kansa kasa ci yayi sai wani ya dafa, ni dama ba kaina nake ji ba, marayun Ƴaƴan nan da basu da uwa nake tausayawa, su na lura basa tsoron shiga hakkin maraya, to ita dai mutuwar nan na kan kowa. Wallahi raina yana ɓaci matuƙa idan naga irin walaƙancin da sukewa ƴaƴan nan, kai kuma baka ɗaukan mataki, yanzu idan na mutu ya zasu yi, shi yasa nake roƙon Allah ya kawowa Sabina mijin ƙwarai kamin wucewa ta". Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka sosai, kukan da duk sai daya
🏠