NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 98

rin zanenta tukunna ta koma ta zauna, kamin ta kalla Umma ta Kalla Anty, sannan ta maida kallonta ga Baba cikin murya mai bada umarni tace. "ka sami damar yi musu bayani, yau ɗin nan nai magana da yawa na gaji". tana gama faɗa ta jefa goronta a baki tana ci. Baba ya zayyane musu kaf abinda Gwaggo tace akan zarginsu da ta ke na ciwona. Yana gama bayani Anty ta rushe da kuka kamar wadda aka yowa aiken mutuwa, faɗi ta ke. "wallahi ina ga kaf duniyar nan bayan iyayen Sabina to duk wani mai sonta ya biyo bayana domin ni zanzo a bayan Gwaggo, amma sam-sam kin gagara fahimtata Gwaggo, gani kike kamar ba ƙaunarta nake ba, kullum cikin haɗa ma ta mugun abu nake, Bayan ba haka bane, Ko abubuwan da suka faru a baya sharrin sheɗan ne, Gwaggo har yanzu kina min mummunar fahimta akan yaran nan. Yanzu fisabilillahi taya za'ai nayiwa ƙaramar yarinya turen aljanu kamar bani da ilimi". Ta ƙarasa maganar tana kuma fashewa da kukan munafurci, Sai kuma taci gaba da cewa. "tunda naga abinda ya sami yarinyar nan hankalina ya kai ƙololuwar tashi, har zuwa yanzu ban samu natsuwa ba saboda damuwar dana shiga, abinci wannan gagarata yayi ina zaune suku-suku saboda hankalina na kan Sabina da kuma hanyar da za'abi ai ma ta maganin wannan lalurar da ta sameta. Amma ƙarshe sai zargi ya shiga tsakani". hmm ni kaina ban san lokacin dana sa ki baki galala ba, lallai Anty ta ƙwarai a iya makirci, tab wannan kafce nata sai ka rantse gaske ne. Umma dake zaune a shirge tace,"to aini gaba ɗaya na rasa abun cewa, yanzu kayi magana ne abun yafi haka tsauri. Sai dai nace Allah ya kyauta ita kuma ya bata lafiya, Allah kuma yayi gaggawar bayyana gaskiya, domin ni gaskiya an shiga da hakkina. Ko wani daban bazan iya cutarwa ta hanyar masa turen aljanu ba bare Sabina da take ƴar mijina, to ni ina nasan ma hanyar wurin bokaye, ai duk rashin son da nake ma ta bana ɗora mata wannan ciwon wahalar ba, amma Allah yana ji yana kuma gani". inaaa ai Gwaggo sai ta saki Baki, hanci da idanu ta zuba musu tana kallon sarautar Allah, duban mamaki takewa Umma, kamin ta dubi Baba tace, "kaga irinta ko, idan na faɗa maka baka yarda, yanzu tunda Allah ya haɗa mu gida ɗaya ka dinga gani ai, ka kalla fa a gabanka nema ta ke tayi min rashin kunya saboda bata ganin girmana, to dama ta ina zata kalle ni da gashi ni ba Asiya(mhaifiyar Umma) ba, amma dai ko ba komai ai ni na haife ka, ta girmamani idan tana neman albarka aure, ta inda nake yabon Halima kenan, Har ta mutu kamar uwar dana tsuguna na haifeta haka ta ke girmamani, babu fitsara ko ɗaya a lamarinta, ga ƴaƴanta nan ma sun ɗebo halinta, dama hali ai tushe ne". Umma ta zumɓuri baki ta ɗauke kai, Gwaggo ta dubi Baba tace, "wai baka ji irin maganganun da ta yaɓa min bane, kana jinta fa wai Allah yana ji kuma yana gani, to me ta ke nufi da hakan? Kai kuma kaga solon namiji ba zaka iya tsawatar mata ba". Allah sarki Babana bawan Allah, cikin muryar nan tasa ta rashin son magana yace, "Hajara ki iya bakinki a wurin nan, da mahaifiyata kike magana ya kamata kisan irin furucin da za ki dinga yi". Gwaggo tai siririyar dariya, ta shiga magana ita kaɗai. "hmm wai faɗa yake yi ahaka, yana magana a hankali kamar matsoraci, ta inda nake takaicin haƙurinka kenan, Kai dai anyi dolon namiji, da ace Sulaimanu ne sai ta karɓi hukuncinta wallah". "kiyi haƙuri Gwaggo". Yace da ita, sannan ya juya gun Umma yace, "ki bata haƙuri". Tana faman ɓata rai tace, "To ni me nace, gaskiya ce kawai ba'a son mutum ya faɗa". A tsawace Baba ya katseta, "wai ke me yasa baki da mutunci ne, zaman tare kuka yi da Halima, haka kika ga ita tana yi?". Sai data ga ransa ya ɓaci sannan tace da Gwaggo, "Allah ya ba ki haƙuri". Gwaggo ta jaddada kai kamin tace,"Uhmmm, kowacce sai tayi rashin kyautawa sai su juye abin tausayi idan a gaban mijinku ne, saboda kuna tsoron takardar cika, yo wannan kiran da ace ni kaɗai ce a wurin ai sai iya abinda kuka wanke ni da shi na gani, amma ba komai Allah dai ya bani ikon gano gaskiya. Ku tashi ku tafi makirai". Umma ce ta miƙe ta fita kamar ana hankaɗata, amma Anty har lokacin tana zaune ta kifa kai da gwiwa tana kukan rashin kyautawar da akayi mata. Gwaggo tace da ita,"ke kin dawo nan ɓangaren da zama ne, mu miƙe mu baku wuri ke da mijin naki?". Anty tana goge hawayenta tace,"a'a Gwaggo Allah ya huci zuciyarki". "to kuma zaman mene kike da ba za ki tashi ki tafi ba, ba ki kalla waccen jibgagar mai jiran kaɗan ita har ta kwashi ƙafafuwanta ta tafi ba. ko kuma kina jiran kiji me nake tattaunawa tsakanina da ɗana ne, tsakani da Allah wannan ma ai raini ne". Anty ta nemi rufin asirin Allah tace,"Gwaggo ba haka bane, kawai dai ba zan iya tafiya bane ba tare da zargin da kike akaina ya goge daga zuciyarki ba. Ko dana miƙe ƙafafuna ba zasu iya ɗaukata ba, ko kaɗan bana ƙaunar fushinki". Shi dai Baba yayi shiru kallo kawai yake. Gwaggo ta taɓe baki, ta kau da kai gefe tana cewa da Baba, "kacewa Matarka ta ɓace min anan". "Zahra'u tashi kije". Yace da ita ba tare daya kalleta ba. Kama
🏠