ara shi. kai kuwa rashin mutuncinka ƙara hauhawa yake. To baka isa ba kayi kaɗan tunda dai ni na haifi ubanka ba kai ka haife ni ba, kuma ka ajiye min kofi, lemun dana aje ai ba kai na ajewa ba amma saboda hannun ɓera gareka shine kazo ka ɗaukar min ba tare da neman izininina ba. to ko Abba baya yi min haka shi da ubansa ma ya siya kenan, saboda haka kake fara neman izini kamin ka taɓa min abuna". Cup ɗin ya aje ya ɗauke kansa gefe yaci gaba da kallon tv. "to waima da ka shigo min wuri kayi sallama ne saboda ina ɗaka banji sallamarka ba?". can ƙasan maƙoshi yace, "amsata ne yake wajibi ba yinta ba". "yo to kai Aliyu dama ai ba mutunci ka cika ba, dan na faɗa ka faɗa wannan ba komai bane a wurinka, kuma dai kasan nafi ƙarfin kayi min rashin kunya tunda dai ni na tsuguna na haifi ubanka. ni ban taɓa gasgata rashin kirkinka ya kai intaha har haka ba sai yau, tsakani da Allah ka kama marainiyar Allah ka duketa ka sata kuka, haka ake rayuwa fisabilillah, kawai saboda kaga tana da haƙuri bata raina na gaba da ita shi yasa ka zageta son ranka, da ka san ba zaka koya mata ba ai saika faɗawa shi Auwalun daya saka, bawai ka juye haushinka a kanta ba, to ka kiyaye ni Haidar, ka kiyayi ramata, ka kiyayi abunda zan aikata. kuma Allah ya saka mata". Ya waigo gareta yace, "ita maƙaryaciyar haka tace miki na daketa ko na zageta?". tace, "ai ba ƙaryata tayi ba, cikin abunda ka lissafa wanne ne baka yi mata ba?, to kaga ni ba zuwa nayi nai doguwar magana da kai ba, Zuwa nayi na faɗa maka muddin kana so zamanka ya ɗore a cikin gidan nan to ka kiyayi ɓacin ran Sabina, idan kuwa ba haka ba sai ka tattara komatsanka kaje can ka kama wani gidan ka zauna zuwa randa zaka gama shi aikin naka ka koma. Haka kawai kazo kana cin arziƙin uban yarinya kuma sai ka nemi ka takurawa rayuwarta, yo ina dole anan sai ka bar gidan Wallahi, ni ba zan ɗauki ɓacin rai ba". Kan Haidar a kan wayarsa har ta kammala baice ci kanki ba, hakan kuma ya ƙara bata haushi. "ina maka magana baka ce komai ba, wato gani banza a wofi ko, ina ihun kare. kai baka iya bada haƙuri akan laifin da kayi ba, ta inda Junaid ya fika kenan, yasan na gaba da shi amma kai dai banda Ubanka Sulaimanu babu wanda kake gani da gashin ido". "to me kike so nace miki Gwaggo, salon nayi magana kice kema na zageki. Ita dai da kike ɗaurewar ƙugu takewa mutane sharri ba rayuwa ce mai kyau kika ɗorata akai ba, randa babu ke wuya zata sha Wallahi". "ɗan baƙin ciki, kamin ta rasa ni insha'Allahu na damƙata a hannun na gari mai gaskiya da amana". ta kama gefen zane tana gyara ɗauri. "Kaga ni tashi tsaye ma, kaji wani laushin kujera kana neman kassara min ita saboda ba'a saba ganinta a gida ba, zaka tashi ko kuwa? Haidar in maka magana kana gyara zama". "wai idan na tashi me zanyi miki? kina fa da takura Gwaggo. Naga dai nima gidan nan na ubana ne, kuma ɗakin nan mallakin kine kuma ke ɗin Kakata ce". "Laaa kaji min mutum; ta ina gidan nan ya zama na ubanka?, wannan gida dai na uban Sabina ne bana ubanka ba, bana son kalen jaraba". sai kuma ta fara faɗa sosai, faɗa na gaske bana wasa ba. "ka miƙe na nuna maka hanyar fita, idan ka fice kuma bana so ka ƙara dawo min sashena har ka bar gidan nan, tunda ba naka bane, mara mutunci kawai, wanda bai tausayin maraya...na rantse Aliyu idan ka ƙara taɓa min Sabina ba zamu kwashe ta daɗi da kai ba, banza wanda bai girmama kansa. shashasha kawai dogon wofi". Haidar Yaja ƙaramin tsaki ya miƙe yana zura wayoyinsa a aljihu ya raɓa ta gefenta ya fice fuuuu kamar mai shirin tashi sama. Gwaggo ta daki cinya tace, "oho dai tafi nono fari, Idan kayi zuciya har ka bar gidan nan karka ƙara shigo min sashe ko da kuwa gaisuwa ne, ni idan mutum naso muyi shiri to ya kiyaye ɓacin ran marainiyata". Yazo fita ni kuma na fito, bamu lura da juna ba muka bugi goshi, na saki ƙara da ihu ina dafe wurin, shima dafe goshinsa yayi da alama yaji zafi, ina niyyar bashi haƙuri naji ya doka wani uban tsakin daya daki dodon kunnena, ya sanya kai ya fice bayan ya jefan mugun kallo. a wannan lokacin banda a ƙule yake da ba abinda zai hana shi kawo min hannu.
*_Masu Tambayan Littafaina kuna da yawa, kuma a haƙiƙanin gaskiya novels ɗina a yanzu idan kuka cire Sirrin Ɓoye da Al'amari Book 1 to banda documents nasu, sai dai kuje wattpad @ Oum_Ramadhan, ko kuma kuje Arewa Books ananne ma zaku sami kowanne book nawa free da paid, shi yafi sauƙi...ina godiya da soyayyarku gareni..._*
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.arewa.arewabooksapp
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(13)*
Anty ce ta fara shigowa sai Umma da ta biyo bayanta. Suka nemi wuri suka zauna, Umma ta wani karkace sai faman hure-huren hanci ta ke, ta ɗauke kai tana kallon gefe daban kamar bata ga mutane a wurin ba, sai da taji Anty ta miƙa gaisuwa ga Gwaggo kana itama ta juyo tana kumbure-kumbure ta gaidata. "lafiya". ta amsa musu babu yabo babu fallasa. Gwaggo ta miƙe ta gyara ɗau