a miki rai? To me ya haɗa ku? Ki faɗan gaskiya ke dai ban sanki da rashin kunya ba". ina goge ƙwalla nace, "ni fa ba abinda nayi masa, tunda na fita yake tayi min masifa har muka je muka dawo, har cemin yake wai kinyi min goyon lalacewa, banda taɓara babu abinda na iya, da anyi min abu dana fashe da kuka sai kace a kaina aka fara mutuwar uwa". sai ta shaki ƙugu ta kama haɓa. "shi Haidar ɗin ne ya faɗa miki haka?". na ɗaga kaina, "ehh mana. Ni dai daga yau bazan ƙara binsa ba in dai shine zai koya min mota, acan ma harda ce min daƙiƙiya, ya bige min baki saboda na faɗa mishi gaskiya ni ba daƙiƙiya bace, Gwaggo har muka je muka dawo fa ba abinda na iya wai shi ai ba bawa bane, hakan ma daya fito dani darajar Baba naci". ta shiga tafa hannaye tana faɗin,"iko sai lillahi, duk shi Haidar ɗin yayi miki wannan rashin kyautawar yaci zarafinki da yawa haka?". "Allah Gwaggo ba zan ƙara binsa ba, ki faɗawa Baba indai Yaya Abba bayanan na haƙura". ta dire farantin dake hannunta, tana gyara ɗaurin zane tace, "yo dama ai ba za'a kuma na biyu ba, anyi na farko anyi na ƙarshe. yo ni kuwa ina dole irin wannan cin mutunci har haka, idan kuka ci gaba da fita tare waya san irin cin kashin da zai yi miki agaba, daga ke sai shi sai Allah'n daya ke kallonku. gashi ke ba ki iya halin rashin kirki ba bare ki rama. Saboda haka kwantar da hankalinki, ki sha re hawayenki haka kar ya rainaki, ni nasan yanda zanyi da shi, kuma idan shi gyatumin naki ya dawo ki sa me shi ki faɗa masa...ina dalili wannan ɗibar albarka har ina". Na kuma turɓune fuska ina fizgar numfashi, ta matso kusa ta cire ɗan kwanlinta ta gogen hawaye tana lallashina. "ki kwanta ki rama baccin safiyar da Abba ya azalzale ki, kamin anjima muje wurin bayerabiyar nan ta wanke miki kai, domin ba zan iya da wannan ƙazantar gashin naki ba, haka kawai muna zaune ƙalau ki jajuɓo mana abinda yafi ƙarfinmu, kwarkwarta ta shafeki. na rasa inda zan saka kaina, nan dai ba tsohon gida bane bare nasa miki omo, yafi nai ta kaiki inji suna dirje shi yanda ya kamata, tunda ba ƙaunar kitso kike ba". ni dai duk ba wannan zancen nake son ji ba, so nake ta fusata ta tafi wurin Yaya Haidar kai tsaye, ita da shi hali ɗaya ne, ya kaishi bango ya fusata ya kwashi kayansa ya tafi shine kawai abinda nake so. sai na shiga rera kuka a hankali, hakan kuma yasa ta hauni da banbami tana faɗin tunda dai na faɗa ma ta ba shikenan ba, na zuba ido kawai naga abunda zata yi, ai nasan bata barin ta kwana akaina.
na goge hawaye na Kwanta, Gwaggo ta gyara min abinda zata gyaran a ɗakin...har ta gama idona na kanta, godiya nake ga Allah daya bani Kaka kamar Gwaggo tunda ta fita nai luff jikin pillow na tafi duniyar tunanin Yayana da nake matuƙar kewarsa. Gwaggo na fitowa ta sami Haidar zaune kan kujera a parlo, ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya akan centre table, hannunsa riƙe da cup yana kurɓan lemu yana kallon tv yana ssuraron labarai. bata ko bi ta kansa ba saboda tana jin haushinsa ta wuce ɗakinta. ta ɗau tsawon mintuna a ɗakinta yana nan, kuma har ta shiga kitchen ta gama abinda zata yi ta fito still yana nan zaune, amma yanzu waya yake latsawa saboda an gama news ɗin. tsayawa tayi tana tunanin abinda zata yi masa ta huce takaicinta, Amina ta shigo parlon ɗauke da sallama bakinta, hannunta kuma riƙe da basket na kayan abinci. Gwaggo ta ansa gaisuwartata a ciki, ta nufi Dining zata aje abincin Gwaggo tace, "ke tsaya, mene wannan?". "Gwaggo abincinku ne". "to koma da shi, jiya kwana nayi ban runtsa ba har safiyar yau lafiya bata ishi cikina ba, kuma duk sanadiyar abincinku da naci ne. don haka tsautsayi ba zai kuma sawa naci ba, dan ban san me zai kuma faruwa ba, ki koma da shi kice Allah ya amfana, kuma daga yau kar a kuma kawo min". A ciki Amina ta saki dariya, burin Ummanta ya cika, dama girkin jiya da gayya ta rambaɗa masa attaruhu yanda zai kasa ciyuwa ko kuma ya ɓata ciki, ta yanda Gwaggo zata ce a raba girki. Haka Amina ta juya da abincin tana mai jin haushin Gwaggo, tana kuma dariyar mugunta, kuma da alaman yanda ta fita sai ta ƙara akan abinda Gwaggo tace ma ta. Kujerar da Haidar ke zaune ta nufa, kansa ta tsaya ta ƙare masa kallo tukunna tace da shi. "Mulkakke, hamshaƙi, ɗan masu isa da taƙama. ka wani hakimce min a kan kujera kamar ɗakin uwarka, sarai dai kasan wannan jibgegiyar ƙafar taka mai kama da doya tafi ƙarfin wannan teburin nawa, amma saboda mugun hali kazo ka ɗora min akai. don haka ka sami damar ɗauketa kamin ka fasa min glass, tunda babu sisin Sulaimanu a siyota". Yaja guntun tsaki a ciki, da yayi niyyar ɗaukewa amma tunda ta haɗa da sunan ubansa ba abinda zai sa shi ɗaukewa. cikin hasala tace, "ɗaukewar ce aiki ko kuma ɗaukewar ne ba zaka yi ba Aliyu?". Nan ma shiru yayi ma ta, hakan yasa ta duƙa ta ɗauke ƙafafun nasa ta watsar a ƙasa. ta hau sababin cewa,"ni dai duk a cikin jikokina ku biyu ne banyi sa'ar samu na kirki ba kai da Junaid, to gwara Junaidu ma sdaya zo ya tafi naga ya ɗanyi sanyi, inaga rayuwa ce ta fara g