. ta cikin madubi ya jefo min harara yace, "who is your driver?". Na haɗe fuska ina shirin fashewa da kuka, muryata a sanyaye nace, "Ohh Yaya Haidar then where should i stay? ". "dilla Malama fito ki dawo gaba, sai anyi magana ki nemi ki ɓarewa mutane baki, ki jawa mutane masifa a wurin waccan tsohuwar da bakinta bai gajiya da magana. a'a ke gaki ƴar gwal ba'a isa an taɓa ki ba. Kamar akan ki ne aka fara yin mutuwar uwa". matsalar ɗaya ni ban iya rashin kunya ba, furucinsa na ƙarshe shi yay sanadin taruwar ruwa a idona, na fito na dawo gaba na zauna, ko ƙarasa rufe kofan banyi ba ya figi motar kamar wanda zai tashi sama. kuma tsoratar da nayi ya haɗe da sakkowar hawayena, shi ko a jikinsa ma dan ba lallai ne ma idan ace na faɗa waje ya lura ba. har muka hau titi ban bar kuka ba don sosai maganarsa ta bani haushi, idan shi bai damu da tashi mutuwar uwar ba aini na damu da tawa, sam Yaya Haidar baiyi halin Uncle Sulaiman ba don ba haka Babansa yake ba. Shi ko tausayi ban bashi ba, saima tsaki daya dinƙa ja yana shafo sumar kai har muka isa wurin koyan motar, hakan ya ƙara bani haushi, saboda ni fa ina takaicin naga ina kuka aƙi lallashina, nafi so ko ya na fashe to a karkato da hankali kaina, ta irin haka ne ma muke faɗa da Gwaggo wataran, idan na bata haushi sai tayi biris da ni. Ni dai yau nayi dana sanin fitowa koyar motar nan, gaba ɗaya ma naji koyon ya fice min a rai, kullum da murna nake fitowa nake komawa indai da Yaya Abba ne, kuma muna wasa da dariya yake koya min, amma yau tsabar tsoron Yaya Haidar koyan kwanar da na kasa yi sama da sati biyu sai gashi cikin rabin awa na iya, mu kanyi awa biyu zuwa uku idan muka zo amma yau ko ɗaya bamu cika ba naji yace tafiya zamuyi shi ya gaji. muna ɗaukan hanya na ɗago na dube shi, murya a ɗarɗace nace, "Yaya Haidar ai bada wuri fa muke komawa ba, Baba yace Yaya Abba yake tsawa ya tabbatar da na iya sosai kamin mu koma". Farko banza yayi min, sai can naga yayi wani miskilin murmushi yayi revers, a bakin filin wurin yay parking, kansa na gaba kamar bada ni yake ba yace, "buɗe ki fita". nai sororo ina kallonsa. ya ƙara ɗaga murya wanda na tabbata har na waje sunji. "nace ki buɗe ki fita. in yaso ki sami wani ya koya miki sai ki biya shi, ko kuma ki kira shi Abba'n ya koya miki shi daya ga zai iya aikin wahala amma ni ba kalata bace sanya daƙiƙiya a gaba ina koya mata abu tana kasawa". "Amma tsakani da Allah Yaya Hydar ai kasan koyon driving ɗin nan da wahala, kuma ma yau ai nayi ƙoƙari dai, gashi kai baka encouraging ɗin mutum, sai dai kai ta faɗa. kuma fa ni ba daƙiƙiya bace Allah, saboda ina da ƙoƙari akan komai, kaje makarantarmu ma ka tambaya, har na gama first class nake ɗauka". Na faɗi hakan ina turo baki gaba, na san wannan ƴar maganar da nayi ba zai barni ba, ile kuwa ina rufe baki ya ɗalle min laɓɓana da yatsansa wanda sai daya sani yin ƙara ina sosa wurin. "karki yi min rashin kunya saboda ni ba Abba bane, tun kamin a haifeki nazo duniya, sai da nayi shekara ɗaya-ɗaya har 13 kana aka haifeki a tsumma, kashinki da tunbuɗinki babu kalar ƙazantar da ban gani ba, saboda haka ki iya bakinki wajen yimin magana, ni ba sa'anki bane". Haushi ya tuƙeni hakan yasa na shiga ƙunƙuni. ina jinsa yana faɗin, "banda kinci darajan Baba daya ce na kawoki, kuma motar ba ta gidan mu bace, ai da sai kin fita in yaso ki daɓa a ƙafa ki koma gida...mara kunya fitsararriya ana magana kina tura baki gaba kamar shantu, ke ai gaki goyon Kaka goyon gata, to ba gata wannan tsohuwar ke nuna miki ba, dan a nan gaba wuya za ki sha da wannan halin naki". Ni dai bance masa komai ba har muka iso gida, bare ya kuma gaya min no sugar, na cika nayi fam saboda haushi, Allah ko da kuɗi, kai ko shi ɗaya ne mai koyar da mota a duniya ba zan ƙara binsa mu fita ba sai dai har na mutu kuwa ban iya motar ba. Yana yin parking na buɗe na fice, Ina ji yana min magana nayi masa banza kome ma yake cewa oho, ɗakina na wuce kai tsaye na kifa kan gado ina kuka, to fa dama da biyu kukan nan nawa, tun jiya kewan Yayana ya isheni, ga shi yau kuma wannan matsolon raken ya ɓatan rai. Ina kwance ina faman shashsheƙar kuka Gwaggo tayo sallama, ina jinta ta buɗe wadrobe ta zuba kaya ta mayar ta rufe, kana ta karkato kaina tana faɗin. "ke kuma yaushe kika dawo? Me akayi miki kike kuka? Me Abban yayi miki? Ko kuma shigowarki wata a cikin gidan nan tai miki hali na rashin kyautawa?". Duk a jere ta jefa min tambayoyin, na miƙe zaune ina goge hawayena ban dai ce ma ta komai ba, ƙaramar wayata dake gefena kawai nake kallo naga ko kira mai sabuwar numba zai shigo, don a kullum bana yanke tsammani da kiran Yayana. ta kama ƙugu tana faɗin,"yau naga sarautar Allah". "keee to ko kin gamu da ciwon baki ne da kika gagara bani amsa? Ina daɗa tambayarki me Abba yayi miki? Za ki bani amsa ko sai na ƙwala miki wannan murfin tasar". Sanin zata aikata yasa da sauri na buɗe baki nace, "ba Yaya Abba bane, Yaya Haidar ne". "Haidar dai! shi Haidar ɗin da yake baƙo ya ɓat