NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 33 of 98

, na duƙawa nayi zan kwashi kayan tace, "ki barsu idan na miƙe zan gyara miki na kai miki, ko ba ki kalla duk karin guguwar ya hargitse bane, kuma kika tsaya cewar sai kin kai ɗaki wancan ɗan masu kwazazzafan sabon aike zai kuma danno miki, ma za jeki sai kun dawo Allah ya kiyaye". nai mata wani hug irin wanda ta gani a tv sanda muna kallo, yanda Patriva ta rungume kakarsu shine tace to nima nake yi ma ta hakan tana so dan Allah. nace,"Gwaggona na gode, Allah ya bar min ke ya ƙara maki lafiya da nisan kwana". Na faɗa fuskana ɗauke da murmushin jin daɗi tare da bata sumba a kumatu. Sauri-sauri na isa dressing mirrow na ɗauka faran powder na shafa, na ɗora da man leɓe sannan na zira takalmina. Duk abinda nake idon Gwaggo akaina, ina ƙoƙarin fita tace. "ke wai dan manzon Allah wacce kalar macece, kina nufin a haka za ki fita da wannan buyagin gashin naki da ba kya so a taɓa shi, ke kin ganki kuwa kamar sabuwar kamu". na yatsine fuska nace, "Gwaggo wancan satin fa aka taje shi, kuma naga baiyi komai ba ne, kuma fa na sanya hula babu mai ganewa sai ɗan sa ido". tace, "ni Hannatu yau naga abinda yafi zare tsayi. to Sabina da aka taje shi wancan satin ma ai tsami yake, Ina taje shi fa ina tara yawu a bakina, kuma yanzu har kina faɗin kin saka hula, ke dai kin shiga uku da ƙazantar kai wallahi, samu ki kai ma shi yasa. to kizo ki wuce ki ɗauko wannan abar mai kama da indararo kizo ki busar da shi ki taje don bazan gayara miki ba, kuma baki isa kin fita a haka ba bare kija min zagi ace Gwaggo bata gyara ki". kamar zanyi kuka na maƙale jikin ƙofa ina roƙonta akan ta ƙyaleni, don ni wallahi idan da abinda na tsana taɓa kaina, da ace Gwaggo ta bani dama tuni na jima da aske shi, to sai tace wallah bazan aske ba haka kawai na rasa mijin aure, tunda ta lura mazan yanzu idan ba gashi ba ƙirji sai su raina mace. "wai kuwa ba za ki zo kiyi abinda ya kamata ba ki wuce kije ku tafi sai kunyi yamma. Kin wani tsaya kina turon baki gaba kamar wadda za'a bawa nono, to bari na kira Abban nace masa gaki anan ba uwar da kike kawai dai ba za ki fito bane". nai saurin cewa, "don Allah Gwaggo ki bari sai na dawo, ko a yanzu zafi yake min, kuma kin san ko ya na taɓa sai ciwon kai". "ai kuwa dai kika je gidan miji da wannan ƙazantar baƙar wuya za ki sha, a tou ni dai gaskiya nake faɗa miki. dan ba zai juri ganinki tsab-tsab ba yana jiyo tashin ƙamshi ta ko'ina a jikinki sai ya doshi kai yaji hammm, yasin sai to miki hanyar gidanku zai yi, idan za ki gyara tun wuri gwara ki gyara". na ƙara cewa, "to Gwaggo nace ki barni na aske ba shikenan sai na huta ba kema ki huta da mita". "yo dama aini ban isa na faɗa maki gaskiya ba, shikenan sai ki ce na cika mita. to kije Allah ya kiyaye, ina kuma faɗa miki karki yarda da tuƙin ganganci irin na Abba, da kinga yana neman wuce gona da iri ki sauka ki nemi mota ki dawo gida, ranki ɗaya ne ba biyu ba...sai kun dawo". Fita nayi ina jinta kuma tana ci gaba da faɗa akan rashin gyaran gashin, idan na dawo ya zama dole ta kaini wajen bayerabiyar nan ta gyara min kai, ba zan kasheta da tsamin kai ba lokacinta bai ba, kuma wallah kaina ba wani wari da yake sharri ne irin nata kawai. ni na lura sababin Gwaggo ma ƙaruwa yayi tunda muka dawo gidan nan. Ina isa ƙofan parlo kiran wayar Farhana ya shigo, ina murna na ɗaga domin mun kwan biyu ba muyi waya ba, hiran yaushe gamo muka hau har tana bani labarin exams ɗinsu ta fito ta sami second class, na tayata murna sosai, na tambayeta yaushe zata zo suga gidanmu tace sai anyi hutun islamiya, nace ma ta Allah ya kaimu, har na bata labarin nima an samo min addimission, tai min congratulations tare da bada shawarwari saboda karatun Uni ba ɗaya yake dana Secondry ba. tun fara wayarmu so nake na tambayeta Yayana amma gudun kar ran junanmu ya ɓaci na haƙura, mu kai sallama na kashe wayar raina ba daɗi. ina ƙarasawo parking lot gabana naji ya faɗi, ƴaƴan cikina naji sun kaɗa har jakar hannuna ta kusa faɗuwa ƙasa, na kuma yin ƙasa da kaina ina takawa kamar bana son tafiyar, don ina ƙwaƙwƙwarar tafiya zan kifa ƙasa, gaba ɗaya a tsorace nake da Yaya Haidar wanda tunda na taho idonsa ke kaina, fuskar nan tasa a haɗe kamar hadarin gabas ya taso, sai wurgan wani mugun kallo yake. Ni dai har na iso inda yake tsaye jingine a jikin mota ƙirjina bai bar duka ba, tsorona da fargabana kar dai ace da shi zamu fita yau. sam shi mutum ne mara daɗin sha'ani, miskilanci da masifa su kaɗai yasa a gaba, kuma tunda yazo gidan ya hanamu sakewa, Amina ce ma take iyawa da shi saboda mara kunya ce ta ƙarshen gaske. ni kam da magana ma bata isheni ba, sai dai yay min son ransa, shi yasa duk na ƙagu ya koma gidansu. kuma tsawar daya doka min ita tai sanadiyar gurɗewar ƙafata. "kin bar mutane tsaye kamar aikinki suke kina biyansu, za ki ɗago ƙafa ko kuwa nima sai nayi tafiyata". A ruɗe nace, "Yaya Haidar to ina Yaya Abban?". bai bani amsa ba ya wurgan harara ya zaga ya buɗe gaban mota ya shige, dana tashi nima na buɗe baya na shiga
🏠