Allah dai...". sai kuma tayi shiru tare da yin ƙwafa. Cikin faɗa kuma taci gaba, "ni dai kaf cikin Yarana babu mai halin kirki irin Auwalu. haƙuri, mutunci, karamci komai ya haɗa, amma kuma duk cikin Ƴaƴana shi ɗaya ne bai yi sa'ar Mata ba, Mahaifiyarku kaɗaice ta ƙwarai, sauran auran nasa kam sai dai a kira shi da auran ƙaddara, jiya na gama yarda da duk wani mugunta nasu da kuke faɗa nake ƙaryataku, saboda kwana nayi ban runtsa ba ina kokawa da cikina. dama duk wani iya shege da suke ina ɗaga musu ƙafa ne saboda darajar Auwalu da suke ci amma na kusa yiwa tufkar hanci, kaf ɗin su za su gane shayi ruwa ne. Hmmm banda ma dai ina da tausayi ai da sai naja musu Allah ya isa, to idan naja musu binsu zatayi su zo su ƙara lalacewa, ni kuma gyaruwa nake so suyi kar a tafi lahira da tarin zunubai, tunda dai Allah ya ƙaddara auren su da Ɗana". ta juyo ta kalle ni, wadda nayi shiru ina sauraronta, ince tace nace shi yasa ma nayi gumm. tana wurgan harara tace, "kinyi shiru ba ki ce komai ba". nace, "to Gwaggo ni me zance". "ki faɗi abinda yake zuciyarki karta kasheki, saboda ina faɗar gaskiya shine kike jin haushina, to sai dai ko me za kice kice ehe, sirikaina ne amma bana sonsu, saboda mutanan sun cutar min daku, yanda bana manta akhairi haka bana manta sharri. ai tsakanina da su Allah ya...". Sai kuma tai shiru bata ƙarasa ba, ni kuwa dariya ce ta taho min, duk masifar da Gwaggo zata yi akansu da zarar tazo kan Allah ya isa to fa ba zata ƙarasa ba sai tayi shiru. "ki sa ki dariyarki mana ki bar ƙunsheta kina cutar kanki, ina faɗa miki gaskiya tausayinsu nake ji ne saboda bakina kaifi ne da shi kamar wuƙar daba, inaja musu Allah ya isa binsu zatayi kuma tabbata lahu sai sun lalace, ai nayi na gani ne, tunda najawa kishiyata Hussaina har kwanan gobe gata nan halinta bai sauyawa ba, iskancinta sai ƙara gaba-gaba yake taƙi tayi dai-dai". na sauke numfashi ina cewa,"yanzu dai Gwaggo kiyi haƙuri ki rabu da su, kowa yayi na gari kansa, ki barsu da halinsu, kuma insha'Allahu kamin nan kamin anjima za ki sami sauƙi, na kira Baba yace Family doctor zai zo". tace, "ai shikenan nayi shiru tunda kinsa baki, amma batun haɗakar girki kam ya ƙare, ni lokacin hutuna ne yazo tunda Allah ya kawo mu cikin wannan ni'imar, kema kuma bana so ki wahala, wannan aikin gajiyar kin gama shi tun a tsohon gida sai kuma bautar gidan mijinki. Saboda haka zan kira Karima idan zata zo ta samo min ƴar budurwar yarinya mai hankali da tsoron Allah". Kamin na buɗi baki nayi magana Zainab ta shigo ɗakin ɗauke da sallama bakinta, Ta tsuguna har ƙasa ta gaida Gwaggo. "lafiya". Gwaggo ta amsa mata fuska a haɗe, murya a can ƙasa. Nima tace min, "Yaya ina kwana". "lafiya lau Zainab". Na amsa mata fuskata ɗauke da fara'a. Yaran dukansu sun hankalta tun jan kunnen da Gwaggo tayi musu, don sun san sarai zata iya aikata komai, ba kasafai ta ke faɗa bata aikata ba, abu ne mai sauƙi a wurinta tai musu auren ƙauye. "kin shigo min ɗaki kin wani tsareni da idanu lafiya aka mutu kai na motsi, ko wani kinibibin ne?, ko kuma an aiko ki gulma ne?. To idan ma itace aka aikoki sai a sami damar juyawa don babu abinda za ki ɗauka". baki Zainab ta turo gaba, bata tanka ma ta ba tace min, "Yaya". nace, "na'am". "Yaya Abba says if you did'nt come out he will leave, becouse you are westing his time". na dafe goshi nace, "Ya rab, tell him yayi haƙuri dan Allah, am comming out now". kuma bata kai ga fita ba Gwaggo ta Gwame baki tana cewa. "idan ka haɗu da abinda ya isheka sai ka zubawa sarautar Allah ido. wannan barbaɗin rashin mutunci har ina?, a shigo min har cikin ɗaki a dinga sauya harshe a gabana, to duk wanda ya zageni kansa ya zaga tunda dai ba iyawa nayi ba bare na rama, ni dama tunda na ganki a ɗakin nan nasan ba alkhairi ne ya kawoki ba...ke kuma da ba ki da wayo kiyita biye musu suna ɗoraki a hanyar lalacewa, kaf gidan nan dai kin san babu mai ƙaunarki sama dani, amma tunda ubanki yay arziƙi kike neman juyawa min baya, to indai waɗannan makiranne gaki gasu nan". Zainab tace,"kai Gwaggo bafa zagi ne akai ba". sai ta kauda kai tace,"sarai ai na sani, Abba ne yayo aike yana jiran ta fito, banji yaran ba amma na fahimci me akace tunda naji an faɗi sunansa...to hakan da kika ga nayi gargaɗi ne nayi saboda kar a ƙara kwatanta hakan wataran, dan baza'a ji daɗin martanin da zan mayar ba...bana son sauya yare a gabana wannan halin munafukai ne". Zainab dai tai murmushi ta juya ta fice. "to ni kam Gwaggo tunda kinji sauƙi zaɓar min kayan na fita, kin san halinsa yanzu zai ƙara yo aike ko kuma yay tafiyarsa". "wa yace miki sauƙi naji, ƙarfin hali ne fa kawai nake...ni matso da kayan na gani". na tura mata kayan gabanta, ta ɗaga wata red ɗin riga tawa ta aje a gefenta tana faɗin,"wannan kamar sawarki uku ko. bari na bawa ƴar aikin gidan can da aka aikota t gaishe dani". tukunna ta zaɓar min wata doguwar riga ta shadda wadda taji aikin stones a jiki, ɗinkin yay kyau sosai. na ɗauka na saka na zaɓi gyale na yafa