arta ni babu ruwana". Zainab na turo baki gaba tace, "to ai Gwaggo ba laifinmu bane, mu yanda ake nuna banbanci a tsakaninmu ne bama so, tsakani da Allah muna uba ɗaya amma sai a dinƙa nuna anfi sonta taya za'ai muji daɗi". ta gwame baki tace, "idan so kuke a so ku ai sai ku zama mutanen kirki irinta". ta juwa ga Baba tace, "ni na gama magana. Kaima idan ka gama taka sai kowa ya tashi ya bar min parlo". Baba yace, "ehhh Gwaggo ai tunda kin gama shikenan". tace, "ka dai ƙara dubawa ko kana da ta cewa". "babu Gwaggo". "tom shikenan". Har zata miƙe sai kuma ta koma ta zauna, "au nayi mantuwa, sai batun girki kuma. Bana son wani girkin ƴar aiki a gidan nan, kowacce zagewa zata yi ta dunƙa dafawa marayun Ƴaƴana suna ci suna ƙoshi, tunda ba auroku akayi dan kuci kuyi kashi ba. A tou; nan dai ba tsohon gida bane bare ayi abinda aka ga dama, kar aji laushin katifa da sanyin AC ace za'ake jaɓarewa ana ƙara kumbura". Baba ya dubi Yaya Abba yace, "kai Abba sai ka dinga fita da Sabina kana koya mata mota B4 ending of this month, saboda already na sama mata addmission next month zata fara lectures". "tom Baba, Allah ya kaimu". Baba ya ɗauko wata baƙar leda a wurin, kwalin wayoyi ne a ciki, takan ƙananun ya fara bawa, ya kira Khadija ya bata tata ƙirar Tecno Spark 4, Zainab kuma Infinix S5, Aminatu da Aisha iri ɗaya suma, infinix Zero5 sannan nima ya miƙo min tawa ƙirar iphone 11 yace na bashi waccen daya bamu, kwacce da sim card ɗinta ya bata, kuma take a wurin yay mana recharging ta bank kowaccen su 2k, ni kuma 3k". Dukanmu muna murna muke masa godiya da adu'a. Daga haka kowa ya watse aka tafi kwanciya.
_Na Sadaukar Da Page Ɗin Gareki Siddeeqer Oumar Barde, kiji dadinki kuma ki sani ina yinki over._
*Please Comment, Vote amd Share.**AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(11)*
Shirin sauri nake tayi Yaya Abba na jirana zamu fita koyan mota. Baki ɗaya na hargitso da kayan sawata na rasa wanda zan saka, saboda na riga na saba tun muna tsohon gida bana iya saka kaya idan zan fita sai wanda Gwaggo ta zaɓa mani, gashi ita kuma yau ta shige toilet tayi zamanta kamar ta shiga labour room. Kiran wayar Yaya Abba ne ya shigo a karo na ba adadi, kai na dafe na share ban ɗauka ba, saboda idan na ɗauka fa raina zai iya ɓaci matuƙa, shi mutum ne wanda ya tsani delay a rayuwa, shi yasa ma ba kasafe ya fiya haɗa fita da wani ba. har lokacin da nake tsaye kamar nai kuka banga alaman Gwaggo zata shigo ɗakin ba, kayan na yayiba na fita da su zuwa ɗakinta, a bakin gado na sameta zaune ta riƙe baya tana ta sauke nishi, kayan na zube a gabanta bakina a gaba ina daɗa turɓune fuska. ta ɗago tayi min kallo mai kama da harara sannan tasa ƙafa ta shure kayan. tukunna a ƙufule tace da ni, "ke fa ba ki iya ganin mutum cikin wani hali ki masa sannu ba ko ki tambayi meke damunsa, a'a ke fatanki a biya miki buƙatarki, to sai ki jira sai na gama wartsakewa". "Eyyah Gwaggo tah wallah nai zaton ko kinyi training ne, ban kawo wani abu ke damunki ba". Wani wawan kallo ta wurgo min wanda yasani yin shiru da sauran maganata. "to idan kin aza sai ki sauke ba training nake ba, zawo nake fama da shi, shiga ta banɗaki na huɗu kenan a cikin rabin awa. Ban yarda da abincin jiya da muka ci ba, ina tunanin waɗannan ƴan iskan sun fara mana barbaɗe a abinci". Da sauri na ƙarasa wurinta cike da tausayawa, duba da yanda idonta ya faɗa lokaci ɗaya. "Subhanallahi, Gwaggo Zawo kuma? to taya akayi hakan? me kika ci da za ki kwanta?". ta ƙara kufula tana cewa,"da wanne yare nayi miki maganar da kika kasa fahimta, ko kuma ƙara maimaita miki kike so nayi, ba kiji nace ina zargin masu kama da tantabarun can ba. Mutum na fama da kansa dole sai kinsa yayi magana". taja guntun tsaki, "ke sam ba ki da saurin fahimta, dole idan za'ai miki bayani sai an faɗaɗa shi, kisa aita doguwar magana". nace, "Gwaggo to aini ban zargesu ba ne, tunda abincin nan dai nima na ci shi, wataƙila dai ko cikinki ne ya ɓaci kawai". ƴar maganar da nai kuma sai ta jawo masifa da sababi, faɗi ta ke,"auto ni za ki gayawa cikina ya ɓaci dake ban san takan cikin nawa ba. Da can da nake girkina naci lafiya na miƙe lafiya fa, da kika ganni sarai nasan takan lafiyar cikina, wannan girkin dai dole anyi wani barbaɗin a ciki domin nasan halin mugwayen matan Babanki, so suke su ƙarasa ni kuma ba yanzu ba, kema Allah ne ya kiyayeki, saboda haka bazan iya ci gaba da wannan haɗakar girkin namu da su ba, anyi an gama daga jiya, kowacce cikin su tayi nata taci da iyalanta, mu kuma yazo ya samo mana wadda zata dinga yi mana namu, wacce zuciyarta ta cika fal da tsoron Allah". Ni dai ina dafe da bayanta nayi murmushi, saboda ban isa na hanata wannan mitar da masifar ba sai kuma ta samu lafiya, cike da tausaya ma ta nace, "Sannu Gwaggo, bari a kira Baba sai ya turo likita". "ehh kirawo shi ɗin, dan cikina a ɗaure yake ni ɗaya nasan irin azabar da nake ci. Ba don ina gudun haɗa rigima ba ai da saina zayyane masa wannan muguntar da aka haɗa min, amma