NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 98

zauna, Gwaggo kuwa ta fusata ta hau masifa tana faɗin, "yo ni idan na faɗa maka Abba baya ganin girmana ai baka yarda. Amma yanzu da yayi a gabanka sai ka tabbatar". Yaya Abba yace, "nifl fa ba ƙin tashi nayi ba Gwaggo, ba kiga ina ƙoƙarin miƙewa bane, kuma tunda nake dake kin taɓa sa ni abu naƙi yi ne". "yo Abba na nawa kuma, kuma ai ba yau ka saba ƙaryatani ba. Kaci mutunci na agaban waɗannan marasa kirkin kaji ko, in yaso kai da su sai ku haɗu kuyi min fitsarar san ranku". jan baki yayi yay shiru bai tankata ba. Gwaggo tabi kowa da kallo ta taɓe baki sannan ta juya ta dubi Baba tace, "to Auwalu ni magana ce nake son nayi, wadda gaba ɗayanta kashedi ce da kuma jan kunne. A tou; ƙwamma a buɗe kunne da kyau a saurareni". "to Gwaggo muna jinki ai". Ya faɗa cikin rissinawa da girmamawa. "a'a ni fa kai tsaye bada kai nake ba, su wancananka ai sun san kansu, uwayen kilibibi da iya kisisina". ya sake cewa "Gwaggo a dai yi haƙuri, shi yasama na taramu anan ɗin gaba ɗaya". "oho dai, ni ka tara ko karka tara dama ina da niyyar isar da wannan saƙon tunda Allah ya haɗamu zama wuri ɗaya. gida dai arziƙin ɗana ne dole na zauna a cikinsa tunda bana uban kowa bane, gida kuma na uban Sabina ne zamanta cikinsa daram dam-dam ehe, babu shege daya isa ya raba inuwarta da ubanta". Anty da ta san dasu ake ta kwantar da murya tace, "Hajiya Gwaggo kiyi haƙuri, duk abunda ya faru a baya ya wuce...". Ai bata kai aya ba Gwaggo ta dakatar da ita tana faɗin, "munafuka ke kika kaini Hajji dana zama Hajiya, kina wani kwantar da murya da sadda kai kamar ta Allah, baƙar makira Allah a fuska Fir'auna a zuci, Yo Zara'u ni ai sai dai ki gayawa wani baƙin halinki, domin farin sanin dana yi miki ko uwar data haife ki bata sanki ba, saboda haka ki daina wani ƙumbiya² ki fito sak a mutum ki faɗa musu sabon tuggun da kike shiryawa a zuciyarki, saboda ni bana karantar fuskar Mutum sai dai na karanci zuciyarsa, wannan baiwar tawa ce ni ɗaya da Allah ya bani. ki sa ni da kyau saboda ki kiyaye gaba, domin kina ƙara aikata abunda ban gamsu da shi ba zan sanya Auwalu ya yanka miki Jan kati, akan Sabina babu abinda ba zan iya ba". Kuka Anty ta saka tana faɗin, "wallahi Gwaggo ba sanin da kika yi min da bane, ki bar yimin wannan mummunar fahimtar a yanzu". Gwaggo ta taɓe baki tace, "ki bar ɓarnatar da hawayenki a banza kina kukan munafurci, Kina yaudarata kina yaudarar kanki, da kika ganni nan na zauna cikin kishiyoyi babu kalar kissa da makircin da ban sa ni ba, don haka kisan a inda za kiyi". Baba yace, "Gwaggo ke fa uwace, faɗa ya kamata kiyi musu da nasiha, amma duk wannan ƙananun maganganun basu taso ba". Ta kalle shi ta kuma kallonsa, sannan ta bishi da kallon sama da ƙasa, kamin nan ta ciro Goro a gefen zanenta ta wurga a baki tana faɗin, "to Auwalu nuna min yanda zanyi kaji kai da kasan dai-dai, har ni dana haifeka zaka nunawa kafi ni sanin abinda ya kamata, ahh lallai ne, aikuwa to ka ƙara magana a wurin nan zan tattatara komatsaina na koma ƙauyenmu, tunda na lura kafi ƙaunar ka zauna da Matanka a sabon gida sama da ni da nayi naƙudarka". "ba haka bane, kiyi haƙuri Gwaggo Allah ya huci zuciyarki". "Ameen". Ta faɗa a taƙaice. sannan ta ƙara cewa, "yauwa ana jina ba. Naji ana cewa babu wata matsala Allah ya bada zaman lafiya, ehh to ameen amma ba anan gizo ke saƙar ba, Ita dai Sabina da bakwa ƙauna ta zame muku ciwon ido domin babu yanda kuka iya da ita, saboda ina tsananin ƙaunarta Mahaifinta kuma na mutuwar sonta, saboda haka muddin ana son zaman lafiya a gidannan dole a ɗauke baƙin ido da mugun baki a kanta, gata nan ita kaɗai mahaifiyarta ta haifa mace, ni kuma na maye gurbin uwarta, A kiyaye ɓacin ranta, domin a duniyar nan idan ana ƙaunar aga ɓacin raina to a taɓa min ita. kun san da wannan amma yana da kyau na maimaita muku don naga baku da hadda. Farincikinta kaɗai nake son gani a gidan nan, kar a kuskura naga saɓanin haka, kallon banza wannan kuka yiwa inuwarta billahillazi ina shaida muku sai kun bar Habuja kun koma gidan iyayenku, musamman ma ke kumbusa (Umma kenan), saboda haka muddin ana son zaman lafiya da kwanciyar hankali ta ɓangarena to kar a taɓan marayun Ƴaƴa, duk da dai shi Abba ba kirki ya cika ba amma a ha nake sonsa, saboda haka a kiyaye, a tou; domin ni nafi ɗan iska iya shege, yanzu sai aga ba dai-dai ba". Sannan ta koma kan ƙannena ta kira sunan su ɗaya bayan ɗaya, "Aisha, Aminatu, Zainab da ke Khadija. Allah ya halicce ku a mutanen kirki amma kun rikiɗe kun koma na tsiya duk kun ɗauko halin uwayenku, to kuma kuji ni da kyau. Sabina dai da kuke gani ba sa'ar ku bace, saboda haka dole ku bata girmanta, ku manta da batun cewa ita zata dinƙa baku kamar yanda kuke so, ita ba waina bace da zaku dinƙa juyata son ranku saboda kunga tana da haƙuri. Ƴan banza masu zubin Ƴaƴan kwaɗi. to dai-dai da rana ɗaya akasin abinda na faɗa ya faru saina kai yarinya ƙauye nayi sadaƙar ta ga tsohon daya kusa shuɗewa, in yaso Yarinya ta zama bazawara da ƙuruciy
🏠