NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 3 of 98

ƙa yana fesar da hayaƙin ta gefensa. zai kuma zuƙa kenan yaji an ƙarɓe ta daga hannunsa, ya ɗago jajayen idanunsa domin ganin mahaluƙin dake da ikon karɓe masa abokiyar rayuwarsa. Idonsa ne yay tozali da ƴar kyakykyawar budurwa tsugune gabansa, tana sauke masa kyakykyawan murmushi, da wannan idanun nata masu zurfi, kallo ɗaya yay ma ta yay saurin ɗauke idonsa saboda faɗuwar gaban daya tsinci kansa a ciki, ba tare da sanin dalilin hakan ba, kuma haka kawai sai yaji ƙirjinsa na bugawa da sauri da sauri abinda bai taɓa riska ba tsawon shekarun rayuwarsa. ina lure da shi da yanda yake bina da kallo ta ƙasan ido, wucewar sakan ɗaya, biyu, uku, ya ɗago da kansa gaba ɗaya yana sauke kallonsa gaba ɗaya akaina, har yanzu ban bar yi masa murmushi ba, hakana ban ɗauke idona daga ƙwayar idonsa ba dake haskawa da ƙyallin mamakina ba, kuma zan iya rantsewa a wannan lokacin abinda yake rayawa acikin ransa shine _ko dai ni mahaukaciya ce?._ na gyara zaman glass ɗina sannan nace da shi, "Hy Mr Man". na faɗa ina ɗaga masa gira sama, sai dai shi idonsa na kan tabar dake hannuna da ban yar da ita ba, sai na kalli tabar tukunna na maida kallona kansa kamin na shiga ce masa. "wannan tana cutarwa, ba ta amfanar da mai shanta, Almubazzaranci ce, tana cutar da na kusa da kai. a bisa haka Malamai suka ce tunda duk abinda ta ke haddasawa haramun ne to itama ta zama haramun". ina gama faɗa na jefar da sigarin a ƙasa, na ta ke da takalmina, sannan na maida glass ɗina dana cire nai cleaning ɗinsa. yaji sanda iska ta ɗebo abunda tace ta shigar cikin kunnensa, kuma yaji yanda kalaman nata suka sami zama acikin kansa, ya tantance maganartata cikin kowanne futar harafi, sai dai ya kasa tantance zaƙin sautin daya fita acikin amon muryartata. ni kuwa ƙura masa ido sosai nai ko tsoronsa ma banji, kuma shi ma sosai yake kallon ƙwayar idona, sai dai Allah masanin gaibu, dan ban san me zuciyarsa ke karanta masa ba. sai kawai na ƙara murmusa kuncina a karo na babu adadi, tare da harɗe hannayena a ƙirji ina faɗa masa abunda bai tambayeni ba, haka kuma babu nuni na yana baƙatar sanin hakan. "Sunana Sabina Auwal, anan garin kano nake. And you?". a wannan lokacin abinda Sabina bata sa ni ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewar_anya ita mutum ce kuwa._ bai bani amsa ba, babu kuma yunƙurin hakan a tare da shi, abu ɗaya ne kawai ke ɗawainiya dani, aiwatar da wasu abubuwa da bana sanin lokacin da nake yinsu ba...matsowa kusa da fuskarsa nai, na ɗaga masa kai alamar ina jiran cewarsa akan tambayar sunansa da nai. sai naji shi da saɓanin abunda na tambaye shi ɗin. "me yasa ki ka faɗan sunanki bayan ban tambaye ki ba?". "ka fara bani amsar tambayata tunda ni na fara". na faɗa ina ɗan karayar da kai gefe. a hankali naji muryarsa na fita, kuma a lokacin so nake na toshe hancina saboda warin sigarin dake fita a bakinsa, amma na kasa saboda bana so na nuna masa walaƙanci. "duk da bana jin yaren da kika yi min tambayar, amma zai iya yiwuwa na fahimta. indai yanda na fahimci tambayar taki ne to ni ba ni da suna, kuma bani da sunan Baba, ban san kuma garin da na ke ba". sai kawai na saki baki galala ina ƙare masa kallo da maɗaukakin mamaki, kuma ƙwayar idona na haska masa da cewar ban yarda da abunda ya faɗa ba. "tun ina ƙarama kamin Mama nah ta rasu, ina tunawa kamin ta rasu ta gaya mun babu kyau ƙarya, don haka kar na yi kuma kar na koyi yinta, kuma kar nayi tarayya da me yinta. Sannan da na girma, Gwaggo nah wata rana ta yiwa Yaya nah faɗa cewar Babba baya ƙarya. So dan haka kaima karka yi ƙarya kaga babba ne kai, kuma ni yarinya ce, idan kayi zan koya a wurinka, kuma nasan ai ba zaka so hakan ba ko Yaya?". ina masa maganar ne da yanayi irin na yara. "me ya kawo ki nan wurin?". Ya tambayeni yana mai tsareni da ido da alamu na tuhuma. na tsarota sosai, kuma tsoron bai sa ni yi masa ƙarya ba, na faɗa masa ainihin abunda ya kawo ni. "na zo ne domin na hanaka shan sigarin da ta ke haramtacciya". "to ki tashi ki tafi, ni ɗin bana son kowa a kusa da ni, ki tafi kar naji miki rauni". yanayin da yay maganar kuma ya ke dubana ba ƙaramin kaɗa ƴaƴan cikina yay ba, ina kallo ya zura hannu a aljihu ya ɗauko kwalin sigari ya buɗe ya ɗauki ɗaya, sannan ya ƙyasta lighter ya kunna, zai kai baki kenan na miƙe da zafin nama na ƙwace ina yin jifa da ita. kamar zan fashe da kuka nace, "don Allah kar kasha, ba zan iya ganinka kana shan abunda zai cutar da kai ba. Kazo mu bar nan wurin don Allah". na faɗa ina kamo hannunsa don mu tafi. a tsawace yace da ni,"kar ki ƙara cemin Yaya, ni ba Yayanki ba ne". "shikenan ba zan kuma ba. Amma sai ka faɗa min sunanka idan ba haka ba ni kuma bazan daina ce maka Yaya ba, tunda kai ɗin ka girme ni ka yi sa'a da Yaya Abba, tarbiyar gidanmu bata koyar damu faɗan sunan na gaba damu ba gatsal". Ƙwace hannunsa yay anawa yana doka min tsawar da tasa naja baya babu shiri, yana faɗin, "ki tafi ki barni ko. Nace miki bana da suna bana kuma da sunan Baba, banda kowa, n
🏠