NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 29 of 98

, kuma Allah ya ganar daku. Sai da Baba ya gama nuna mana komai na gidan sannan kowa ya wuce part nasa. Ina shiga side namu na raka Gwaggo ɗakinta, na nuna mata yanda ake amfani da duk wasu abubuwa musamman ma na banɗaki, ni ɗin ma ba kowanne abu na san ta kansa ba sai dai na jarraba musamman Ac. Duk wannan abun gwananintar da nayi ma ta ban burgeta ba, Sai da tayi min tsiyarta da ta saba. Harda cewa ai ruwan zafin hita da akasa yake zuba a famfo da gangan aka saka don ya salluɓe ma ta fata ne saboda an san ba iya amfani zata yi da shi ba, to ita a cire shi kawai. ni dai bance ma ta komai ba, ita kanta dariyar ƙeta take min harna gama na fito. Ɗakina na wuce kai tsaye, ina shiga na hau cire kayana domin yin wanka saboda duk a gajiye nake. Wanka nayi da ruwa mai ɗumi sirke da turaruka masu ƙamshin gaske, da aka jere su a toilet ɗin, ban wani jima a ciki ba na fito, ina fitowa na shafa mai da kuma faran powder. closet na nufa na zage domin ciro kaya, cak na tsaya ina riƙe da baki na saboda mamaki, kamin na buga tsalle na kurma ihu saboda daɗi, ashe shiyasa Baba yace babu buƙatar mu taho da kaya, mu bada duk waɗanda muke da su, kayan na shiga dubawa ɗaya bayan ɗaya, shegun kaya ne na alfarma kamar wata amarya aka zuba min a ciki sunfi set 30, Kuma duk abayas sunfi yawa dama sune favorite nawa, ban san lokacin dana zube kan gado ba ina hawayen farinciki ina kuma kwaranyo Baba adu'a, oh ni Sabina ban taɓa mafarkin tsintar kaina a irin wannan daular ba, ko da kuwa a gidan miji duk kuwa da ina fatan samun miji mai yalwar arziƙi na halal, sai gashi ashe zanyi katari da shi tun a gidan ubana, lallai arziƙi na ubangiji ne, shike badawa da hanawa a duk lokacin daya so. Wata dark blue abaya na ciro mara nauyi na saka, sannan nabi lafiyayyan gadona na kwanta, nan take kuwa bacci yayi awon gaba dani. Bani na farka ba sai da ana sallan isha'i, da sauri na diro akan gadon tunawa da nayi banyi sallar magrib ba, ina toilet ina ta ma kaina dariya, Ƴar ƙauye an haye gado anji laushin katifa, naji daɗin baccin da ban saba yinsa ba. Ina zaune bisa sallaya ina karatun qur'ani sai naji landline ɗin dake aje a drowern gefen gado na ƙara, banma lura da zamanta ba sai ayanzu, na miƙe da sauri na ƙarasa don ɗauka domin nasan kiran baya rasa nasaba da Baba tunda dai shine yay mana connecting baici ace kowa na da numban kowa ba. Ina ɗagawa naji Baba yace, "ki fito parlo ki same mu". Na amsa masa da, "to Baba". Daga haka shi kuma ya kashe wayan. ina gyara zaman veil na fita zuwa parlo, yanda na sami duk ƴan gidan kowa a zaune kan kujera yaran kuma a ƙasa, na san magana ce mai muhimmanci Baba ke so yayi damu. wuri na samu na zauna nan ƙasa da gefen ƙafar Gwaggona, sannan na ɗago da kaina na gaida su Umma. Anty na washe min haƙora ta amsa min gaisuwar tawa, saɓanin Umma data amsa min a ciki-ciki kuma fuska a turɓune. Baba yay gyaran murya yace da Yaya Abba yayi adu'a. Bayan gama adu'a Baba ya fara magana akan abinda yasa ya tara mu, maganar duka akan nasiha ce da kuma faɗa akan zaman lafiya,. Ƙwalla na taruwa a idona nace, "insha'Allahu Baba zaka same mu da yin abinda kake so, ko domin farincikinka da kuma kwanciyar hankalinka". Yace da ni, "Yauwa Sabina haka nake son ji, Allah yayi miki albarka. Dama nasan ke baki da hayaniya". na amsa da, "amin". Cikin farincikin adu'ar da yayi min. kishin wannan adu'ar yasa ƙannena suma suka ce, "insha'Allahu Baba, ba zamu yi abinda zai ɓata maka rai ba". Amma ba wai don sunyi niyya ba saboda da yayi maganar babu wadda tayi yunƙurin magana. Anty ma tace, "karka damu Baban Abba, adu'an kawai da zamu yi shine Allah ya bamu zaman lafiya. Amma ni ta ɓangarena babu wata matsala". "nima haka". Umma ta faɗa murya can ƙasa fuskarta na nunawa da abinda ke cikin ranta. Sai da kowa ya gama magana sannan Gwaggo ta gyara zamanta, ta taɓa kafaɗata tace, "ke hayo nan". Na miƙe na hau kujera kusa da ita na zauna, ta kuma dubana tace, "kinji daɗin zaman?". Nace ma ta, "ehh Gwaggo". ta dubi Yaya Abba tace, "kai Abba tashi ka kashe min wannan na'urar sanyin, kasan ina da mara lafiya, ba zai yiwu ni a ruɓar dani ba, ita kuma Albarkar tawa da nake ji da ita a bar min ita da jinya". Yayi kamar bai jita ba yaci gaba da danna wayarsa, domin yasan sarai rigima ce irin tata yasa tace a kashe, gari dai bana damuna bane babu sanyi ko kaɗan, Yanzu haka zafi-zafi ake, to amma ni kuma jikina baya son sanyi ko kaɗan, idan kowa zaice yana jin zafi ni kuma zance sanyi, ita kuma Umma jikinta irin shirgegen nan ne, bata shiri da zafi ko kaɗan, duk sanyin da ake zaka same ta tace a kunna mata fanka ko kuma ta fito shan iska, Ko bini-bini kaga ta yayi mi mafici ta hau firfita, yanzu haka ma saboda yanda ta ɓaɓɓashe iska na shigarta ta ko'ina yasa Gwaggo tace a kashe Ac. ta haɗe rai ta kuma cewa, "Abba dan ubanka Auwalu dake gabana a yanzu, nace ka miƙe ka kashe min na'urar bada sanyi ko". Baba yace, "kai Abba ba magana ake maka bane". Sai a sannan ya miƙe yaje ya kashe Ac'n ya dawo ya
🏠