NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 28 of 98

na masu aiki, sai ɗayan da babu kowa. Nan ya kuma zagayawa damu zuwa wajen parking lot, wayyo Allah nah, wasu tsadaddun motoci ne cikin wata rumfa kamar a ƙasar turai, in taƙaice muku dai ginin gidan kamar a saudiya. Baba ya nuna min wata arniyar mota fara mai tintend glass ƙirar lambogini, ya juyo ya dube mu ƴaƴansa mu shida, yace" ina kike Sabina". Na matso kusa ina faɗin, "Gani Baba". Maƙullin mota ya miƙo min, nasa hannu na amsa, abinda nake rayawa a raina shi kuwa ya tabbata. Domin buɗar bakin Baba cewa yay dani, "wannan farar motar taki ce Sabina". Kan ubancan, ai ban san lokacin dana buga tsalle nai sama na dire ƙasa ba, na kaiwa Gwaggo wata muƙura na ƙanƙameta, saura kaɗan ya rage ta zube ƙasa na riƙo kayata, daɗiɗin duniya ya gama baibayeni, ihun murna nake ina kwaranyowa Allah godiya daya mana wannan arziƙi, na sake ta na dawo wurin Baba, a kunyace naje jikinsa na rungume shi, adu'a nake masa da kuma tarin godiya, shima yasa nasa hannu ɗaya ya rungume ni yana sanya min albarka. Hmm wani abun dariya sai kunga matan gidanmu, yanda suka kumbura kamar an hura baloon tana jiran fashewa, kowacce sai faman aika min da saƙon harara take, baƙin cikinsu na daɗa fitowa ƙarara, har Umma ta kasa danne zuciyarta tace. "to amma Alhaji ga sauran yara a gabanka sai ita ɗaya ne zaka ma kyauta daga zuwanmu, kuma kyauta ma harta irin mota mai shegen tsada, motar da sai a ƙasar turai ake ido huɗu da ita". cikin rashin nuna gane lissafin nata yace,"banda abinki Hajara ai cikinsu itace Babba, suma za'a basu amma ba yanzu ba". Baba na shiru Gwaggo tace, "to shi mai sunan Sahibina ba zaka bashi bane?". Baba yace, "shi da yake magajin gida Gwaggo, ai ragamar komai na hannunsa, da kansa zaizo ya zaɓa". tai wani murnushi na ƙulawar sannan tace,"auto yanzu naji bayani. Tunda ka gama da marayun ƴaƴana, can ta matsewa sauran, su samu ko kar su samu ko a katarina". Ta dubi Yaya Abba, cikin mutunci yau ake masa magana tace, "mai sunan Sahibina zo ka zaɓa ka dirje, kamin ƴan baƙin ciki su haɗiya zuciya su mutu ba suga arziƙinka ba. Hakan ba zai min daɗi ba sam". _Hmm Ya kuke ganin zaman wannan gida zai kasance?_ _Ina Alhussain ya shiga?._ _shin ko zaiga takardar da Sabina ta bar masa?._ _Ko zasu ƙara haɗuwa?. idan da rabon zasu ƙara haɗuwa to aina?_ *Please Comment, Vote and Share.**AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(10)* baba ya girgiza kai, a yanayin yanda Gwaggo tai magana fuskarsa ta nuna rashin jin daɗi, to amma babu damar yayi magana, dan yanzu zata dire masa tace dama shike ɗaure musu gindin zaluntar marayu, duk wani abu da suke da sanya hannunsa a ciki, shima dama ba ƙaunarmu yake ba, kuji fa, wai mu da ubanmu amma abu kaɗan zaiyi za tace baya sonmu. Ni dai da har yanzu daɗi bai gama saki na ba tuni na nufi motana na buɗe na shige ciki ina dubawa, shi kuwa Yaya Abba na daga zaune kan wata kujera ya zuba ido yana kallon abinda ake. Anty da ta ƙware wajen iya kissa nan da nan ta kawar da baƙincikinta ta hau borin tayani murna, Anty macece da ta tsanemu sosai ni da Yaya Abba, don da tana da ikon kawar damu da tuni ta aikata hakan, amma kuma fa duk wannan ƙiyayyar ta ƙware wajen iya kissa da makirci, domin bata taɓa nunawa tana ƙinmu a gaban Baba, Ta inda tafi Umma wayo kenan, domin ita Umma agaban kowa nunawa take bata son ƴaƴan mijinta. Shi yasa Baba idan zaka kwana dubu kana ce masa Anty tayi Laifi baya yarda, Ita kanta Gwaggo da ba ta yarda da laifinta, saboda Anty makirar macece, Kuma ko laifi tayi to tasan hanyar da zata wanke kanta, amma itama tun a inda Gwaggo ta rafkowa lamarinta, ranar da tace Ya Abba ya shigar Mata ɗaki. Anty ta taho inda nake tana ta fara'a tana ce min, "Masha'Allahu mota tayi kyau sosai, inye su Sabina an zama ƴan gayu, lallai arziƙi mai daɗi, gaskiya na tayaki murna wallahi, Babanki ya gwangwajeki ƙwarai matuƙa, duk randa aka fara driving ni za'a fara ɗanawa, sai ki masa adu'an Allah ya ƙara wadata arziƙinsa ya kuma kare shi daga sharrin maƙiya mahassada, kema kuma Allah ya rabaki da sharrin ƙarfe". Duk tana faɗaɗa fara'arta take tayani murnar, wanda sam bai kai har ƙasan zuciyrta ba. hmmm amma kunsan me? saboda baƙar mugunta kunsan kuma abin ba don Allah take ba, hannunta na kan wuyana tana bani wani mugun mintsini, da naga tana neman raunana min wuya sai na fito a motar ina yaƙe domin shegen mintsininta ya shigeni, na sauke hannunta daga wuyana na riƙe a hannuna, inama ta murmushi nake cewa, "ameen Anty na gode sosai". Na faɗi hakanne saboda Baba dake tsaye a wurin, nima kuma cike da mugunta na ganyarata ma ta mintsini a hannunta dake cikin nawa, ba shiri ta janye hannunta tana yaƙe da dukkan alama ya shigeta kamar yanda nata ya shige ni. Na juya wurin ƙannena nace su zo su ga motar, dan suna tsaye ne kamar gumaka, to dake kowacce ta ɗauko halin uwarta haka suka zo suna leƙa motan suna tayani murna, fuska babu yabo babu fallasa, ni dai a raina nace oho muku, ni bana riƙo da irin yanda kuke min
🏠