NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 27 of 98

da damuwa, yanzu sai hankalinsa ya tashi. Duk yanda naso ɓoye damuwan abun yaci tura, domin kuwa ina zuwa Baba ya shiga tambayana abunda aka mani, kamar nace masa bana son tafiyarmu sai kuma naga rashin dacewan hakan, na ɗago na dube shi nace, "Baba babu komi". "ba kya min ƙarya karki farata a yau, mene aka yi miki?". sai na tsinci bakina da faɗar abun kwata-kwata babu lissafinsa cikin kaina. "Baba ina fargaban zaman mu da su Aunty ne". Yace na taso na dawo kusa da shi, cike da kulawa da kuma lallashi yake ta bani baki har naji zuciyana ta fara sanyi. Washe gari tunda ƙarfe takwas Baba ya kira waya yace to mu shirya ƙarfe sha ɗaya ne zamu tafi. zai aiko mana driver ya tafi damu, shi kuma zai tafi da matansa. Ina jin hakan nayi maza na faɗa wanka, cikin sauri na shirya na fito na gillawa Gwaggo ƙaryar data hau ta zauna akai, domin kuwa ce nayi ma ta Malam Albani ne ya kira yace yanzu naje makaranta suna son ganina, da yake zancen na makaranta ne bata musa ba tace,"Sai kin dawo Allah ya kiyaye, amma kiyi sauri kin dai ji abinda gyatuminki yace". "insha'Allahu yanzu zan dawo Gwaggo. Amma fa sai kin bani kuɗin mota saboda nafi sauri, kinga bada Farhana zamu tafi ba, koma da ita ne ɗin motanta ya lalace". Nan da nan ta kunce gefen zanenta ta ɗauko dalleliyar ɗari biyar ta bani, yanzu tana ji da tashen kuɗi, saboda ko jiya Baba dubu biyar ya bata da daddare. Ina fita na tari mai napep ya kaini Sharaɗa, a mazaunin Yayana a wurin nace ya ijje ni, na sauko na taka na ƙarasa zuwa wurin, ina ta dube-dubena da lalube na ban ganshi ba banga inuwarsa ba, ji nayi kamar na kurma ihu, idona ya ciko da hawaye, cikin zuciyata nake rayawa ko dai Yaya ya daina zaman wurin nan ne saboda ni, tunda yace na bar zuwa wurinsa naƙi, lokaci guda hawayen da nake ƙoƙarin dannewa suka sami nasarar gangarowa, nasa hannu na goge, shikenan yanzu yay min nisan da bazan kuma tozali dashi ba kenan, yanzu nasan yana can yana shan tabarsa, naji zuciyata kaman zata fito waje saboda ɗacin da take min. Sai kuma nayi wani tunani, Yayana zai iya tsere min ne a iya lokutan daya san zan iya zuwa wurinsa, amma tunda ba shi da ko'ina jazaman dare yayi zai dawo wurinsa domin kwanciya, Da sauri na buɗe jakana na ɗauko wata takarda da nai rubutu tun a gida mai ɗauke da taƙaitattun bayani kaman haka. _ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya Yayana, don Allah idan kazo ka nemi waya ka kira ni, zamu bar garin kano mu koma abuja da zama, ina maka fatan alkhairi. Ƙanwarka Sabina._ sai daga can ƙasa na zuba numbobin wayana guda biyu, wayar da a daren jiya Baba ya bamu ni da Yaya Abba. Kangon na shiga na sami inda zai iya katari da ita daya shigo na soke a wurin. Tukunna na fito na koma cikin napep ɗin muka juya, damuwar duniya ta tarar min aka, gefe guda rashin sanin taƙamaimai halin da Yayana ke ciki, ɗayan gefen fargabr zamanmu da Matan Babana, daga Anty har Umma babu mai sona a cikinsu, ko me na tare musu oho, sai dai nafi alaƙanta hakan da irin son da Baba yake min shine yasa Anty ta tsaneni, ita kuwa Umma haushinta da ni sunyi zaman kishi da Mamana. har ƙofar gida ya ajeni, lokacin da naje driver'n mu har ya iso a cikin mota ƙirar Sienna mai azababben kyau, ta burgeni sose sai dai yanayin damuwan da nake ciki ba zai barni nuna jin daɗina ba a fili, amma mamaki na cewar motar mallakinmu ce bai barni ba. Ina shiga Gwaggo na cewa, "yauwa kin dawo". "ehh". Shine nace da ita a taƙaice ina goge hawayen gefen fuskana. Na wuce zuwa ɗaki tabi bayana da kallo tana karantar yanayin nawa. "ke lafiya kuwa, ko wani abun ya faru a makarantar ne na ganki a haka?". Gudun kar ta hauni da tarin tambaya sai nai maza na ɗau buta na faɗa toilet. Na wanko fuskana kana na fito ina ƙaƙalo murmushi, ina kallonta nace, "Gwaggo wai har an fito". "ehh ke kaɗaima muke jira. ina tambayanki kin mani shiru baki bani amsa ba, nace lafiya naga kin dawo kamar wadda aka yowa akaina uwa da uba sun mutu lokaci ɗaya". "Gwaggo na biya ne munyi sallama da Farhana". tana taɓe baki tace, "uhmm shine idonki yay wannan jawur ɗin haka. to naga dai kashin awakai ma suna rabewa bare ku da zaku iya ziyartar juna a duk sanda kuka so...kai Wannan lokacin aurenku kwai lusin". Ƙarshen furucinta ya bani dariya wai looking zata ce shine lusin. Mu uku muka ɗunguma zuwa mota, Yaya Abba a gaba ya zauna, mu kuma muka shiga baya. Da la'asar muka isa Abuja, gidanmu a wani estate yake na manyan mutane, cikinsa baki ɗaya gidaje ne na alfarma, kai daka shiga kaga estate ɗin masu muƙami, a gida na tsakiya mai lamba uku mukai horn, aka buɗe mana tangamemen gate ɗin gidanmu, ya ilahil alamina, Aljannar duniya kenan, mai karatu karka so kaga haɗuwa da tsaruwar gidanmu, wai tun bamu shiga cikinsa ba kenan, ta ko'ina fitilu ne ke haskawa, yayin da wasu haɗaɗɗun flowers ke mana maraba. Part part na gidan ya kai kusan 7, nan Baba ya fara mana lissafi, part ɗaya nasa, ɗaya ni da Gwaggo, ɗaya na Anty da ƴaƴanta, ɗaya na Umma da nata yaran itama, sai na Yaya Abba, sai kuma
🏠