o kusa da ita muna ta jera mata tambaya. sai cewa Baba tai, "wallah Auwalu ina tunanin tafiyar nan ne na bar bazawari na, Ya'u mai kayan miya mutumin nan na ƙaunata har ransa, sai dai bazan iya cin amanar Sahibina, domin kuwa har Aljanna shi ɗaya ne zaɓina. Yanzu dai shi Ya'u ka bashi haƙuri kace ya nemi wata amma ban yaudare shi ba, babu yanda na iya ne da ƙaunar Sahibina, duk wanda na aura bayansa tabbas naci amanar ƙauna". Kunyar maganarta a gaban Baba yasa na miƙe na wuce ɗaki ina dariya, banma san lokacin da Baba ya tafi ba, sai can na fara bacci naji shigowarta itama zata kwanta.
To haka muka fara shirye-shiyen tafiyarmu, ni dai duk bana cikin hayyacina, idan ka ganni kamar wadda tayi sati tana rashin lafiya, duk na faɗa, ramin idona ya ƙara zurfi. Tafiya ce ta farinciki amma ni babu wannan farincikin sai tarin damuwa daya farma ni, walwalata duk ta tafi, nayi wani suku-suku dani, Gwaggo na lure dani amma bata ce min komai sai dai ta bini da ido tana faɗin, "hmmm". Farhana itace mai kwantar min da hankali idan ina damuwa, itama yanzu bata tani saboda tana cikin damuwar zanyi mata nisa, ni kuma ina fushi da ita. Ko gidanmu bata zuwa yanzu, idan ta kirani a waya ma ƙarƙari tace, "Ina fatan kina lafiya". Da zaran nace ma ta, "ehh Lafiya, hope kema lapia?". shikenan zata kashe wayanta ba tare da ta bani amsar tambayana ba. Yauma naje wurin Yayana na dawo, cikin ɗakinmu na shigo na sami Gwaggo na haɗa sauran kayayyakinmu, kasancewar gobe ne tafiyan mu, na nemi wuri na zauna na haɗe kai da gwiwa ina rera kuka, kun san mene ya sani kuka? Yayana! Karo na huɗu kenan yau ina zuwa wurinsa bana samunsa, babu shi babu dalilinsa, babu kuma wanda zan tambaya yace min ga inda yake, wannan dalilin yasa hankalina tashi, na nemi natsuwar zuciyata na rasa, sai aikin bugawa da sauri da sauri da take, tambayar da nake wa kaina wai anya zan iya ci gaba da numfashi ba tare dana san halin da yake ciki ba? ina ya tafi tsawon wannan kwanakin? Na rasa amsar hakan, sai na kuma fashewa da kuka, ina rayawa a raina in har Baba ya dawo zance masa mu fasa tafiyar nan har sai zuwan ranar da Allah ya dawo da Yayana, idan yaso sai na fa ke masa da wata ƙaryar dana san zai ɗoru akanta, tunda duk abinda nace yanayi.
Ina wannan kukan ne naji Gwaggo na cewa dani, "ke ɗago ki kalle min nan ki bani amsa sai ki koma ki ɗora daga inda kika tsaya". Tana faɗa da nuna halin ko'in kula akan kukan nawa, wanda ni kuma hakan ke ƙara bani haushi, dan atleast ina so a kula dani a wannan lokacin. "yo baiwar Allah ina miki magana ne fa, kuma nasan kin jini amma kinyi uwar kunnen shegu dani". ta kuma cewa dani, sai a sannan ne na ɗago, a tunani lna wani abun arziƙin zan gani, sai ta wani nuna min gajeran wandon Yaya Abba tana faɗin, "kema naga ƴar ƙwallo ce, za ki san takan amfanin kayan, wannan naga ya tsufa da yawa zai yiwa Abba amfani ko nasawa almajirai saboda naga mazaunansa duk sun ɓuɓɓule, kuma wannan rigar ma naga hammatar ta ɓeke, kuma duk bashi-bashi suke, na bayar ko na bar masa kayansa?". Haushi baisa na bata amsa ba, na maida kaina naci gaba da kukana, sai dai a wannan karan kukan zuci ne nake bana hawaye ba. ina jin Gwaggo na doka tsaki tana faɗin, "karki bani amsa ɗin. Idan kinji haushi kin amsa ke ɗin ba rainona bace, miskila kawai uwar nurƙufanci, kici damuwarki ke kaɗai tunda babu wanda ya isa ya tambayeki abunda ke damunki ki faɗa masa. Ni kuma idan na ƙara tambayanki tagwagwa ta gwagutse min". Har dare Gwaggo bata sake kulani ba kuma nima ban kulata ba, ni haushina ɗaya akanta da taƙi zuwa ta lallasheni naji sauƙin abinda ke damuna, sai dai ina jinta tana ta kai komon haɗa kaya, tana yi tana waƙarta cikin nishaɗi, tai waƙar Mamman shata da ɗan ƙwairo, ta kuma juya tayi ta yarensu na buzanci. Idan tayi ta gaji ta hau mitar ni da Yaya Abba bamu da tausayi sam, tana tsohuwa da ita amma mun barta da hidimar haɗa kaya, to walle ba don ta gaji da wannan gidan mai rufin kwano da yoyon ruwa ba, sai dai a fasa tafiyar. haka Ina jinta da Yaya Abba ya dawo yana tambayarta abincin dare, tace yaje ya duba kitchen akwai daddawa ya daka yay kwaɗo idan zai iya ci kenan, idan kuma ba zai iya ba ya bar mata abinta idan aljanun kaina sun sake ni ƙila ni naci, idan kuma duk ba zamu ci ba sai a barshi ya zama rabon almajiri, domin itama baci zata yi ba, ita da abinci sai na sabon gida. Baba daya zo yaji ni shiru ban fito ba, suna tsaka da hira shi da Gwaggo da Yaya Abba yake tambayana ina ina, tace da shi, "tana can ƙuryar ɗaka tana fama da aljanun miskilancinta, yau ban san uwar da akayi mata ba har suka zo ɗaukan fansa. Ƙilan kai idan ka kira ta tazo tunda suna jin maganarka sa tafi, amma ni da basa gani na da gashin ido ko ta kaina ma basa bi". Tana maganar ne tana shan raken da Yaya Abba ke ɓare mata. Baba ya ƙwala min kira, na ansa ina miƙewa, ban fita ba sai dana saita natsuwa ta, na sami guntun ruwan ledan pure water na wanke fuskana, saboda a rayuwata bana so naga Baba ya fuskanci ina ɗauke