azurtaka da shi, the more kana badawa the more kana ƙara samu. Hadisi ne fa guda karka rama sharri da sharri...". Ai tun bai kai ba Gwaggo ta dakatar shi, tana jefa goro a baki tace, "kai ba dama a fara magana sai ka nemi yanda zakayi ka kashewa mutum zuciya da faɗin Allah da ma'aiki. To naji na yarda amma fa da mutum guda zamu tafi, kaje goben kaiwa Addagana magana ita kawai nace bance da wannan mai zubin sauron ba. Domin ita a rayuwarta sam bata da mutunci, itama Addagana arziƙi ɗaya taci ta taɓa sammin gishirin miya amma wallah da bazan yarda ta ɗanɗani arziƙinka ba Auwalu, saboda matar nan lokacin zaman mu iya shaƙa na shaƙa a wurinta, to da yake ma ni ɗin ba kanwar lasa bace sai muka yi dai-dai da ita. Itako waccen mai yanayin dusar awarar ko bayan raina ban yarda da sisinka ka kashe mata ba, domin ta cutar dani iya cutarwa saboda tana gani na ƙwaila dani a lokacin, haka ta haƙa rami ta binne borkono da citta da sauran barbaɗenta ta ƙyallo mu ta mudubi ni da Sahibina amma da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai kaidinta ya koma kanta, hakan bai isheta ba sai da tayi nasarar haɗani faɗa da shi na tsawon mako guda, ya daina min magana ya daina saurarona. Kai Allah ya isa tsakani na da Hussaina, insha'Allahu sai ta wayi gari idonta ɗaya ya koma ƙeyarta na gaban kuma ya ma ce". ta faɗi hakan tana matsar ƙwalla, Baba kuma na bata haƙuri, ni da Yaya Abba muka tafa muna kwasar dariya muka ce, "Gwaggo; Gwaggo; Gwaggo; ikon Allah...Hajiya Gwaggo a daina ruƙo dan Allah, duk abunda ya wuce ya riga ya wuce, shekaru aru aru kinƙi cire abu a ranki". ta ɗago ta kalleni aka wurgan harara aka ce, "Sabina ina jiye miki ranar da zaki wayi gari ki kalla kishiya a cikin gidanki, ina mai faɗa miki karda ki sa ke kizo wurina na baki tofin Allah tsine don kifi ƙarfinta, saboda kina ɗaya daga cikin masu cutar da zuciyata, duk sanda nake bada labarin zamana da kishiyoyi maimakon ki tausaya min, a'a sai dai ki bushe da dariya kamar wadda aka bugawa guduma a tsakiyar ka jini da ƙwaƙwalwa suka gauraya suka haɗe. Ko da yake yau ai kin nuna min matsayi na a wurinki, tunda mutuwar Sahibina ma baki iya cewa Allah ya jiƙan rai ba sai dariya to ai kuwa babu abun alkhairin da za ki iya min". ta dubi Baba shima ta jefe shi da harara tace, "kai kuma saboda ƴarka ce shi yasa ba zaka iya tsawatar mata ba akan tsiyar da take shuka min. Wannan yarinya ai da miji ɗaya muke aure baƙin cikinta ne zaisa na bar mata gidan". Baba yace, "Gwaggo ke da jikarki ai bana shiga zancen ku ba. Kefa kika ce duk wani mai ƙaunarki to ya zuba muku ido a sha'aninku ke da ita, saboda tsakaninku ko aure ba zai raba ba, ƙaunace ta har abada". tace, "wannan magan kuwa na soke ta a yau ɗin nan. Saboda itama halin Hussaina gareta, a fuska su nuna suna yinka amma a zuciyar su kamar su kasheka, ta bayan gida su dinga maka mugun ƙullin da zasu daina ganinka a raye". Ina dafe ƙirji nace, "kai Gwaggo yanzu duk wannan mugun halin ni ɗaya, Ki sassauta min mana kona sami rangwamen zafin zuciya". "karki samu sauƙin zuciya ki shekara ki shekare a cikin zafinta ba damuwata bane, mara kirki kawai". Yaya Abba yace, "Gwaggo mita; to wai ita Inna Hussaina me tayi miki haka ne da kika sanyo ta a gaba, kika kasa mancewa da abunda tai miki tun kina amarya". sai ya riƙe haɓa yace,"kai Allah ya raba mu da riƙon abu a rai irin naki". ai yana rufe baki ta furzar da goron bakinta ta hau sababi,"au wato ni ce ma na sanyota a gaba kenan. To dan yayar ubanka bari kaji abinda tayi min, matar nan saboda baƙar azzaluma ce, na wayi gari wani dare na aza sanwar tuwo, nazo kaɗa kuka bani da ita, gashi ana ta ruwan sama bare na aika yara a sayo min, haka na dinƙa safa da marwa a tsakar gida ina gudun Sahibina ya dawo ban kammala girki ba, Ashe idonta na kaina, taje ta ɗauko kuka a ɗakinta kamar ta Allah ta bani, ina godiya ina jin daɗi nazo na kaɗa miya, tun ina kaɗawa naji jiki na yay sanyi saboda duk babu yauƙi amma sai na barta a ko tsohuwar ajiya ce, sai da Sahibina yazo cin lafiyayyan tuwon dana tuƙa, miyar kuka tace shani kaji daɗi, ashe ƴar tahalikar nan lalle ta bani na kaɗa, tana jin Sahibina ya fara faɗa ta fito tana ce min kayya amma Hannatu wannan abu baiyi daɗi ba, dama sai dana ce miki karki saya wannan kukar bata da kyau ashe ma ƙarshe lalle ne, da tun farko kin karɓi guntuwar dana baki da ba haka ba. kai kuji min baƙar makira, ai ranar naga ƙarshen makirci da iya kissa ganin idanuwana biyu, ranar dai ban ƙwaci kaina ba a wurin Sahibina ba, amma nima dana tashi nayi ƙundun bala sai dana juye mata Maɗaci rabin kwano a cikin damun kokon safe, akan hakan sai data karɓi farar takarda a wurin Sahibina, tsabagen farinciki sai dana yi sadakar ƙuli... Saboda haka wallahi ba za'aje Babaja da ita ba, sai dai ta dawwama a ƙauyen ɗan kande". ta dubi Yaya Abba dake dariya cikin ƙufala tace, "ɗan banza mai kama da ƙosai". Wani abun mamakin sai gani muka yi Gwaggo ta fashe da kuka, duk sai kuma hankalinmu ya tashi, na mats