kuma maganar Farhana data kutso cikin shirun da nai yasa ni rufe ido ina sauke numfashi, tukunna furucin nata daya fito ya tsaya a iska ya sami damar shiga kunnena.
_Masu Karatu what do you think will happen on this trip?_
_ta yaya zamu fassara kalaman zuciyar Sabina?_
_kuna ganin akwai yiwuwar ƙara haɗuwarsu da Al-hussain kamin tafiyarta?_
#Vote.
#Comment.
#Share.
#Mikiyawriters*AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(9)*
"Sabina tun a washegarin ranar da idanuwanki suka sauka akan ɗsn wiwin kan bola na kalli wani abu acikin ƙwayar idonki akansa, sai gashi ayau abunda na gani a saman fuskanki ya ƙara tabbatar min da shi...Sabina a haƙiƙanin gaskiya ba tausayinsa kike yi ba, sonsa kike, irin son da kika kasa ganewa balle har ki gasgata shi". Nai mata wani kallo na rashin fahimtar maganar tata sannan nace,"ina kika dosa kenan? i din't get you well". tai wani guntun murmushi da ya tsaya iyaka leɓenta sannan tace,"wanda kike kira da Yayanki mana...Sabina Whether you agree or not; you love him. Kuma irin son da kinyi zurfi a ciki, since za ki iya shiga wannan yanayin na tashin hankali becouse you are going far away from him. Tun a ɗazu fa ina lure da yanda Mood naki ya sauya lokaci guda bayan kin gama murnarki, kuma dana gama karantar fuskanki, i saw nothing beyond love full of compassion". Naja wani uban dogon tsaki, wanda yasa har mai napep ɗin dake janmu sai daya juyo ya kalle ni. Cikin masifa nake ce mata,"kina raina min ajawali da yawa Farhana. Wai me kika ɗaukeni ne hala ma tukunna, kawai kin bi kin Haɗa da wani hasashenki mara kan gado kin dage akan cewan Sonsa nake. Well, I dont like him at all, I just know I feel very sorry for him. And I can do anything to see that I change his life to a world of happiness unlike the one he is in now". sai ta saki wata dariyar ƙeta tana kallona tace, "ta ya kenan?". ta kuma harzuƙa ni, na wulla mata harara na ɗauke kaina, ina kallon waje nace da ita, "I just told you karki kuma cewa ina sonsa, otherwise kuma zamu yi faɗa". "ke wallah bazan bar cewa kina sonsa ba, ai labarin zuciya a tambayi fuska, ba wai na ƙirƙiro na faɗa ba ne". Na kaɗa kaina ban kuma ce ma ta komi ba, the way I heard her hypocritically laughed, saina tsaida mai nepep ɗin na sauka, dan ba zan iya tafiya da ita tana ci gaba da faɗan wannan banzan zancen nata ba. Allah yaso na fito da sauran kuɗi a hannuna na bashi, ina jinta tana min magana nai mata banza, saboda ma karta takura ni nayi saurin tsallaka titi, har cikin ranta nasan ba taso hakan ba, to amma kuma ya ta iya, dama ni na nema mu tafi tare kuma nace na fasa. Wani mai napep ɗin na kuma tara na faɗa masa unguwarmu, yana sauke ni ƙofar gida mukai karo da Ya Abba, shi ya biya kuɗin motar saboda ni babu a hannuna. Fuskata a turɓune na shigo ina sallama a ciki, sai dai duk ɓacin ran da nake ɗauke da shi, show ɗin Gwaggo da Baba sai ya kawar da shi, take na fara ƙyalƙyala dariya. Sai a lokacin ne ma suka san da shigowata, Baba ya dube ni zai yi magana Gwaggo ta riga shi tana ce min, "mutan kan naki sun sauya miki ra'ayi kenan?". Ina zama kan kujera nace, "ɓata min rai tayi shi yasa na fasa binta, dama ba wata uwar zata tsinana min ba, bare ta sani gaba tana min dariya kamar taga mahaukaciya sabon kamu". tace, "oho miki dai, mai jure ma halinki sai ita ɗin. Ke nifa da ni ce ita da tuni mun jima da gama ɓaɓewa dake, yo ina dole a nan, zamaninmu idan naga ƙawa na min iya shege saboda taga ina sonta sai na nuna mata ba'a haifi wanda ya haife ta bama". "to su Hajiya Gwaggo Allah yasa ba ke ɗin bace, kuma Allah yasa bata nan bare ki zugata. Nima fa Gwaggo ko ni ɗin, da kece ƙawata yasin ba zan iya zama dake ba". Ai tun ban rufe baki na ba tace, "yo ga mai mugun hali ke kuwa ai dole kice haka. Yanzu ai idan baki zauna dani ba kya zauna da matan ubanki da basa ƙaunarki". Yaya Abba dake shigowa yace da ita, "don zamu koma can ai ba yana nufin zamu zauna gida ɗaya dasu bane". Gwaggo ta taɓe baki tace, "to dan masu iya magana ai bani na faɗa ba, ubanka shi ya faɗa gashi nan a zaune sai ka tambaye shi". tana maganar tana hararsa. Sai kuma taci gaba da wa Baba faɗa tana cewa, "nan inace lokacin da Allah ya jarabceka da karayar arziƙi, cikin ƴaƴan su babu wanda yayi yunƙurin taimaka maka har zuwa yanzu da muke ciki, ni kaina daga lokacin suka bar zuwa gaishe ni saboda baka da abinda zan sanya kayi musu. Amma kake ambaton zamu tafi da iyayensu, saboda gaka wanda yafi kowa zuciyar imani, to ni ban yarda ba". Ni dai ban gane akan mene suke magana ba, amma yanda naga Gwaggo ta rikeɗe nasan maganar kishiyoyinta akai, domin Allah'n daya halicci Gwaggo bata ƙaunar sunan kishiyoyinta, sai kace yanzu ne ta ke zaune da su suke bugawa, idan tayi wani abunma sai kai zaton ko ita ɗaya ne aka taɓawa kishiya. Baba ya numfasa, cikin magana ta sigar lallashi yace, "Gwaggo ai ita rayuwa idan zakama mutum abu karka dubi halinsa, duba Allah sai kayi masa, kuma idan Ubangiji ya