aggo bata gama lazimin da take yi ba, sai da ta gama sannan ta juyo da kallonta kanmu tace, “oh yau naga abinda ya ishe ni, yo bakwa iya zama sai dai ku tsaya min haka aka ƙi ƙam sai kace kunzo ɗaukar fansa”. Farhana tayi dariya ta zauna kan kujera, ni kuma na tsugunna a lokacin da nake jin kamar nai fiffike na isa ga Yaya. Farhana tace da ita, “Allah ya huci zuciyar Gwaggo, ina abin ɗaukar fansa anan, sauri muke yi shisa muka ga ba sai mun zauna ba”. Gwaggo ta ajiye carbin dake hannunta tace, “to naji sarakan iya tsari, meye ne dama?”. tana tambayar ga Farhana ne a lokacin da take kafeni da ido. na ɗan ɓata fuska gudun karta harbo jirgina nace,"bafa ni kika tambaya ba da kike jiran amsa daga bakina". ta watsa min Harara kana ta juya inda Farhana take tana faɗin, “ina jinki Farhana meye ne?". “Gwaggo dama tare da Sabina zamu je gida gobe insha'Allah sai mu dawo, ina so zata rakani taron get together da zamu yi ne a school”. Gwaggo ta gwame baki tana kauda kai, sannan ta samu damar furta,“ta jira ubanta ya shigo in yaso sai taji daga gare shi”. nasan sarai ta faɗa ne dan bata so naje, kuma ba zata iya cewa Farhana a'a ba, domin a rayuwarta in akwai abunda bata so shine na kwana ba kusa da ita ba. na yamutse fuska nace, “Gwaggo dan Allah”. na rufe ido ina ƙara faɗin,"Gwaggo, Gwaggo, Gwaggo wai ce nake kece ke da iko da ni, to kuma why zaki ce sai Baba ya amince". tayi ƙwafa bata ce min komai ba, ta ɗau carbi taci gaba da lazimi. duk na ƙosa ta bani attension ɗinta na fara yi mata magiyar dana saba, amma gaba ɗaya sai naga ta sauya fuska, har Farhana ta miƙe tace ita kam tafiya zata yi, nai saurin riƙo hannunta ina roƙonta sai ga Baba yayi sallama muka amsa mashi, ya samu wuri ya zauna, yadda ya ganmu ya sashi faɗin, “duk yadda aka yi akwai abin da kuke buƙata ko...ko kuma wata matsalar ce?". ni dai nayi ƙasa da kaina, Farhana kuma tace,“Baba dama..dama muna son zuwa..”. Baba yana murmushin manyance yace, “ina jinku meye ne dama?”. tana sosa gira tace,"Baba dama ina so mu tafi gidanmu ne tare da Sabina tunda kun kusa tafiya ku barni". ina kallon yanda Gwaggo tai saurin juyowa tana kallon Farhana da ɗumbin mamaki, tama kasa rufe baki, saboda jin furucin daya banbanta da wanda ta faɗa mata a ɗazu, fuskarta kuma na haskawa da rashin yarda damu, dan yanda maganar Farhana ta banbanta tasan dole kwai wani abu da muke ɓoyewa. laɓɓanta suna motsawa da son faɗin wani abu amma sai bata faɗa ba, ta ɗauke kai ta kama ƴan waƙoƙinta na ɗan ƙwairo. "mai zai hana ni ƙin amince miki Farhana, ba ke ɗaya da kuke aminan juna da Sabina ba, ko dan mutunci da karamci irin na mahaifinki babu abinda zaki nema ki rasa daga gareni. dan haka kuje Allah yay muku albarka, gidan ku ai kaman gidansu ne itama...kya gaida Abban naki don na kwan biyu bamu haɗu ba". godiya muka yi masa sannan muka miƙe muna nufar hanyar fita. “au ko sallama don iya shege ba zaku min ba, shi ne kuka miƙa kai kamar ƴaƴan zabi”.dariya sosai Baba yayi, ita kuwa Gwaggo ko dariya bata yi ba, Farhana tace, “wallah Gwaggo kin iya yanka, salon muce wani abin kice mun ce”. “yo ai gaskiya na faɗa, ina kallo fa ko kaya bata ɗauka ba. Ko haka zata tafi babu kaya? ko da yake zumuɗi na gaba da suturta jiki ai”. na manta da Baba yana wajen nace da ita,"Allah Gwaggo kin fiya sa ido, haka zanje ɗin ni don Allah ki ƙyale ni...Baba mun tafi”. ina faɗa naja hannun Farhana zamu fita. Gwaggo ta kuma cewa, “yo ai sai kiyi kuma, da wuyanki kamar mariƙar lema, na san dai kayan Farhana ba zai maki ba ko ɗaya, dan haka ki dawo ki ɗauki dai-dai ke”. duk wannan maganar da take saboda dai a fasa tafiyar ne, dan haka ban tsaya tanka mata ba balle ta sami abinda take so, naja Farhana muka fice, muna jinta tana faɗin,"Allah dai na kallonku, ni bance sai kunji tsorona ba amma kuji tsoron Allah". A mota kuwa muna tafiya Farhana sai dariyar kalaman Gwaggo takeyi, yayin da ni ko kaɗan dariya bata zo min ba, tunanina kaf bai wuce neman mafita ba. idan muka bar garin nan sai yaushe zamu ƙara dawowa?, idan na tafi ba tare da nayi sallama da Yaya ba shin idan na dawo zan sake ganinsa?, ban ɗau tsawon lokaci tare da shi ba, amma ya fara sakewa na san da wannan, ba kullum nake kasancewa da shi ba, amma a jikina nake jin rayuwarsa ta fara sauyawa, haka zalika ajikina nake jin sauyin rayuwarsa na gab da zuwa, gab, kusa-kusa, kusan da bata da wuya wurin Allah, sai da a wurinmu ƴan adam...to amma abunda na kasa ganewa shine, tun a ranar farko zuciyata ke faɗa min kece wannan ƙaddarar, kece ƙaddarar da zaki sauya rayuwarsa, silarki komai nasa zai warware, wataƙila yanzu wataƙila sai an ɗau tsayin lokaci. kuma ayau da wannan abin farin cikin ya samemu, tun bayan dana gama murnata, haka zuciyar tawa ke faɗa min, ki tafi da shi, karki barshi anan, acan inda zaki je, acan inda zaki je zaren wata ƙaddarar zai warware, zuwa Abuja alkhairi ne...abinda zuciya faɗa tana ƙara faɗa kenan tun a ɗazu.