gane nufinki ba, "me kuma zai maida mu Baba Ja?". Gwaggo bata taɓa cewa Abuja sai dai tace Babaja, saboda acewarta ai cin mutunci ne yasa aka lanƙwaya sunan ubanta aka maida shi Abuja daga Abubakar. Baba yaci gaba da mata bayani, "ehh Gwaggo zamu koma Abuja ne da zama saboda ƙarin matsayi da ma'aikata ta bani". "kai don manzan Allah??". ta faɗa har tana zamowa daga wurin zamanta. "wallahi kuwa Gwaggo, an bani muƙamin MD na ma'aikatar wutar lantarki. Sun bani gidaje biyu acan Abuja, da motoci uku, da kuma miliyan uku, ta buƙaci na ɗauki iyalaina mu koma can da zama gaba ɗaya nan da sati guda".
_Please Share, Vote and Comment let me know what you think._*AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(8)*
Gwaggo ta rangaɗa wata uwar guɗa data amsa a gaba ɗaya cikin gidan, hamdala take ta jerawa ga Allah, har da miƙewa ta taka rawa irin tasu ta tsofaffi. "Allah maji kukan bayinsa...kai gaba ɗaya ma na rasa wacce iriyar murna zanyi". Yaya Abba daya shigo yace da ita,"tsohuwa kina ta ihu fa dare ne, maganarki har soro, dama ke muryar kamar cakwaikwaiwa". tace da shi,"umm Abba ai yau sai dai kayi da wata bada ni ba kam...dan lokacinka dai ban da shi". Murna nake yi sosai kamar babu gobe, amma ɓangare guda na zuciyata yana tunanin halin da zan shiga zai kasance. wannan mutumin, wannan bawan Allah'n da Allah ya haɗani da shi ta ayar da ban san fassararta ba, wannan mutumin da nake jin kamar ina da wata babbar alaƙa da shi, mutumin da babu ƙarya tun a ranar farko nake jin tasirinsa a tare dani a kullu yaumin, mutumin da tunanins akaɗai a sanda bana tare da shi yake sakani zubar hawaye saboda rashin sanin dalilin wanne hali yake ciki.
Gaba ɗaya murnar da nake yi tsayawa tayi cak, saboda tunawa da nai zan tafi na bar Yaya, tunanin daya haifar da wani ɗan ƙaramin tashin hankali a zuciyata, ta fara bugu kamar zata fito waje. dai-dai ta nutsuwata nayi saboda ina gaban wanda bana son ya fahimci yanayin da nake ciki. dan duk wanda ya kallen a yanzu dole sai ya ɓazgo wani abun, Ina kallon Farhana ma yadda ta kafe ni da idanunta, tana son gano sirrin dake zuciyata, amma sam na kafa na tsare saboda yanzu sai ta ruguza min tsari, dan ita bata iya sirri ba. Ganin hakan yasa ni furta, “Yauwa Baba barin zuba maka ruwan alwala, na kalla magriba ta gaba to”. ina gama faɗar haka na miƙe na nufi hanyar fita, idon Farhana na kaina har a lokacin, yayin da Gwaggo take ta faman zuba kamar kanyar da ta samu jeje da iska. Ina fita na samu damar dai-dai ta nutsuwata, amma fa sam hakan ya gagara, don tuni hawaye sun fara zubo min, dama ni Allah ya hore min kamar famfo, hawayena a wajen tausayi da rauni basu da wahalar sauka. ina zuba ruwan na dawo, na samu gefen Gwaggo na zauna ina sauraron hirar ta su, ba wani fuskantar hirar nake ba, tunanina da neman mafita bai wuce yadda za'ayi tafiyar nan tare da Yaya ba. kallon Farhana nai, nayi mata sigina da ido, saboda mu fita mu samu abin faɗa, amma sai naga ta basar kamar bata ganni ba. Ganin haka yasa na miƙe na kama hannunta ina faɗin, “tashi mu shiga ciki”. Hannuna ta kama muka nufi hanyar ɗaki, muna shiga ta dube ni sheƙeƙe tace, “ya dai uwar ɗorawa kai damuwa”. harara na watsa mata ina faɗin. “ke fa ƴar rainin hankali ce Farhana, meye nufinki dama?”. ta ɗan harare ni tace, “Oh oh jimin rainin tunani, ke zan tambaya dai meye ke damunki, naganki sukuku, don tun ɗazu na fuskanci damuwar da kika shiga bayan kin gama murna”. na ɗan ja ƙaramin tsaki kaɗan na miƙe tsaye ina safa da marwa kana na kama ƙugu na tsaya nace, “ba zaki gane ba Farhana, kin san halina sarai, ina da saka damuwa akan abinda nasa a raina but..”. ban ƙarasa faɗin abinda zance ba Gwaggo ta bankaɗo labule tana faɗin, “an kira sallah ko baku ji ne wai, ko kuwa ba zaku yi ba ku duka?”. nace, “kaii Gwaggo mai baiwa, yo waye yace maki bamu ji ne wai, banda abinki Gwaggo kuma anyi ta rashin sallar kenan?”. tace, “oho maki marar kunya, na sani ko ba zaku yi ba, tunda ku ko yaushe a cikin jini kuke. abu da a zamaninmu iwar haka ma yara kamar ku basu fara abin mata ba sai an wuce haka...amma ku yaran yanzu nan da nan sai ku nemi kufi ƙarfin kan mutum”. “gaskiya Gwaggo Allah ya baki baiwa, baiwa ba ta faɗe ba, ina ruwanki ne ke kam, don Allah kije, na san abin da kike nufi gamu nan kije abinki”. na faɗa sanda nake ƙara riƙe ƙugu. Farhana kam dariya kawai take tana faɗin, “ni kam dramar ku tana burge ni, muje muyi alwala kafin ta dawo”. muna idar da Sallah Farhana tace zata tafi, Gwaggo ta zuba mata tuwon shinkafa da miyar kuɓewa tace ta kaima Hajiyarsu. Ta karɓa tana godiya, har mun kai soro naja na tsaya ina faɗin,“muje kice ma Baba zan kwana a gidanku in yaso sai mu tattauna abinda zamu tattauna kinji”. Farhana ta ɗanyi jim kafin tace, “Gwaggo dai nasan zata yarda amma kina ganin Baba fa?”. “ke kam muje zai amince insha'Allah”. na faɗa da ƙosawa, da wani abu dake bin jikina wanda ban san menene shi ba. muka koma ciki, Gw