NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 21 of 98

ci. Abba ba dai ni zaka nunawa tsiya ba, zaka ganta iya ganin idonka, dama kowa ai da ranarsa. Idan kaji haushi ka koma can filin ball ɗin su dafa su baka, ko kuma kaje can gidan su budurwar taka daka saci ɗankwalina ka kai mata matsayin toshin sallah saita baka...kana faman ɓoɗara hanci kamar gajeran wando, da wasu idanuwanka ƙifi-ƙifi kamar na ƙaramar touchlight ɗin masu gadi, har na zaka nunawa fushi Abba". Haushi ya tuƙe Ya Abba, don haka ya juya kawai ya fice yana jijjiga kai. Gwaggo tabi bayansa da ido tana murmushi tayi ƙwafa tace, "ɗan ƙwal uba dani kake zancen ai". Muna haka muka jiyo sallaman Baba, da sauri na sakko a saman kafita na fita cikin hanzari ina amsa sallamar tasa, kamin Gwaggo da Farhana su mara min baya. Yana zama kan kujera na ƙaraso da fara'ata ta nuna jin daɗin ganin mahaifina nace, "Baba sannu da zuwa". Ya amsa min da, "yauwa Sabina". Farhana ta ƙaraso itama tana masa sannu da zuwa. Lokacin da Gwaggo ta ƙaraso ta zauna kan kujera, Baba ya sauko ya gaida ita, tana amsa masa tana sanya masa albarka. Baba yace, "Mama mene ya haɗaki da jikin naki, yace kinƙi bashi abinci". "auto kaga masu ɗa, ai ban san kana tuhuma ta ba sai naga ka sanya mini ankwa, sai naji daɗin maka jawabi...amma yanzu ban ganka da kakin ɗan sanda ba ina zan san kana yi Awwalu. Abinci ne na dafa bazan bashi ba, har ni yaron nan zai tsulawa tsiya na roƙe shi nace yazo ya siyo min kayan miya Sabina na makaranta, amma ya buɗi baki yace ai filin ball zaije, koma ba haka ba ai yayi girman a aike shi wurin me kayan miya, ƴan mata ai sai su raina shi. Ranar haka na zauna ban girka na rana ba sai da Ƴar arziƙi irin albarka ta dawo, wadda tayo gadon kirki a wajen mahaifiyarta". Baba yace, "to ayi masa afuwa Gwaggo ba zai ƙara ba. ba'a horo da yunwa ke kika faɗa mana hakan, kuma shi idan baici anan ba aina zaici". ta taɓe baki kamin tace, "ya tafi can wajen matan ubansa yaci, ko kuma tunda Allah ya kawoka ka ciri ashirin ka bashi ya sayo awara, abincina ne dai yau Abba ba zai ci ba". Baba baice komai ba, dan yasan tun da ta kafe kam bata sauya ra'ayinta. ya dai kalla Ya Abba da ido sukai magana, nan ya tashi ya fita bayan Baba ya bashi kuɗi a ɓoye, in ba haka ba Yanzu Gwaggo sai ta kuma sauke masa sababi idan ta gani. Baba ya kira ni yace nazo, na taso na dawo kusa da shi, kasa ɗauke idona nayi akansa duban yanda naga yana ta zabga murmushi da alamu yau ɗin yan cikin farin ciki, don tunda ya shigo na lura da hakan, ni kuma abunda yake min daɗi kenan a rayuwata, naga mahaifina acikin farinciki da kwanciyar hankali. Baƙar jakar hannunsa ta laptop ya buɗe ya zaro wasu takardu ya miƙon yace na karanta. Habawa ai ina karanta layi biyun farko na miƙe tsaye nai wani tsalle nai juyi ina ihun murna, Farhana na fizgo na nuna ma ta itama, tsabar farinciki mun kasa ƙarasa karanta sauran rubutun. baki ɗayanmu tsalle muke muna murna, kamin daga baya na koma na zauna ina hamdala ga Allah, maimaitawa nake, "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah mun gode maka abisa ni'imar da kayi mana. Ya Allah kaci gaba da bawa mahaifina nasara a rayuwarsa". Gwaggo tace, "wai meke faruwa ne, ni duk kun barni a duhu, ko abin farincikin banda ni ya sama. An baki aba kin wani ƙwaƙwame ke kaɗai, ina ce dai ɗa nawa ne tunda sai dana haifa kika sa me shi a uba". nace, "oh Allah na! nikam yau gwaggo ban san me na maki ba. to gashi nan".Na faɗa ina tasowa na bata takardar. Sai da ta gama mani kallon sama da ƙasa kana ta karɓi takardar, hannu ta miƙa saman abun tv namu ta ɗauko akwatin glass ɗina, ta buɗe shi ta ɗauko glass ɗin ta ƙwaƙwuma a fuska sannan ta wani harɗe ƙafafu ta hau kallon takarda kace gaske karantawar take. Dariya muke so muyi daga ni har Baba amma gudun sababinta yasa muka gimtse kayarmu. ta ɗau kusan mintina biyu sannan ta sauke takardar daga kallonta, ta cire glass ɗin, tana faman juya takardar ta kalla Baba tace, "Kai Auwalu, tunda ta gama nata zagin kai sai ka sami damar min bayanin abinda ke ƙunshe aciki. Sarai ai kasan babu abinda na iya karantawar amma ka barta ta miƙo min saboda cin fuska, dama ranar nan tace min ni ai bana ganewa, kamar Addagana haka nake. Yo Allah na tuba duk lalacewa ai nafi wannan lukutar matar tunda ni nayi makaranar Allo. Ita yarinya ce har yanzu bata san mene kishi ba shi yasa take haɗani da waɗanda suka kusa rabani da mijina". O'o, niko na riƙe baki ina kallonta har tagama magana. Gwaggo ba dai mita ba, wannan zancen anyi wata da yinsa amma duk sanda ta tashi sai tace ai nace bata ganewa Addagana tafi ta jaa, kuma ba komai bane saboda na haɗata da kishiyarta. Baba ya numfasa yace, "Mama wannan takarda ce daga wurin aikinmu...". Ai tun Baba bai ƙarasa ba ta dafe ƙirji cikin tashin hankali tace, "na shiga uku na Auwalu ba dai sun kuma korarka bane, wannan ƙaddara da me tayi kama". tana faɗa tana shirin yin kuka. Ina dubanta ina gwame fuska nace, "kai Gwaggo hakanne zaisa kiga ina murna kuma. Abuja fa zamu koma". Tayi min wani kallon sheƙeƙe na ban
🏠