na warkewa sai gashi ya dawo yana kuma zayyana min irin soyayyar da yake min, Kuma fa ko da yana kwance kullum sai ya aiko azo duba mishi ni, in taƙaice miki dai ƙarshe ai sara mishi kawai nayi nace Sahibina ai kai bai kamata a kiraka da masoyin zuciya ba, da masheƙin rai da zuciya ya kamata a kiraka". "to fa! garin ya ya cancanci wannan sunan Gwaggo?". Farhana ta faɗa tana waro ido, tana ƙara tunzura Gwaggo. Ina duban Gwaggo ina dariya na miƙo mata hannu ta sammin goron sai ta make hannun nawa, yau harda su murguɗa min baki bayan harar da ake watsa min. Nan taci gaba da bawa Farhana labari, "ai ɗiyar Aljannah ya cancanci wannan sunan shi yasa na raɗa masa. Akaina fa yay faɗa da ƴan daba talatin saboda sun kawon hari, duk wuƙaƙen da suke tare dasu haka yay masu fata-fata, Ya kamo hannuna cikin kulawar so ya dawo dani gida, kamar zai yi kuka yake roƙona don Allah Sahiba karKi sake fitowa waje bare wani banza ya kuma kalle mani Ke, take a wajen naji wani ƙahon sonsa ya huda zuciyata ƙaunarsa ta nemi waje tai malemale, naja da baya na matso kusa da shi na yi masa kirarin so mai jijjiga ruhin masoyi, sannan na koma gida. Ina shiga na cewa mahaifiyata Adi, nifa Fillo zan aura, kowa daya ji haka sai da yayi mamakin abun saboda ada nace akan me zan auri wani matsolon rake, ai ƙwamma na sami ɗan'uwana usulin buzu kakkaura mai ƙwarin ƙashi na aura. Farhana ai banga so da ƙauna ba sai dana je gidan Sahibi na Sahibarsa, Kishiyoyi suka sanyo ni gaba amma sam Sahibina baya bi takansu, ni kuwa haka na dinga tsula tsiyata a gidannan ina gasa su son raina da tawa salon kissar, kuma fa gani ƴar figigiya amma haka na zame musu ciwon idanu. sanda na sami ciki na fara laulayi ai Kamar na zazzagawa kishiyoyina wuta a jiki saboda yanda Sahibina ke Tattalina kyace wata ƙwai". Gwaggo ta numfasa tana kuma fashewa da kuka tace, "Allah ya jiƙan Sahibina, ya mutu yana cikin mayen so na". Wayyo Allah cikina ni Sabina, yau nayi dariya na godewa Allah saboda dramar Gwaggo, na ƙara tsokanota da cewa, "to amma kuma Gwaggo ai tarihi ya nuna Kakanmu kamar yafi son Uwar gidansa Addagana, akace ma yana kan cinyarta ya mutu". Ba shiri naja bakina nai shiru saboda kallon da Gwaggo ta wurgo min haɗe da jefo min murfin bokiti. "to duk wanda ya faɗa miki wannan zancen ƙarya yake munafikin Allah ta'ala. Ke Sabina zanfa iya haɗa ki da D.P.O yau ɗin nan, saboda haka ki fita a idona, ke kiji wata makirar ƙarya, a gidan ubanwa ya mutu akan cinyarta, wanne shegen ne ya faɗa miki haka?". ni dama ba don komai yasa na faɗi hakan ba sai dan kunnata, saboda nasan yanda take tsakaninta da kishiyoyi, gashi dai shekaru da dama amma kamar waɗanda mijin ke aurensu yanzu. Gwaggo dai kamar nai mata me, haushin maganata da dariyata suka tsaya mata a rai. alhalin ita kanta wadda ake bawa labarin dariya ta ke, amma tawa dariyar ita ta zama laifi, na buɗi baki zanyi magana kenan ta dakatar dani cikin kwazazzafa. "ke kin san Allah zan miki adu'a bakinki ya tsaya a haka na tsawon shekara guda, sarai kin san na gada a wurin Kakana na biyu na ɓangaren kishiyar Babata Adi, kasancewar sunyi zaman mutunci sai muka zama kamar ƴan uwa, don haka ahir ɗinki da ni a yau ɗin nan. Ki tambayi kishiyata Hussaina kisha labari, da tayi min ba dai-dai ba sai da ta kwan talatin da bakwai ba tayi kashi ba, shima banda ta bani haƙuri sai dai ta shura a haka". Nai shiru ban kuma magana ba, ina latsa wayar Farhana. Ina jinsu Suna ta shan hirarsu. Ya Abba ne ya shigo ɗakin ɗauke da sallama a bakinsa, muka amsa masa ya shigo ɗakin ya tsaya yana zuba hannayensa a aljihu. Sannan ya shiga buɗe kwanuka da alama abinci yake nema, ya ɗago yana kallon Gwaggo yace, "ina abinci na?". a hasale tace da shi,"Ka kawo ka aje ne, ko kuma aure na kake da zaka shigo min gida har cikin ɗakina kake tambayana abinci". Ya kama ƙugu ya riƙe yana dubanta babu alamar wasa a fuskarsa kamar wani mijin gaske, yay gyaran murya yace, "naji koma mine kice, ni dai ina abinci na, yasin yau na kwaso yunwa baki ga yanda nai wani laushi ba kamar lagwani". Ta harare shi tace, "To ai kai dama lagwanin ne, saboda kullum a yamushe kake Kamar lawashi. Ni wannan yaro don dai Allah yay maka halittar maza ne amma da sai nace mace ne kai". Ya Abba ya ɓata fuska yace,"nifa sai na rubuta miki takarda akan irin wannan cin fuskar da kike mani. Kuma idan kina wasa ki kuma cewa tak ki kalla idan ban sake ki ba...ya zaai a gaban ƙannena kike faɗa min irin wannan maganar". Gwaggo tayi tsaki ta doki cinya tare da tura masa mazaunai tace masa, "karka fasa saki na ɗin, kaine zaka ji haushi. Saboda ina fita zan sami rangaɗeɗen saurayi mai rai da lafiya yayi wuff da ni, kai Abba kana raina wannan Sauran yarintar dake jikina ko, to Rabon kaji na aure shugaban ƙasarku ne". Ya Abba ya kaɗa kai kawai, idan ya biye tata abincin daya dawo ci ba zai sami cinsa ba. Ya dube ni yace, "ke tashi ki ɗauko min abinci na". Kamin na miƙe Gwaggo tace, "ke yi zamanki, yau kam sai dai ya nemi wani gidan yaci abin