ra da medical glass, ciwon idon dana gada a wurin Kakata mahaifiyar Abbana, ita kuma Farhana na gayu ne, wanda bata iya rabo da shi a kullu yaumin.
zuwanmu bakin jar motar da ta ke mallakin Farhana ce muka tsaya, sannan Farhana ta buɗe booth ta sanya ledar kayan hannunta, tukunna na buɗe gaban motar na shiga, bayan Farhana ta rufe booth sannan itama ta zagayo ɓangaren mazaunin driver ta shigo ta zauna tana yiwa motar key. "wash Sister wallahi na gaji da yawa yau, kai ni kam sai na kwan biyu ban kuma zuwa wani biki ba". na faɗa a sa'ilin dana ke kunna Ac'n motar. "yanzu ai zamu ƙarasa gida, nima da kika ganni duk a gajiya na ke, buƙatata kawai na jini cikin shower". cewar Farhana tana karya kan motar zuwa kan titin da zamu hau. na ƙara cewa,"ke kin san ma za ki samu ruwa a gida, ni yanzu na koma da wuya idan ba sai na fita neman mai ruwa ba, saboda anguwar mu muna cikin matsalar ruwa...Gwamnati gaba ɗaya bata tausayin rayuwar talaka, ba wuta ba ruwa a inda talaka bawan Allah ke rayuwa, kai Allah kayi mana magani". na numfasa kamin na ƙara cewa,"Allah sarki Gwaggo nah nasan yanzu tana can tana tsumayin dawowa ta, kuma kin san fa sai da ta ce ka da na jima". Farhana ta ce,"kinga ba wannan bama, ni damuwar ma Allah yasa mu tarar da telan nan yana shago, kar musha wuyar banza ga wannan uban go slow ɗin, kalla fa tun ɗazu danja ta ɗaga amma har yanzu motoci sun gagara wucewa". "to amin dai, Allah ya nufemu da ritsa shi a shagon ɓuyarsa". na faɗa ina yatsine fuska alamar gajiya sosai a tare dani. Direct sharaɗa muka wuce shagon da Momin Farhana ta aikemu amso ma ta ɗinki.
Ba ƙaramin takaici muka ƙunsa ba da muka je ba mu sami me ɗinkin ba, tsabar haushi ma ko jiran yaron shagonsa dake mana bayani bamu yi ba muka fice dukanmu rai a ɓace, danni har ji nai kaman na gwaɓe bakin saurayin dana san ƙarya ce kawai yake gilla mana. tun fitowarmu daga shagon nake ta duban jefi-jefin jama'ar da ke layin, kasancewar sa layi ne da bai tara mutane ba, sai ƴan tsirarru haka, unguwa ce bata masu kuɗi ba amma kamar wata babbar estate shiru kake ji. nace da Farhana, "ni kam kiyi sauri mu bar layin nan ina tsoronsa, kin san yanzu kidnappers sun yi yawa a gari, mutane ba tsoron Allah". itama tace,"hmmm sauri ai kece zance kiyi, kina tafiya kamar ba za ki taka ƙasa ba, kee ni ko dai kina da matsalar ƙafa ne?". na harareta sannan nai murmushina mai sanyi ba tare dana ce ma ta komai ba, muka ci gaba da tafiya hannunmu riƙe dana juna kace mu twins ne, sai dai muna gab da ƙarasawa inda mukai parking naji ƙafafuna sun tsaya cak daga tafiyar, yayinda hannuna ya zame daga cikin na Farhana, na bi gefen haguna da kallo kafin naji ƙafafuna na jana suna tafiya da ni zuwa wani wuri, wani wuri da ban san me zai iya faruwa ba idan na riske shi, na bar Farhana naci gaba da tafiya tana ta maganarta ita ɗaya duk tunaninta tare muke. sai da tayi gaba sosai sannan ta fahimci tafiyar tamu ba tare muke ba, ta waigo da kanta sai kawai taga babu ɓurɓushina ma a wajen, kuma a wannan lokacin ɗaga idon da zatai can gefe ta hangeni ina tafiya cikin sauri-sauri har ina harɗewa, saurin da a duniyarta zata rantsewa wani bata taɓa ganin nayi shi ba tun yarintarmu.
tsananin mamaki sai yasa ta riƙe haɓa, cikin zuciyarta na ayyanawa da me zanje yi a cikin bola?.
"Sabina! Sabina!! ke Sabina wai ina ki ke neman zuwa haka? bola fa naga kina neman shiga, wai kin yi hauka ne? Keee!!".
zan iya cewa a sama-sama naji abunda ta ke cewa, dan haka hannu na ɗaga ma ta ta baya kawai ba tare dana yi yunƙurin tsayawa ba, kuma zagin da ta ƙunduma ta wurgo min shi yasa ni ɗaga ƴar muryata ina cewa da ita,"Farhana ba fa bolar zan shiga ba, ki biyo ni ko ki jira ni yanzu zan dawo".
Farhana ta sauke numfashi tana zubawa sarautar Allah ido, tabbas banda tasan wace ƙawarta lallai zata iya cewa aljanu ne da ita ko kuma tana da ciwon hauka ne, amma a yanzun ma ba zata ƙi cewa Sabina ta sami matsala ba. Gani tai sam ba zata iya barinta ita ɗaya ta shiga cikin wannan bolar da shigarta babu abinda mutum zai kwasowa kansa fa ce musiba, hakan yasa ta bi bayanta itama cikin sauri, abunda ya ƙara bata mamaki kuma hangenta da tai ta tsaya gaban wani mutumi da ke zaune saman bulon wani kango a jikin bolar. Farhana tai turus ta tsaya domin ita kuwa al'amarin ya fara bata tsoro, gwara ta tsaya daga nan ɗin idan taga abin bana tsayuwa bane saita arta ana kare, domin ta fara tantama da lafiyar ƙwaƙwalwar Sabina.
Saurayi ne kyakykyawa na ajin ƙarshe zaune saman bulo a bakin wani kango, shekarunsa zasu kai 27-28, shi ba fari ba kuma shi ba baƙi ba, hasken sa dai-dai misali, jikinsa sanye da yadi me arha ruwan madara wanda ya amshi jikinsa, a kallo ɗaya zaka yiwa kayan jikinsa ko da ace daga nesa ne ka gane cewar yadin a koɗe yake, irin koɗewa da jemewar da suka gaji da duniya, Farin silifas ne wanda ya ɗanji jiki sanye a doguwar ƙafarsa me ɗauke da zara-zaran yatsu, Kansa a ƙasa yake hannunsa riƙe da taba sigari, cikin ƙwarancewa yake zu