NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 19 of 98

ɗauko hasken Sahibina da ba'a san kalar da zaki kwaso ba, da har kike tsokanar wata, ki bar ganin Samari na aikin sunturi akanki duk tabarakin Sahibina kika ci. Ah tou". tai maganar dan ta ramawa Farahana, amma sai taji ba ki ɗayanmu mun sheƙe da dariya, Na buɗi baki nace, "Wai naci tabarakin Sahibinki, Abunda tarihi ma ya nuna shi Sahibin naki Kawu Baffa Sule ma ya fishi kyau, kinga kuwa in haka ne ai da an gani ajikin sauran Ƴaƴan nasa. Kawai dai shi Babana Allah ya zaɓe shi ne, gashi nan santalele kamar balarabe, Shi yasa ake kishi da shi, don ko Sahibin naki da kike koɗawa albarka". Na faɗa ina ƙunshe dariya ta saboda yanda naga Gwaggo na aika min wani kallo mai kama da harara. Gajeran tsaki ta saki tace, "Ki kiyayi ramata Sabina, shi gyatumin naki har kishin mene zanyi da shi, banda aikin wofi na haife shi kuma na kama kishi da shi". sai kuma ta ɗauko mifici ta shiga dukansa a ƙasa tana faɗin, "Kuma In faɗa miki ƙaryar tarihi ya faɗi abin kushewa akan Sahibina Allah ya jiƙansa da gafara. Ke idan a wannan zamanin naku ne ma ai sai na dinga tofe shi da li'ilafi ƙuraishin, ko da yake a wancan zamanin ma me aka fasa, yanda ƴan mata ke tururuwa akansa kamar ƙuda ya sami zaƙi tsabagen tsantsar kyawunsa da farin jini. Amma haka ya miƙe ya dire yace sai ni, haka ya dinƙa bani tabara ana aika min da yasin a gidanmu, Ɗan baiwa kenan wallahi shima Zaɓin Allah ne domin kuwa Allah ya bashi. Ai naga zallar soyayya a wurinsa, Allah sarki Allah yay maka rahma abin ƙaunata". Kawai sai ganin Gwaggo mukai ta fashe da kuka tana matse ido. Niko mai zanyi banda dariya da tafawa harda ƙwalla. "Allah ya jiƙansa, kice Dai Gwaggo kunsha ƙauna ke da Kakanmu". Farhana ke mata wannan tambayar tana ƙunshe dariyarta. "Hmmm". Gwaggo tace tana juyowa ta fuskanci Farhana."amin ƴar aljannah, ai ke kam mutunci ba daga nan ba, ki godewa Allah da baki ɗauko halin ƙawarki ba na rashin kirki". Farhana na daɗa riƙe dariyarta tace,"Gwaggo yau kuma Sabinan taki guda". Gwaggo ta harari gefena da cewar,"Wannan ai ƙaunar da take min a baki ne kawai... kina ganin ta haka sam bata ƙaunata. Yo banda rashin ƙauna ana zancen marigayi kina dariya saboda ɗibar albarka, ai yau Sabina ta nuna min matsayina a zuciyarta". Ni dai dariya nake kawai  bance mata komai ba, dan yanzu ina ƙara yin magana zata kuma hawa. dama Gwaggo sarkin zuba zance, sai dai idan baku zauna da ita ba, Nan ta hau bawa Farhana Labarin Kakanmu wato mijinta kenan. "ina faɗa miki Farhana ai naga zallar soyayya daga wurin Sahibina, soyayya ba irin ta ƴan yanzu ba irin ta aljanu. Babu irin kalar walaƙancin da ban masa ba amma bawan Allah'n nan haka ya nace yace idan babu ni sai rijiya. ke abokansa har ce masa suke babu zuciya a ƙirjinsa saboda irin wulaƙancin da nake masa. ni kuwa abunda ma yake ƙara ƙona min rai nake ci masa fuska idan naji yana faɗin wai in bani rijiya zai faɗa ko kuma ya rungumi tiransufo ma. idan ya faɗi hakan raina yana sosuwa, saboda lokacin ina jin tashen ƴan matanci, gani kyakykyawa gashina har gadon baya, idan ba kiyi min farin sani a matsayina na buzuwa ba to zaki rantse kice baƙar balarabiya ce, gidanmu fa Maza dandazo suke a ƙwar gida sai akai asuba ana jiran fitowata, ni kuwa dama ta samu nayi ta juya su kamar waina a tanda, tunms layi yazo kan Sahibina Allah ya jiƙan rai, shi dama ya kwashi buhunhunan rashin mutunci a wurina, amma don tsiya da tusa min takaici duk sanda nayi masa sai yace ai indai ba ƙona shi zanyi ba ya zama toka, to ba zai daina zuwa inda nake ba kuma ba zai fasa furta min soyayya ba. Watarana dana shirya masa mugunta, Ina jin ance yana sallama da ni Na kaɗa karkashi na fita ta bayan gida na sami dakalin ƙofar wani gida na sheƙa a wurin, Sannan na dawo naci gayu na yafa gyale, na fito waje ina tafiyan rangwaɗa sai faman yauƙi nake kyace tarwaɗa kin san mu buzaye bada ganan ba. Shi ko yallaɓai tunda ya ganni yake faman murmushi yana nuna jin daɗi, Ji yake kamar ya sure ni mu shilla sama, ina isa wurinsa na wani kashe masa ido ɗaya sannan nayi masa sigina da hannu ina masa nuni da ƙofar gidan da zamu yi zancen. Hmmm haka ya biyo ni sai wani nishaɗi yake a tunaninsa yau ya taki sa'a ya mallaki zuciyata ne bai san mugunta na shirya masa ba, ɗan Fillo'nka na hawa saman dakali jinsa kike timmjim ya zame ya faɗo cikin kwalbati, salati yake yana neman ɗauki ni kuwa sheƙa masa dariya nake kamar zararriya saboda mugunta, nayita iya kuɗina na kaɗa masa mazaune nace gobe ka ƙara dawowa inda nake". duk yanda naso dariya a wannan lokacin sai ya gagara, saboda yanda Gwaggo ta saito faranti a fuskata, jira take na ƙyalƙyale ta kwaɗo min. Farahana da biye ta dakakke sai ce ma ta tayi, "ohhh Allah sarki Kakanmu, amma dai daga ranar bai kuma zuwa wurinki ba ko Gwaggo?". Gwaggo ta jawo robar goro ta ɓalla ta Kai baki, tana tauna tana cewa, "ai ɗiyar Aljannah ina kai ki bana baroki, daga inda na sallamawa mutumin nan a faɗuwar da yayi sai da yay karaya biyu targaɗe ɗaya amma ya
🏠