NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 98

ishe ni ba”. Gwaggo tace, “au yo to ni ai nazaci baki ganta ba, kinga fa bana son iya shege, sai kace baku san juna ba, kai ku dai ko miji kuka haɗa iya ka abin da zakuyi kenan, Allah ya shirye ku to”. Miƙewa tayi tana faɗin bari nayi alwala, har ta kai bakin ƙofa ta ɗaga labule ta dawo tana faɗin, “au ke la ɗazu kuwa Farhana tazo zaku tafi, nace mata baki dawo ba, ƙila ko kin tsaya bada hadda ne”. saboda kar taja zancen da sauri nace, “eh, hadda na bayar saboda jiya ban bayar ba, kuma bana son tayi min yawa shisa”. “au to madalla, ai na zaci ko wurin ɗan iskan yaron can kika koma, dan ta kawon ƙorafin hakan”. Sai da zuciyata ta buga, bugun da ban taɓa jin tayi ba, zuciyata bata son ana zagin bawan Allah'n nan ko kaɗan. Rumtse ido nayi ta dubi Gwaggo da wani irin kallo, da ƙyar leɓena na ƙasa ya samu nasarar motsawa kana na sama ya motsa suka haɗu suka samu nasarar furtar kalmar a’a ga Gwaggo. Bata kuma yinƙurin cewa komi ba ta saki labulen ta fita. ni kuwa na dafe kaina saboda yanda naji yana sara min na furta,“Ya Salam!”.*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(7)* "kinga farar singlet ɗina?". muryar Yaya Abba ta amsa a cikin kunnena. "ban ganta ba, bani na kwashe kayan ba sai dai ka tambayi Gwaggo". na ƙaraso wajensa ina ƙara faɗin,"Yaya Abba dan Allah zuge min". ya kama zip ɗin rigata ya zuge min sannan yasa kai ya fice ya zabga mitar da baya rabo da ita. ban dai ji Gwaggo ta tanka masa ba kuma nasan saboda karta yi magana suyi da shine shiyasa ta share shi, ni kuwa da ina gyara naga singlet ɗin amma na manta inda na ajeta shi yasa nace masa ban gani ba, dan ina cewa ban san inda na aje ba na shigesu da jaraba yau. bayan na gama shirina na fita parlonmu da yake madaidaici, na zauna naci sauran ɗumamen tuwon da Gwaggo tace ta rage min, ina gamawa kuma na dawo ɗaki na ɗauki littafin da nayi renting shekaranjiya na shiga karatu, tun a daren jiya na gama karanta book 1 ɗin, Sumayya Abdulƙadir ce ta rubuta shi ina masifar son littafanfa. sai wajen sha biyo na miƙe, na fito falon ina gyaran ɗaurin ture kaga tsiyana sai ga Farhana ta shigo bakinta ɗauke da sallama. fuskarta na washewa da siririyar dariya ta ƙaraso inda nake, wanda ni kuma ganinta yasa na cukule fuska, na dakata da waƙar da nakeyi, ina faman cika ina batsewa, saita hannu tasa da nufin ture ɗaurin nawa tana faɗin, "bari na ture sai naga tsiyar". Na wani bankama mata uwar harara sannan nace, "da kuwa kinga tsiya ganin idonki". Tayi dariya tana kama hannuna da nufin mu zauna kan kujera, na turje ina daɗa nuna mata nifa ban bar fushi da ita ba. cikin daɗin baki ta kama cewa, "haba mana Sabina wai mene kike hakan...wai so kike sai duniya ta jimu ts mana dariya". ta faɗa tana duba na tare da manno min kiss a goshi. ganin dai kamar ba zan sauko daga kan dokin fushin dana hau ba sai fuskarta ta sauya zuwa damuwa, nan fara'arta ta ɗauke gaba ɗaya, ni kaina na sa ni Farhana na tsananin so na, haka nima, bama iya faɗan minti biyar bamu shirya ba, kai hasalima bama yin faɗan, mukan yi ƙoƙarin kiyaye duk wani abu na ɓacin ranmu, duk da cewar wani lokacin ni na kan kasa haƙuri amma ita ko menene haƙuri takeyi. sai dai a wannan karon ina mamaki da silar abunda yasa nake faɗa da ita har nake irin wannan fushin haka, fushi da ita akan mutumin da ban sa ni ba, na tsince shi ne kawai a hanya, har kuma nake jin zan iya rabuwa da ita akansa, bama ita kaɗai ba, kowanene gani nake zan iya rabuwa da shi muddin bai samawa Yaya lafiya ba. Na kauda fuskana gefe guda domin bama zan tankawa maganar da tai ba. tana ƙara riƙe hannuna da nake son ƙwacewa tace, "kinga indai akan Yaya'nki ne kwantar da hankalinki, daga yau ba zaki ƙara jin bakina akansa ba. Wannan alƙawari ne na maki". jin hakan yasa na juyo ina dubanta, idan na kalla shin maganartata da gaske ne, ganin na zuba mata ido ina karantar fuskartata yasa tace, "wallahi da gaske nake miki, ni bazan yarda wani ya lalata mana zumuncinmu ba. Tsakanina da shi Allah ya shirye shi kawai, ko ba hakan kike so ba?". na saki fuskata ina murmushi, kamar yanda muke yi ada yanzu ma haka mukai, domin kuwa tafin hannuna ɗaga na bata muka tafa ina faɗin, "yauwa ko kefa, yanzu naga haskenki". sai tamin harar wasa da cewa, "ji min walaƙanci, duk wannan uban hasken nawa baƙi kike ganinsa dama?". Ina dariya nace, "yo da kike wani kaurara hasken naki, ai na bogi ne tunda na bature ne". Ina faɗa cike da tsokana, ina kaucewa biyo ni da tayi. Har ɗaki ta biyo ni muna dariya, Gwaggo na linke kaya ta bimu da ido. Sai dana ɓuya a bayanta ta sami damar yin magana tana duban Farhana. "ƙalau kuke kuwa?". Farhana na riƙe da ƙugu take ce mata, "wai Gwaggo saboda kuturun walaƙanci ni yarinyar nan zata cewa fari na bature ne". "ai ba ƙarya nayi ba, uban tulin robobin mayukan ɗakinki na mene?". Ina dariyar ina magana kuma cike da tsokana. Gwaggo ce ta juyo ta dube ni, ta wani yatsine fuska kana tace, "kema ai banda Allah ya rufa maki asiri gyatuminki ya
🏠