NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 17 of 98

a saninsa da mu yasan duk ɗinmu bamu da hayaniya, daga ni har Farhana, wani lokacin idan har ana faɗa da ɗaya, ɗaya yakan shigar wa wani, gashi a wannan karon abinda ya bashi mamaki mu da kanmu muke faɗan. wanda ada saboda irin kyawun alaƙar dake tsakaninmu da yawan Malamai da ɗalibai zatonsu gida guda muke. Malam Hamza yayi gyaran murya ya dubi inda nake tsugunne yace,  “Sabina lafiya yau kam, kuda ba’a jin kanku sai kuma gashi yau anji?”. Bance da shi komi ba, saboda ina da saurin ƙwalla duk da nakan mayar da martani, amma a wannan karon muddin nace zan buɗe baki nayi magana to fa zan iya yin kuka, saboda irin kalaman cin mutumcin da aka dinƙa faɗa min, ana cewa Farhana wai dama tsiyar abota da ɗan talaka kenan, shi yasa tuntuni suke nusar da ita munafukarta ce ni, ba dan Allah nake zaune da ita ba sai dan kuɗin gidansu, ita kuma lokacin ban san meke shiga zuciyarta ba har ta ɗauki huɗubarsu ta yaɓo min maganar data tsayan a rai, wadda ba dan da kunne naji daga bakinta ba, wallah ba zan taɓa yarda ba. Malam  Hamza ya dube ni ya kuma faɗin, “Ko ba zaku iya magana ba ne sai nasa muku bulala, sanin kanku ne baku fi ƙarfin hukuncin makaranta ba". Farhana zata yi magana kenan nai caraf na tari numfashinta, saboda nasan idan na barta tsab zata iya faɗin abin da ya haɗamu. “Malam yau dama ban koma gida ba, na zauna bada hadda wurin Malam Ibrahim, tana ta tambayata, ni kuma yau banjin magana, ita kuma ta takura min da magana shine muka fara faɗa, kuma kaja mata kunne idan ta kuma gani na a irin wannan yanayin ta daina kula ni”. Malam Hamza yace, “to shikenan ke Farhana kinji abinda tace saboda haka ki kiyaye karku ƙara bari shaiɗan ya shiga tsakaninku, ku tashi ku bani wuri”. Farhana zata yi magana Malam Hamza ya dakatar da ita, na faki idon shi nayi mata gwalo wanda nasan ya sosa ranta, ta girgiza kai tare da yin ƙwafa muka nufi hanyar fita. Bayan fitar mu shi kuwa Malam Hamza murmushi yayi gami da girgiza kai. Kafin mu ƙarasa aji kuwa, muna tafe ina banka mata harara itama tana aikomin da martani a haka har kowa ya isa ajinsu. Ƙarfe shida saura kwata aka tashi, kamar kullum tana inda ta saba jirana, ni kuma na gama cin alwashin ko ita ne mai mota ɗaya a duniya wadda dole sai na hau zanje gida sai dai na shekara ban isa gida ba. Ina kallonta ta gefen ido, tana bina da kallo, ni kuwa har wani sauri na ƙara tamkar zan kifa, ƙafafuwana har sarƙewa suke yi, amma hakan baisa na daina sauri ba. Ina tarar mai napep nayi sauri na shige don ko bayanin inda zai kaini ban samu damar yi ba sai da nashiga muka fara tafiya. A ƙofar gida ya sauke ni inda ina sauka su Adda Karima suna fitowa ita da Mardiyya daga gidan mu, ko kallo Addan bata ishe ni ba bare nasan Allah yayi ruwan halittarta a wurin, da hanzari na ƙarasa da fara’a fal shimfiɗe kan kuncina na shiga gaida. Itama anata ɓangaren Murmushin baƙin cikin tayi asanda ta kafe ni da ido tana neman inda zata samu makusa, saboda macece wanda Allah ya dasa mata zuciyar kushe, akwai fara’a amma fa irin mai ɗauke da taɓe bakin nan. ta dube ni sannan ta dubi Gwaggo tace, “Wai ni Yaya me kike bama yarinyar nan ne gaba ɗaya sai ƙiba take kamar ana hura ta, billahillazi idan baka santa ba sai kace ba ita bace, ke duba min yadda take kumatu ta ke cika tana ɓatsewa kamar wadda take shan sha ka fashe”. Yadda ta ke sababinta ni kuma yana saka ni nishaɗi, ita kuma idan duniya akwai abinda ta tsana tana faɗa ina dariya, duk da kasancewar ta itama Kaka ce a gare ni, Gwaggo tayi murmushi ta dube ni tace, “Karima wannan kuma ai gaki gata, yo me zan bata ni kuwa, abin ma da ba wani ci take yi ba, gaba ɗaya makaranta ta saka ta gaba, ko baki kula ba yanzu ma daga can ta ke”. Adda Karima ta gwame baki tace, “kuma fa haka, ita wai huda-huda, gara dai ayi aure duk sa’anni sunyi sun dire ku kuma kunce karatu to ayi dai mugani, lafiya ƙalau”. Saboda tsabar gulma nacin ta bata samu damar amsa gaisuwar da nai mata ba sai da ta gama habaicinta. ni kuwa ina dariya nace, "7Adda Karima kenan, ke dai ba’a raba ki da abin faɗa, to abinda kema kina da iko akaina, miji ai sai kimin wannan abu ɗan sauƙi..”. Kafin na ƙarasa tuni Adda Karima tace,"abu ɗan sauƙi fidda wando ta ka, Sabina ai shikenan tunda haka kika ce”. ina jinta na shiga ciki, duk bakin Gwaggo idan Adda Karima tana wuri tofa nata mutuwa yake yi muɗus. Napep ɗin dana sauka shi ya ɗauke su, ita kuma Gwaggo ta dawo ciki daga rakiyarsu. ina ɗaki ina canja kaya Gwaggo tayi sallama ta shigo ɗakin, gefen gado ta zauna tana faɗin, “ina raba ki da mayarwa Karima martani idan tana maki magana, kinsan dai kaf dangi babu wanda ya kaita shiga abinda babu ruwanta, saboda haka ki kiyaye ta wallah”. Ina gyaran zaman rigata, na miƙa hannu na ɗakko hula na sanya akaina sannan na dubi Gwaggo nayi mata kallon tsaf nace, “to karki damu Gwaggo zan kiyaye, wai da naga itama matsayin Kaka take a wuri na shisa ma nake yi da ita, baki ga ita wancan ko kallo bata
🏠