NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 98

tace, "ƙawata wai ina kika je ne? Na biya maki ɗazun Gwaggo ke cewa ai baki dawo ba, sai nace ma ta ƙilan kin zauna bada hadda ne don bamu haɗu ba". "ummm". Shine abunda nace ma ta kawai ina maida kaina a window. "to daga ina kike?". "daga inda kika aike ni".Na bata amsa a taƙaice. Bata damu da sha re ta ɗin da nake ba ta kuma matsowa kusa dani, hannuna dake kan littafin ta dafa, ta fara mani magana cikin damuwa da kuma nuna kulawa. "Sabina tun muna ƙananun yara muke tare, mun riga mun zama tamkar ƴan'uwa, muna bawa junanmu shawara kuma mun zama sirrin juna. Shin mene yasa lokaci ɗaya wani zai sanya ki sauya daga yanda kike a gareni, kawai akan ina faɗan gaskiya...". "karki yaudari kanki da cewan kina faɗan gaskiya akansa, ko za ki Kawon hadisin daya ce ka aibata musulmi? Ina sauraron ki". Na faɗa idona tarr akanta. "babu". "to Kin san da cewan babu kenan amma kike taƙarƙarewa kullum kina aibata shi akan abunda baki da masaniya akai, ko kin san asalin rayuwarsa ne?". "ai ba wai ƙarya nayi ba. Zahiri fa na gani, don nace masa ɗan iska ko ɗan daba ai banyi ƙarya ba". "wallahi da ace kin san yanda nake jinsa a zuciyata ba za kike jifansa da waɗannan kalaman ba. Da kin san matsayinsa a wurina da tuni kin jima da rufe wannan dogon bakin na ki". Na faɗa ina kawadda da kaina bayan na jefeta da banzan kallo. Tayi wani munafikin murmushi sannan tace min, "wato Sabina idan banyi kuskuren hasashe ba son wannan ɗan wiwim kike ko?" .ta tambaye ni tana kafe ni da ido cike da rainin wayo. Tsaki naja ina faɗin, "Kinyi hauka ne hala? Taya za ki ce mani ina sonsa, To akan mene ma zan so shi? Kawai ban san shi ba ban san daga inda yake ba na wani kama sonsa, abunda na sani kawai shine ina tsananin tsausayinsa na kuma damu da shi". Murmushin rainin hankali ta ƙarayi tace, "to ai dama ke ba za ki gane ba, amma tuni kin faɗa a son wancan ɗan isakan, sai dai zan faɗa miki tun wuri ma idan haka ne karki bar abun ya girmama ki cire shi a zuciyanki domin ba zan taɓa yarda da hakan ba, tunda shi ɗin ba mutumin arziƙi bane". Sosai naji zafin maganarta a zuciyata, daurewa nayi na sha re ta ban saurare ta ba, sai ƙwafa da nake ƙasa-ƙasa. "kinsan Allah Sabina, idan har baki fita a harkan wannan ɗan shaye-shayen ba na rantse miki saina faɗawa Yaya Abba, wai akan mene zaki ke kai kanki inda baki dace da nan ba. Ke ni walla ma tsab zan iya ɗauko masa police su kamashi ai dama ɗan wiwi irinsa bai dace da zaman cikin anguwa ba". Nan ma shiru na mata ban tanka ta ba, haushin hakan yasa ta shiga zaginsa ta inda ta ke shiga bata nan ta ke fita ba. Babu zato babu tsammani taji na sauke mata zazzafan mari saman kuncinta. A zabure ta ɗago ido tana dubana da nake faman huci akanta. "tashi ki fita a ajin nan tunda bana ku bane". Na faɗa ina ma ta nuni da hanyar ƙofa. "ni kika mara Sabina? Akan wani banza ɗan iska wanda bakin uwa ya bishi kika mare ni?". Cakumar kwalar hijabinta na ƙarayi, raina a matuƙar ɓace nake dubanta, dukan mu huci muke tun ba ma yani. "Farhana kinyi kinyi karki kuma kiransa da ɗan iska, idan ba haka ba na rantse zan miki abunda bazaki taɓa mantawa ba. Kuma shi ɗin da kike kira ɗan iska bari kiji ya fiki matsayi a wuri na, wallahi ina mai gargaɗin ki karki ƙara kiransa da shege ko makamancin haka". Ta yarfar da hannuna dake ciwkwikwiye da Hijabinta. "ni kika mara ko? Za ki san kin mare ni, kuma kinyi da ƴar halak. Kuma indai ɗan iska ne yanzu na fara faɗa duk abunda zakiyi karki fasa". Cikin zafin nama na shaƙo wuyanta ina kaɗa mata kashedi. Kan kace mene wannan idon ƴan aji ya dawo kanmu, tuni akaje aka sanar da Malaman makaranta. _Short Update☹️. Anyway lets just say i don't feel motivated anymore🥴, like i just stop the typing mu huta gaba ɗaya ko? becx i dey see you people you dont like the story at all...ina gani daga comment & voting naku wanda yanda kuke yi baya encouraging nawa gaskiya...so please and please you guys should changed or you just tell me to stop westing my precious time._*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(6)* kamin a kawo mana rahoton Malam na kiranmu, masu jin haushin alaƙarmu da Farhana sai zugata sukeyi, mu kuwa lokacin shaiɗan ƙara buga mana ganga yake a kunnuwa, faɗa kamar ƙananun yara, abunda zamu iya rantsewa wani bamu taɓa yi ba tun wayonmu. gashi dai haushin hakan nake ji a ƙasan raina, amma kuma na rasa dalilin daya sa ko na nemi na huce sai zuciyata ta kuma ingizoni da zigar kar na raga mata, wataƙila shi Yayan da take zagi wani abu ne mai muhimmanci da Allah ya turo shi cikin rayuwata. kuma a hakan bakin Farhana bai mutu ba, dagewa take tana ƙara zaginsa, ni kuwa ina ƙara ƙuluwa har na rarumo wata kujera zan buga ma ta Allah ya kawo Malam Isma'il. Office ya kaimu, raina idan yayi dubu to kuwa tabbas ya ɓaci, sai cika nake ina faman batsewa. Malam Hamza principal ya shigo office ɗin ya gyara zaman shi akan kujera da hularshi irin ka fiya nacin nan, ya dube ni tsaf, sannan ya juya ya duba Farhana, a iyak
🏠