NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 15 of 98

anke magana da shi". "har ƴan gidanku?". sai yay ɗan jim kamin ya gyaɗan kai, wani ciwo dake ƙasan zuciyarsa na nunawa a fuskarsa kamin yace,"na faɗa miki ban taso na ganni ina rayuwa a gidanmu ba. zuciyata ma faɗa min ta ke wataƙila daga sama na faɗo". ayau gam na gama gasgata shi da wannan furucin nasa, dan haka ɗaya naji zuciyata ta gamsu da shi ɗin. muka ci gaba tafiya ina bashi labarin zaɓata da akai acikin waɗanda zasu yi musabaqa a wannna shekarar. #Vote. #Comment. #Share. #mikiyawriters.*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(5)* "Allah ya bada sa'a". abunda yace dani kenan, kuma har muka isko titi ba wanda ya ƙara magana cikinmu. ya faɗa min abunda bai taɓa yi ba iyakar tsayin rayuwarsa shine tsayar da mota ya hau, duk inda zaije ƙafarsa ke kai shi balle ma babu inda yake zuwa. ni kam na dage akan sai ya tsayar min, haka ya miƙa hannunsa na rawa ya tsaida me napep ɗin daya taro, daga hakan na yarda da maganarsa, dan kana kallon ma yanda yake tsayarwar da yanda yakewa mai napep ɗin magana zaka san frin shiga ne. "ɗan dakata Malam". yace da me napep ɗin sanda na shiga ciki na zauna shi kuma yana ƙoƙarin ja, sia ya tsare ni da ido yana kallona kamar ba zai ɗauke idonsa akaina ba. Yanayin kallon nasa yasa ni sadda kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna ina murmushi, ji nake kamar kar na tafi na barshi ko kuma kawai mu tafi tare, domin ina jinsa ne tamkar wani ɗan'uwana na jini. "Sabina". Ya kira sunana a hankali cikin zazzaƙar muryarsa. Ɗagowa nayi na dube shi tare da faɗin, "na'am Yayana". "kiyi haƙuri bani da kuɗin biya miki". Ina murmushi na gyaɗa masa kai, "karka damu Yayana, na gode". Yana kallon mai motar yace, "don Allah ka tuƙata a hankali, ka kula da ita amana ce na baka". Ya faɗa yana ɗauke hannunsa daga ƙarfen motar zai juya. nai saurin riƙo hannunsa da sauri ba tare dana sa ni ba, ya juyo yana kallona, nima ɗin kallonsa nake kaman zanyi kuka nace,"Yaya don Allah kazo muje gidanmu, bana son tafiya na barka anan". sai ya tala leɓensa da murmushi, a cikin magana ta rarrashi yace min, "kin kalla yanzu ai makaranta zaki je, ki bari sai kin dawo wataran sai mu tafi tare". Cike da murna da kuma zumuɗi nace, "da gaske Yayana?". Shi kansa ya lura da yanayin farincikin dana shiga, kansa ya jijjiga min alaman ehh da gasken yake. Sai kuma na kwaɓe fuska ina marairaicewa a hankali na furta, "to ai Yaya kace kar na kuma dawowa inda kake, idan ba haka ba zaka yi fushi dani". Idonsa naga ya ɗan rumtse ya buɗe ya zuba su akan hannuna dana riƙe nashi gam. Na lura so yake ya zare hannun nasa amma naƙi bashi damar hakan saboda riƙo na masa kamar wanda za'a ƙwace shi. "ya kamata ki tafi karki makara". Ya faɗa muryarsa a sanyaye. "tom shikenan yaushe zan kuma dawowa?". "a'a karki dawo don Allah, kinga ke macece mutuncin ki zai zube idan kina zuwa wurina, alhalin kuma mutane ga kallon da suke min". Na tari numfashinsa, "to ni ina ruwana, ai na san Yayana ba yanda suke tunani bane...". Ban kai ga ƙarasa faɗin Abinda zan faɗa ba naji yana kiciniyar cire hannunsa daga nawa, riƙewa na sake yi har ina ɗan cije leɓena, ganin naƙi sakar masa yasanya shi sunkuyo da kansa saitin fuskata, idonsa na kallon gefe guda yace, "ke ɗin ba muharramata bace, ni dake gaba ɗaya mun kai munzalin daya zama haramun wani ya taɓa wani, duk da ba lallai kina sanin lokacin da kike aikata hakan ba, amma riƙen hannu da kike saɓon Allah ne". Sai naji kunya ta rufeni, jikina kuma yay sanyi, zuciyata ta motsa, na kasa raba hannu na dana shi sai shine ya cire nasa. Ɗago idon da zanyi naga har ya tsallaka kwata, ido na zubawa bayansa ina jin kamar na fita na bishi, Allah ya sani ina tausayinsa kuma ina sonsa, irin son da nake ma Yaya Abba. gashi shi ɗin dai ba wani ba, ba kuma ɗan wani ba, amma yana da matuƙar burgewa, domin komai nasa me kyau ne, yanayin rayuwar daya tsinci kansa ne kawai ya maida shi wani kala, amma tabbas da ace shi ɗin a gidan gata ya fito, to lallai da anyi namijin gaske, nayi murmushi mai sanyi. na shiga duniyar tunanin ta ina zan iya taimaka masa, zuciyata na faɗa min taimakon da zan masa shine sada shi da ahalinsa, aina zan gansu? ta ina zan fara?, wani abu daya shigo ta cikin kaina ya wuce shi yasa na kulle ido tare da kwantar da kaina jikin kujera, Dai-dai lokacin kuma wata mata tai mani sallama na matsa ciki itama ta shigo ta zauna sannan napep ɗinmu yaci gaba da tafiya. A gadon ƙaya muka sauketa, daga nan kuma mai napep ɗin bai kuma ɗaukan kowa ba, ina jinsa yana ta mani surutu ni dai bance masa komai ba, kasancewata ba ma'abociyar magana da kowa ba, har muka isko ƙofar makarantarmu ya sauke ni, na bashi kuɗinsa ya tafi ni kuma na juya na shiga makaranta, Allah ya taimake ni kuwa ban makara ba. Ina shiga aji sai ga Farhana ta shigo, ashe taga lokacin da nake shigowa ta tagar ajinsu, kallo ɗaya na mata na ɗauke kaina akanta, nifa alallai fushi nake da ita tunda har ta ke aibata mun Yayana. Ta dafa kafaɗana tana ƙaramar dariya
🏠