NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 14 of 98

a macuci ba, kowa ya ganka yaga mutumin kirki, dan haka ka aje barazanarka a gefe". sai yace,"shi dama mugu yana da kama ne?". saina girgiza masa,"ko kusa, hasalima sai kake rayuwa da mugun mutum tare da kai ba tare daka sa ni ba...amma ko menene dai kai ba mugu bane". da ƙaramar murya naji ya kirayi sunana, "Sabina". na amsa, "na'am Yaya nah". "don Allah ki daina zuwa wurina, kar mutane suyi miki mummunar shaida irina, kinga ke ɗin halinki mai kyau ne". Na gyara zamana ina dubansa nace, "Yaya nah ni macece da bana mu'amala da wanda baya jin kunyar Allah, wanda yake saɓon Allah, amma yau gaka kai kuma ka tsaya min a rai, irin tsayawar da har na fara tsorata, ina tsananin tausayinka, hakan yasa na kasa barinka domin kai ɗin ina jinka ne tamkar jinina". Yace, "na gode da har kika iya fahimtata saɓanin mutane da yawa. Amma ni dai ina roƙonki da ki bar rayuwata". "Yaya bazan iya barinka ba a halin da kake ciki". Na faɗa ina zura hannuna cikin aljihunsa ba tare daya sani ba, sai a lokacin dana ɗauko kwalin sigari na nuna mishi ina cewa. "Yaya wannan hatsari ce ga rayuwarka. Kaji tsoron Allah ka daina shanta, Hakan da kake yi yana nuna cewar baka tsoron Allah ne, nasan cewar halin rayuwar daka tsinci kanka shi ya jefa ka cikin wannan halin, amma me yasa ba zaka amshi ƙaddarar da Allah ya jarabce ka da ita da hannu biyu ba? Bayan kasan cewar yarda da ƙaddara Mai kyau ko mara kyau suna cikin shika-shikan imani. Manzon Allah S.W.A yana cewa da ace zaka ciyar da kwatankwacin dutsen uhudu na zinare cikin ɗaukaka Addinin Allah, lallai ba zai karɓa daga gare ka ba har sai kayi imani da ƙaddara. Yaya nah don darajar Allah ina so daga yau kaji tsoron Allah ka daina saɓa mishi, ka nisanta kanka ga waccen abar mai cutarwa". sanda nai shiru na ɗago ina kallonsa, wanda idanunsa suka cika da ruwan hawaye a dai-dai lokacin kuma suka sami nasar zuba. Tausayinsa ya ƙara damƙar zuciyata, Allah kaɗai yasan wanne hali wannan bawa nasa ya shiga a rayuwa, a raina nayi adu'ar _Allah ka kawo mishi mafita._ Tunda ta fara magana ya kasa ɗauke idanunsa akanta, wani abu a ga me da ita na shiga zuciyarsa, tunaninsa ya katse sanda naci gaba da cewa,"Yaya nah zaka iya min alƙawarin daga yau ka daina shan sigari?". kamar wanda yake acikin tsoro da furgici sai yay saurin ɗaga min kai alamar ehhh. Murmushi na saki nace, "da gaske daga yau ba zaka kuma shan sigari ba?". amon muryarsa ya fito da faɗin, "Nayi miki alƙawari, Allah ya bani ikon cikawa". na lumshe ido na buɗe, har ga Allah sautin muryarsa na min daɗi shi yasa wani lokacin nake jan maganar da zai tilasta shi yay magana. ina dubansa da washewar murya nace,"Yaya idan har ka daina shan sigari zanji daɗi, amma fa ka sani duk ranar da na kuma ganin kana sha ina mai tabbatar maka da nima zanyi koyi da kai, dan sai na sha taba sigari naji wanne ɗanɗano kake ji a cikinta". abunda bai taɓa yi ba, yay Miskilin murmushi mai ɗan sauti wanda hakan yasa na buɗe ido ina dubansa, na ɗaga masa gira da faɗin,"murmushin na mene? kana tunanin ba zan iya ba?, ko kuma ce min da kai ba zaka ƙara ba yaudarata ne kayi?" "duk ba haka bane, ina so na koyi irin yanda fuskarki ta ke ne kullum cikin murmushi shiyasa na gwada, kuma sai naji ya haɗe da ciwon dake maƙale a zuciyata kenan yafi ƙarfina. yanzu dai Sabina tashi ki tafi gida". laɓɓana na motsawa na saka hannuna duka biyu a kumatunsa na talasu ina cewa,"indai ka saka a ranka cewar Allah zai maka magani to kullum wannan fuskar zata kasance a haka. ai ba abu ne mai wahala ba". yana ɗauke hannuna yace,"ni dai nace ki tashi ki wuce gida". "Kai Yaya daga zuwa na kuma sai ka kore ni, ni ai bamu gama hira da kai ba, kaga shi Yaya Abba baya bani lokacinsa kullum.yana wurin ball". yace, "aini ban iya hira ba, kuma kinga ke macece ya kamata ace kina cikin gida idan ba makaranta za kije ba. Gaki nan ma da alama makaranta za ki tafi". "a'a na dawo daga tahfeez ne yanzu sai dai ta ƙarfe huɗu". "to ki tashi ki tafi lokaci ya kusa". na miƙe ina gyara zaman jakata nace, "tom Yaya sai wataran?". Gani nayi shima ya miƙe yana zura hannu cikin aljihu, ya kalleni kaɗan yace, "ki ɗaura niƙab ɗinki mana". ina yamutsa fuska ina karayar da kai nace, "Yaya zafi akeyi ne yanzun, ɗazu ba zafi shi yasa na saka". "ki ɗaura don Allah, saboda kan hanya akwai mutane, idan kika je gida sai ki cire". ina marairace fuska nace,"Yaya Allah...". bai bari na ƙarasa maganata ba ya katseni da tashi,"ni dai don Allah". "tom shikenan na ɗaura". na faɗa a sanda na gama ɗaura niƙab ɗin, sannan nace da shi. "na tafi sai wataran". "muje na raka ki". ina kallonsa ta cikin niƙab ɗin zanyi magana ya tari numfashi da cewa,"bana son mutum me musu". Hakan yasa na fasa maganar da zanyi, nan muka jera tare muna tafiya. yau kam ya sake dani sosai, dan harda ce min wai na cika magana, nace masa ai kaima kana da surutun gashi nan tunda muka taho kana magana. sai ya tala laɓɓansa da cewa,"wannan ne karo na farko a rayuwata". "me yasa?". "saboda banda wanda z
🏠