NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 98

ba ta duƙa tana gaida Gwaggo. Gwaggo tace da ita, "ya haƙuri da halin ƙawarki duk da nasan kina yi. amma yanzu lamarinta ƙara ta'azzara yake sai an kai zuciya nesa zama da ita...kin ganta nan tun jiya rabonta da min magana, gaisuwarma yau ko samu banyi ba, ni kuwa tunda Ubanta dai yazo ya gaisheni tata ba abar damuwa bace". Farhana tayi murmushi Kawai ta miƙe a tsugune tana dubana tace, "mu tafi ko". na ɗan harare ta gami da murguɗa mata baki kana nace, "ni ai bance ki biyo min ba. Kiyi tafiyanki kawai". Gwaggo ta rarumi mafici zata ƙwalo min nai saurin miƙewa na fice. "ƴar ƙwal uba da ki zauna mana. Farhana indai tayi wani shirmen ki faɗa min dai-dai nke da ita". Farhana na dariya ta amsa da, "to". tunda muka shiga mota babu wanda ya kula ɗan'uwansa, sai da muka kusa zuwa makaranta ta kama ce min. "wai ke don Allah mene na damuwa da wannan mahaukacin, ɗan daba kawai, ɗan iska wanda bakin uwa yay tasiri akansa, haka kawai yazo zai sanya min ƙawa a damuwa, ni Allah da ace nasan haka zata faru da bamu je amso ɗinkin ba a ranar". na juyo na harareta ace, "ni ina mamakin rashin imaninki Farhana. Duk wanda yaga wannan bawan Allah'n sai yaji tausayinsa, amma ke na rasa dalilin bushewar zuciyarki akansa. kuma kina ta bada shaidar zirrr akansa kina ganin kaman burgewa kike, to tunda Allah yasa islamiya za kije kya tambayi Malami makomar irinku". "irinmu? makomarmu ta me?". "kice Malam Ali mene makomar masu shaidar zirr zai baki amsa". "Sabina zirr fa shaidar ƙarya kenan". "to me kike yi banda ita?". sai tai guntun murmushi tana cewa, "To ni dai tausayinsa ne ba zanji ba, kuma abunda na gani da shi zanyi shaida, mutumin da baya jin tausayin kansa kan me kuma kai zaka tausaya masa. Ai sarai yasan shaye-shayen da yake cutarwa ne a gare shi amma yake yi. Shege ɗan iskan banza kawai". ban san lokacin dana kai hannu na daki stearing motar ba har ina ƙoƙarin ƙwace shi daga hannunta, tai ƙarfin riƙewa da kyau tana tureni. na ɗaga murya cikin masifa nake ce mata, "Farhana na faɗa miki babu kyau aibata musulmi ko da ya kasance yana aikata mummunan halaye bai kamata aibata shi ba. Farhana na roƙe ki karki ƙara furta mummunar kalma akan Yaya, idan ba za ki iya masa adu'ar shiriya ba don Allah kiyi shiru da bakinki akansa...karki ga ina roƙonki, na rantse miki gaba ba zata mana daɗi dake ba". na ƙara maganar ina jan ƙwafa. ita dai ta min shiru bata ce komai ba, domin ta lura akan wannan banzan mutumin zamu iya ɓaɓewa ta har abada. kuma har muka isa makaranta ban bar surfa mata masifa da bala'i ba. kuma ci kanki bata ce min ba sai ma earpice data maƙala a kunne naci gaba da haushina ni ɗaya, aiko sai dana tsinka shi. Ƙarfe 2 aka tashemu a makaranta, maimakon nai gida saina tari napep nace ya kaina sharaɗa, ban ko bari mun haɗu da Farhana ba dan Malam na fita na fito kasancewar bamu zauna sit guda da ita ba. Dai-dai kan layi nace mai nepep ɗin ya saukeni, na ciro kuɗinsa a jaka na bashi, ina yankowa wajen bolar kuwa na hange shi a bakin wani tanki ya kunna famfo ya duƙa yana shan ruwa, yauma dai jikinsa fes yana sanye da yadin dana ganshi tun a ranar farko, da alama dai siturarsa ɗaya ce, sai Allah masanin lokacin da yake cirewa ya wanke su. yana gama shan ruwan kuma ya koma can inda ya ke zama ya zauna, da zamansa ya zaro taba sigari cikin aljihu ya kunna ya fara zuƙa. haka kawai sai naji zuciyata tayi matsewar da bata taɓa yi ba, sam-sam bana ƙaunar ganinsa da wannan sigarin ban san me yasa ba, sai naji ƙafafuna na saurin tafiyar da zance basu taɓa yi ba har na ƙarasa gare shi. kansa na duƙe kamar yanda ya saba idan zai sha, ina isa na zare sigarin daga hannunsa a hankali na jefar, fuskana a haɗe. abunda ban sani ba tun ɗazu ya hangeni sai dai baiyi tunanin ni bace kasancewar niƙab ne lulluɓe a fuskata, sai yanzu dana zo na ƙwace masa sigari ya gane ni ɗince shi yasa ya kawar da kansa. yanzu na riga na saba da wajen da yake rayuwarsa, bana jin ƙyanƙyami ko kaɗan, warin sigarin ma yanzu na saba da shi, na naɗe hijab ɗina na durƙusa a gabansa dai-dai saitin inda fuskarsa take. sai ya sake ɗauke kansa ya maida ɗayan gefen, nai murmushi na ɗaga niƙab ɗina ina sunkuyar da kai na leƙa fukarsa nace, "Yaya ni ce fa, fushin na menene? ƙanwarka ce fa Sabina ka juyo ka kalleni". bakinsa ya motsa a hankali kamar ba maganar zaiyi ba yace,"na san kece ai". sai na ɗan shagwaɓe murya ina faɗin,"to amma shine kake ɗauke kai daga gare ni". Yace,"bana kula mara jin magana ne". "Yaya rashin jin maganan me nayi kuma?". na faɗa ina ɗan marairaicewa. ya ɗago ya duben sau ɗaya wanda ya sanya shi jin faɗuwar gaba yace, "bana hanaki zuwa wurina ba, kina so na yi miki fyaɗe ko?". Da mamakin dake haskawa cikin ƙwayar idonsa na rashin tsorota da irin wannan furucina yasa ya tsareni da ido. sai nai siririyar dariyar data bayyanar da fafaren haƙorana kamin nan nace. "Yaya ba zaka fasa tsorata ni da wannan kalman na fyaɗe ba, haka ba zan fasa faɗa maka kai ɗin baka yi kama d
🏠