ya amasa min yace,"Yau ba makaranta ne?". nace, "a'a da akwai, ai da sauran lokaci. Amma yanzu ma zan shirya da mun gama cin abinci". "to madallah. Ana dai dagewa ko?". "ehhh Baba muna yi sosai". Fuskar Baban ta washe da fara'a yace, "Allah ya bada nasara, ya kuma yi muku albarka...ai ba'a bina kuɗin makaranta ko?". Ya faɗa a yayinda yake zuba ruwa a cup zai sha. "amin amin Baba na gode. ehh ba'a binka". na miƙe naje na ɗauko namu abincin ni da Gwaggo, ina cin abincin ina satar kallon mahaifina da nake jinsa mafi soyuwa a gareni. kusan tare muka cinye abincin da shi, saboda muna ci ana hira, nan da nan muka tashi kan shinkafa da waken daya ji haɗin kayan lambu. na tashi na haɗa kan kwanukan da muka ɓata na kai kitchen, na dawo na gyara wurin duk da ba wani ɓata shi muka yi ba, sannan na wuce zuwa ɗakinmu da muke kwana ni da Gwaggo.
nai wanka na shirya cikin uniform ɗina na islamiya milk colour, kayan sun mun kyau sosai, jakar littafaina na ɗauka na rataya kana na fito nace da Gwaggo da Baba zan tafi. a gaban Baba na duƙa ina cewa da shi, "Baba kayi mani adu'a". Ya dubeni cike da soyayyar uba ga ƴarsa sannan ya ɗora hannunsa saman kaina yace, "Sabina Adu'a ta zama dole, kije Allah yay maki albarka, ya baki masara a rayuwarki. Allah ya kaiki lafiya ya dawo dake lapia ya kareku a duk inda kuke". ina murmushi nake amsa mishi da,"amin Baba nah na gode sosai, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana". Gwaggo ma tayo tata adu'a sannan na fita, Har naje soro sai kuma na dawo, saboda tunawa da nai akwai inda nake son zuwa kuma banda kuɗin mota, satina guda kenan rabon dana fita waje, dama inda makarantar boko ne nake ɗan samun canji a hannuna, to anyi hutu, itama kuma islamiyar sai yaune muke komawa. to yanda na ƙwallafa rai da zuwa inda nake so naje yau ai yacce Baba ya shigo dole na nemi kuɗi. ganin na dawo Baba ya shiga tambayana me ya dawo dani, ni kuma kai tsaye nai masa ƙaryar zan siya littafi ne na manta ban karɓi kuɗin ba. na faɗa masa ina tsoron kar yace babu kuɗin a hannunsa amma naje zai shigo makarantar anjima yaywa Malam Saminu magana su bada bashi kaman yanda aka saba. Allah ya taimakeni sai naji kawai yana tambayana nawa ne kuɗin, da yake ban saba da ƙarya irin haka ba sai na rasa nawa zance, na tsaya ina kame-kamen kamar 200 kamar 150, sai kawai ya zaro 500 ya bani yace na riƙe canjin idan yayi saura, na kuwa amsa murna fal raina inata zabga masa adu'a. shima kuma ya shiga yi min adu'ar Allah ya jiƙan mahaifiyata ya haɗani da miji na gari.
ko da naje islamiya bayan an gama yi mana ƙarin karatun ƙur'ani mu ƴan manyan aji, sai aka kiramu aka rarraba mu zuwa sauran ajujuwa domin kula da yara sakamakon Malamai zasu shiga meeting. Sai biyar da rabi kana Malamai suka gama meeting, kuma a ciki ne har aka tattauna akan cewar za'a ɗauke ni gasar musabaƙar qur'ani ta ƙasa domin na wakilci makaranta kasancewata gwarzuwa. A lokacin da Malamai suka dawo daga meeting muka koma zuwa ajinmu, ina zaune Malam Hussain ya kira ni, nan ya sanar min abinda hukumar makaranta ta tattauna akaina na ga me da zuwa musabaqa, saboda haka saina sanar da iyayena idan zasu bani damar zuwa, kuma duk da hakan suna da buƙatar ganin mahaifina ko kuma wani babba a gidanmu. ina ta murna da farinciki na miƙe daɗi duk ya isheni, dan ni kaina ina alfahari da baiwar ilimin da Allah ya ban. Ƙarfe shida aka tashemu, a bakin gate ɗin makaranta na sami Farhana tsaye tana jirana, ƙirjina rungume da qur'ani na ƙaraso inda take, nan muka jera muka fara tafiya. shiru shiru babu wanda yay magana acikinmu tsawon tafiyar da mukai, kamar bamu ɗin nan da bama rabo da abin faɗa ba idan muka haɗu, hasalima idan aka tashi muka taho bamu da aikinyi sai gulmar Malam wane da wane. can dai Farhana da bata iya haƙura da yin shiru ta nisa cikin ƴar murya tace,"Ƙawata wai lafiya naga kwana biyu kina sha re ni, laifin me nayi miki ban sani ba ƙawalli?". ta faɗa tana dafa kafaɗa ni kuma ina zamewa, fuskar nan tawa na ƙara cukuleta dan sarai na san ta san dalilin ɗauke mata wutar da nai, amma saboda rainin wayo da neman magana take tambayana. dan haka nima saina raina mata nawa wayon da cewa, "ba komai, me kika kalla dama?". nayi mata tambayar kaina na gaba ina tafiya cikin sauri-sauri. ta ƙara cewa,"aikam dai da wani abu, domin ba haka muke da ke ba, amma a ƴan kwanakin nan duk kin wani sauya min". kaman zance mata a'a ko nayi mata shiru, sai na tuna da maganar malaminmu da yake cewa mutumin daya fi kowa shine wanda idan mutum yay masa ba zai ƙullace shi ba, zai samesa ya faɗa masa wane kayi min abu kaza da banji daɗinsa dan Allah karka sake, amma duk wanda zai ƙullaci mutum akan yay masa laifi ya riƙe abin a ransa yaƙi faɗa maka, ko kun haɗu a zuciyarsa zai gaisa da kaine ta dole yay maka yaƙe to wannan mugun mutum ne, ni kuwa bana so na kasance cikin mugwayen mutane. dan haka na ɗan waigo nai mata kallo ɗaya sannan na ɗauke kaina nace,"Farhana ba magana ta wasa ba, da gaske nake faɗa miki bana