NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 98

nka, hasali ma sai ƙaunarka da nake yi. tun jiya dana ganka zuciyata ke faɗa min ko me zaka yi min kar na rabu da kai, tana faɗa min akwai wani abu da zai kasance a tsakaninmu, tana faɗa min kai mutumin kirki ne, tana faɗa min an halicceni ne domin na tambayeka...so ka bar tsorata ni, ni bana tsoron kowa da komai saboda ina tare da Allah. yanzu dai ga abinci nan kaci mu tafi gida”. Kanshi ya kai duba ga plask ɗin da nake turawa gabansa. “Bana ci, ki ɗauka ki tafi, idan baki so nayi maki fyaɗe”. "banda lokacin ɓatawa". abunda nace da shi kenan ina buɗe jaka na ɗakko pure water, na miƙe na isa har gaban shi tukunna na kama hannunshi na wanke mishi, shi ko sai bina yake da ido yana ganin ikon Allah, sai dana wanke masa duka biyun sannan na buɗe plask ɗin na saka mishi a gabansa, na ɗakko kofi na zuba tea shima ta ajiye a gabansa ina faɗin, “Oya Yaya kaci mu tafi gida”. shi dai yayi shiru na zame masa abar kallo, zuciyarsa na cika da al'ajabina. ni kuwa ganin baida niyyan ci yasa na ɗauki tea cup ɗin na nufi bakinsa ina faɗin,"haaa". sai kawai ya koma kamar ɗa me biyayya ga uwarsa, babu musu ya buɗe baki ba tare da yasan ya buɗe ba, na saka mashi dankali da ƙwan ya taune ya haɗiye sannan na bashi tea ya kora. haka na dinƙa feeding nasa yana ci, ci sosai, kuma duk wannan bashi ɗin da nake ina jin yanda idonsa yake akaina, ni kam cin abincin da yake sai naji kamar ina tare da wata matsala me a rayuwata amma ta akan hakan ta yaye. har saida ya cinye irish ɗin nan tass baima sa ni ba, sai ji yay ina goge masa baki ina faɗin,"yauwa Yaya Nah ko kaifa...yanzun idan ka huta sai mu tafi gida ko?”. Tsaye ya miƙe da yanayi na fusata yace,"ba zan iya zama da mutum mara yadda ba, Sabina fice anan, ki fice anan wurin kamin nayi miki abinda har ki mutu ba zaki bar kuka ba. Kuma daga yau kar na ƙara ganinki anan na faɗa miki wannan". Ya faɗa a tsawace yana nuna min hanyar fita. Kallonsa na tsaya yi a lokacin da idanuna suka kawo ruwa, sannan na duƙa ƙasa na kwashi kwanukan abincin, zuciyata sam-sam ba daɗi, na fita na bar kangon ina mai waigen shi, maganganunsa na min yawo acikin kaina. Sai bayan fitowana tukunna ruwan hawayen da suka gama cika idona suka sami damar zuba, na sanya gefen hijabina na goge, sannan na saita kaina naci gaba da tafiya. shi kuwa tana fita ya sauke dogon numfashi, idonsa a rufe ya nemi wuri ya zauna yana mai jin ransa da zuciyarsa duk babu daɗi. to amma ya zaiyi, ita macece, yanzu idan tana zuwa wurinsa sai ta ɓaci a idon mutane, a dinƙa yi mata irin wannan kallon da akeyi masa, kuma ya tabbata iyayenta suka san da hakan zasu iya saɓa mata, kuma kamar yanda ta faɗa ne, shi ba macuci bane dan haka ba zai taɓa iya cutar da ita ba. hasalima abu guda ɗaya ne yake nan, Allah ya sani, yana so ya dinƙa kasancewa da yarinyar ko da ba koda yaushe ba ne...bai yi tunanin zata kuma dawowa wajensa ba, amma ya tashi da tunaninta a yau. sai ya rumtse ido ya shafo sumar kansa yana fesar da iskar baki, wanda hakan ke ɗabi'arsa ce, kamin nan ya nemi waje ya zauna yana bin wurin da ta zauna da kallo, inda hoton zamanta a wurin ke haska masa cikin ido, maganganunta masu taushi kuma na yawo cikin kansa. #Vote. #Comment. #Mikiyawriters.*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(4)* hidimar aikace-aikace nake tayi tun wayewar gari, yau babu inda ban gyara ba acikin gidan nan lungu da saƙo, hakan yasa ɗan ƙaramin gidan namu ya sake yin fayau da shi yay ƙal-ƙal, haka nake sam bani da ƙiwar aiki, Gwaggo na yawan faɗa min Mamana na gada, amma duk wata bauta da nake yi a gidan nan Yaya Abba baya ganinta dai-dai da misƙala zarratan. wuyarta nayi wuyarta ya ɓata kuma ya kushe, wani binma idan ya ɓata yay ficewarsa nai zuciya nace ba zan gyara ba, to bala'i ko sai dai idan bai dawo gidan ba, amma sai ya sauke min shi, ya dinga cewa Gwaggo wai tana sangartani, zan lalace na zama ƙazama. Gwaggo tace masa to ubanwa ke faɗawa idan na gyara, ta hakanne kawai nake samun salama, amma ni kaina na san banda ciki guda muka fito da shi la shakka ba zan ke raga masa ba, ina da haƙuri dai-dai gwargwado amma ba kanwar lasa bace. kiran sallar azahar ɗin dana jiyo yasa na shiga sauri-sauri na kammala aikin kamin lokacin tafiya islamiya yayi, dan lokaci babu wuya yanzu agogo ya buga ƙarfe uku, dama da safe naji Gwaggo na cewa da Yaya Abba ya saka mata sabon batiri a agogonta, agogon me shegiyar ƙara da zarar cikar daidai yayi zai kama kiɗinsa me hawar min kai. Gwaggo ta fito zata shiga banɗaki tace da ni, "Sabina sannu da aiki". na amsa, "yauwa Gwaggo, kin fito alwalar ne, bari na zuba miki ruwan". Ɗaya daga cikin botikan dake nan tsakar gida na buɗe na zuba ruwa cikin buta kana na bawa Gwaggo. Alwala Gwaggo tayi ta koma ɗaki domin ta gabatar da sallar azahar. Idarwarta kenan sai ga sallaman Baba, ɗakin ya shigo inda ya zauna nan bisa kujera yana gaida ita. na shigo a lokacin na durƙusa na gaida shi tare da ajiye masa ruwa da abincin dana kawo mishi. bayan
🏠