NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 95 of 97

, Daadee ya zame Maamee daga jikinsa yana yiwa mahaifiyarsa barka da isowa. Marfu'a kuma ta wuce da ƙaton basket na abinci taje suka gaisa da su Ummani kana ta dawo ta zauna kan kujerar da Samra ta tashi tana karɓar yaronta a hanun Nani. "Saukar yaushe?". Madam ta ce da Dadee suna tafe zuwa wurin su Ummani ita da shi. "Yanzun haka, don ina shigowa kuna zuwa". Daadee ya ce da ita daidai da ƙarasowar tasu wajen dangin Sa'ida waɗanda suka kame kansu a gefe guda suna jiran tsammanin rai ko mutuwa na ƴarsu. Madam ta miƙa hannu ga Ummani tana cewa,"Bayin Allah sannunku, ya muka ji da wannan tashin hankali?". Daadee shima ya miƙa hannu ga Abbaa da Kaka suka gaisa. Kafin nan ya shiga basu haƙurin hatsarin da ya afku yana kwantar musu da hankali akan da yardar Allah ƴarsu zata sami lafiya. Suka amsa da amin tare da godiya bisa karamcin tsayawa da aka yi akan ƴar tasu wannan kaɗai ma basu da bakin godiya sai dai su ce Allah saka da alkhairi, hatsari kuma ai afkuwa yake ba da gangan ba saboda haka babu buƙatar ake basu haƙuri ai an masu mutunci ma da aka ɗauke musu ɗawainiyar asibitin. Daadee ya kai ƙwayar idonsa ga hanyar shigowa wanda yay daidai da shigowar SJ kuma take annurin fuskar Daadee ya ɗauke, yay saurin ɗauke idonsa daga wajensa yana kawarwa gefe fuskarsa na nuna ɓacin rai, shima ɓangaren SJ ganin mahaifin nasa a wajen yasa shi dakatawa da tafiyarsa ya tsaya daga can nesa, haka kuma yanayinsa na sauyawa zuwa wani yanayi me wuyar fassaruwa, tabbas in ace ya san mahaifin nasa ya dawo to bai ga abin da zai kawo shi wajen nan ba, kamar yanda a ɓangaren mahaifinsa shima cikin zuciyarsa ke faɗin in da ya san SJ zai zo asibitin da babu abin da zai kawo shi a lokacin da zai zo. Ahlan yaywa Maamee nuni da SJ, ta kai kallonta wurin suka haɗa ido da shi yana tsaye hannayensa sarƙe a ƙirji sai kallonta ya ke babu ƙiftawa, fuskarsa na nuni da rashin jin daɗin ganin Daadee da yay a wajen. Ta tashi ta ƙarasa gare shi don ta san ba zai ƙaraso ba kam, tayi mamakinsa ma da bai koma ba kamar yanda tayi mamakin Daadee shima bai fice a fusace ba, ita a duniyarta kam bata da wata damuwa bacin ta SJ da Daadee da basa jituwa ko na misƙala zarra kamar ba Uba da Ɗa ba. Da isarta wajensa ya kama hannunta ya riƙe a nasa, tana kallonsa ta ce,"Me yasa ka baro aikinka?". Ta faɗa cikin harshen faransanci. Yay shiru na ƴan sakanni kana shima cikin harshen na su ya ce da ita,"Maamee karon farko da naji sautin kukanki, kinga har yau zuciyata motsawa take da zafin kukan da naji kina yi". Yay shiru yana rufe idanuwansa yana shafa hannun mahaifiyarsa da ke cikin nasa, bayan numfasawar minti guda ya ce,"Yarinyar fa?". Kasa ba shi amsa tayi, ya buɗe ido tare da sanya hannu ya ɗago fuskarta ya ce,"Da ace kuɗi na siyan lafiya da ba'a kawo wannan lokacin ba, sai dai lafiya na wurin ubangiji bamu da yanda zamu yi, shi likita nasa taimakawa ne kawai. Don Allah Maamee ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki zata sami lafiya fa, Yanzu haka da na shigo sai da na fara zuwa wurin Dr yay min bayani kuma ya bani tabbacin zata farka lafiya lau wasu mintuna kawai ake jira, na dai jaddada masa suyi iyakacin iyawarsu wajen ganin Yarinyar tayi surviving and ba tare da zaman wani mummunan rauni a tare da ita ba". Ya ƙarasa maganar yana sauke numfarfashi tamkar wanda yay tsaren gudu tsabagen doguwar magana nayi masa wahala. "Amma Bhai kana gani sama da 24hrs fa bata farka ba, kar ya zama na yi sanadin rai". "Maameeeee". Jin yanda ya ja sunan nata yasa tace,"To nayi shiru Allah ya tashi kafaɗunta". Hannunsa bisa fuskarta ya ce,"Marci". "Ga mahaifanta can da ƴan uwanta muje ku gaisa ka tayani ba su haƙuri". "Ok let's go". Yana riƙe da hannun mahaifiyar tasa suka nufa wurin. da zuwansu SJ ya duƙa har ƙasa ya gaida su da girmamawa tare da tambayar,"Ya mai jikin?". Sautin muryarsa ya fito da rashin ƙwarewar hausa a bakinsa. Abbaa ya dinƙa kallonsa lokaci ɗaya sai yaji ya shiga ransa, saurayi mai kamala da natsuwa gami da girman kwarjini. Ya ce da shi,"To sauƙi yana wurin lillahi, tana can kwance dai har yanzu bata farka ba amma likitan ya ce wai zata farka duk da mun barwa Allah yay ikonsa". Kan SJ sunkuye a ƙasa, cikin tausashshiyar murya ta son kwantarwa da mutun hankali ya ce,"Zata farka kuma cikin sauƙi in sha Allahu, likitoci za su yi iyakar bakin ƙoƙarinsu akan lafiyarta babu wani damuwa ku kwantar da hankalinku". "To mun gode Allah ya saka da alkhairi". Ummani ta faɗa tana kallonsa. Ya miƙe yana yi musu sallama. Ummani ta kasa ɗauke idonta daga kansa, kallonsa kawai take yi tana so ta tattara yanayin da take ji akansa ta ɗora a ma'aunin lissafinta kana ta fassara shi, zuciyarta ta harba ɗaya, biyu, uku, tare da kalmar GARKUWA. Duk da halin jimamin da ake ciki hakan bai hana ahalin Sa'ida furta yabo da burgewa ba akan SJ da ahalinsa. "Ak
🏠