NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 94 of 97

nyar can a gadon asibiti, yanzu idan ita Dr ɗin ce ai tuni ta kwan ta yini a gidanki wallahi, haba ake duba da hankali da tunani mana, wannan rashin lissafi ne sam". Da gama faɗin haka ta kashe wayar tana tsaki fuskarta na nuni da ɓacin rai. "Ni ban san zunubin da na aika har ma na haifi wannan yarinyar ba itama ta haifi wancan gantalallan yaron nata, duk ba su da lissafi. Ke kuma wuce muje ko sai an ƙwala Assalatu tukunna za ki tuna da Asibiti muka nufa". Marfu'a ta kalleta tana kumbura fuska tace,"To motar zan ɗauko na kawo nan ki shiga ne?". Harara ta ɓalla mata bata ce da ita komai ba, kuma kafin ta ɗaga ƙafa sai ga SJ ya wuce ta gabansu cikin sassarfa. Ta waro ido ta cikin gilashinta tana dubansa da cewa Marfu'a,"Kamar SJ ko?". "Ba kama ba ne shine ɓarawon da kika so kurmawa ihu ɗazu". "Allahu akbar yaushe ya dawo ƙasar? Ki ce Allah ya rufa asiri da yanzu shima an kwashe shi sumamme, gwara da Allah yasa kika ƙaryata ganina kika ce sharrin aljanu ne. Da yau Uwassa tsab ta baro wancan tashin hankali ta dawo kaina tana zunduma ihu. To maza tsayar da shi mu wuce tare don na san shima asibitin ya nufa". "B ɗin za ki bi Madam? To ai kina da lambarsa kira shi, ni kam kinga tafiyata". Murya ta kalar masu tausayi ta ce,"Shi ai yana iya yarda mu tafi indai zan masa shiru ba zan cika shi da magana ba. Kawai dai Na-Madam ne yafi shi daɗin tafiya ana tafe ana hira ana raha, to shi matsalarsa a wargaje yake mutunci bai ishe shi ba. Amma dai da zamu bi SJ ɗin da yafi ana ta yiwa Amb ɓarnar man mota". "Sai kuma ki yi ai, ni na tafi". Marfu'a tayi gaba abinta tana barin Madam a baya wacca ke gyara zaman lafayar jikinta. Tsohuwa ce sosai amma ji take da gayu tamkar ƴan mata, ga lafiyayyan jiki ma sha Allah irin ɗan ciwon ƙafar nan na tsaffi ma ita ba ta da shi, ba ranƙwafawa babu tamushewar fatar jiki da yawa, haƙoranta ras lafiyayyu ko irin cutukan nan da zaka samu tsofaffi ita ba ta yi, Allah ya bata kam, don gayu take ci abin ta har da su hoda da jambaki kamar tsofaffin amuruka. Cikin tafiyarta da ke yanayi da ta SJ ta taka zuwa motar Marfu'a, da shigarta ciki wayarta tayi ƙara, ta amshi jakarta hannun Marfu'a tana ciro wayarta ƙirar iphone 7 kai baka ce wayar tsohuwa ba, ganin sunan mijinta na yawo akan screen tayi murmushi kana ta ɗaga tana sallama cikin yarensu na faransanci. "Bonjour Mon chéri, celui qui fait batre mon coeur j’espère que tu te porte bien". _(Assalamu Alaikum. Fatan mijina abin alfaharina yana cikin ƙoshin lafiya. )_ "Sava très bien celle qui me rend heureuse, je tais appeler sa ne passe pas .comment va la santé de l’enfant a l’hôpital?". _(Lafiya lau farin cikina, nayi ta kiranki ba na samu. Ya wajen yarinyar asibiti?)_ "C’est aujordhui qu’on va allez la voir on dit que sa ne va pas sa santé". "Quallah lui accorde la santé .mon marie t’aime tous les jours". "Moi aussi j’aime mon marie ,Quallah nous facilite le coeur .merci?". *PSC Specialist Hospital Limited, Lamiɗo Cresent.* Ƙafafun Ambassador Jadda su ka ƙaraso ƙofar room ɗin da aka rubuta V.I.P 05 da bayyanuwar tashin hankali a tare da shi. Wanda saukarsa ƙasar kenan daga ƙasar Italy. Maamee na daga can gefe kan kujera, hango shi ta taso ta taho gare shi da sauri kamar yanda shima ya tafi gareta da sauri. "Daadee". ta faɗa da ɗan ƙarfi tana faɗawa jikinsa, ya kewaye matar tasa da dukkan hannayensa biyu cikin tsantsar so da kulawa yana faɗin,"Sorry Mon Cheri, calm down, calm down everything will be ok by God Grace". Bata iya cewa da shi komai ba sai sabon kuka da ta saki shi kuma yana ƙara rungumeta ya shiga shafa gadon bayanta ba tare da sunyi la'akari da mutanen da ke wajen ba. Cikin kuka sosai take cewa da shi,"I am so scared Daadee". "Don worry relax and calmdown, i am here now, everthing will be oak, you stop crying please". Ya ɗago kai ya kalli Samra yace da ita,"Iyayen yarinyar fa an samesu?". Ta ɗaga masa kai,"Yes Daadee". ta faɗa tana yi masa nuni da kan wasu chairs inda iyayen Sa'ida su ke a zaune, tare da su kuma ƴan uwa ne kusan mutum goma a tsaye kowanne cikin jimami. sai yabi wajen da kallo yana ƙare musu kallo me tarin ma'anoni da yawa. Ya tattara hankalinsa da tunaninsa wajensu gaba ɗaya, sunyi tagumi kowannen su fuskarsa bayyane da bala'in tashin hankali da tsantsar damuwa, yanda yay nisa a kallonsu zai tabbatar maka da ya tafi cikin dogon nazari, kuma daga yanda yake faman yamutsa fuska sai kayi zaton ko ƙyanƙyamin kallon na su yake. Samra da ke kallon mahaifin nasu ta fakaici idonsa a hankali kuma cikin dabara ta zura hannu cikin aljihun rigarsa ta zare kwalin sigaret ɗin da ke ciki. Da sauri ta bar wajen da nufin zuwa ta jefar, idan da abunda suka tsana a duniyarsu bai wuci shan sigari da mahaifinsu ya mayar tamkar abinci ba. Barinta wajen ƙarasowar Madam da Marfu'a
🏠