NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 93 of 97

rki da dukkan yabo su tabbata ga Alhakimu, Alkaliqu, mabuwayin sarki mai azurtawa, ubangiji mai girma da ɗaukaka, mahaliccin da ya halicci wannan bawa nasa. lokacin da yake cikin motar ba zaka san da cewar asalin kyau ne da kansa ke zaune ba sai a yanzu da ya fito ya tsaya a tsaye, ƙwarai ubangiji ya zuba tsarin sura a jikin wannan halittar, kyakykyawan saurayi ne na gaban ai kwatance, ba fari ba ne tas amma hasken fatarsa na da ɗaukar hankali, hancinsa har baka, ga yankan madaidaicin baki da tausasan laɓɓa pink colour, idanuwansa madaidaita irin oil eyes farare tass da su babu datti ko kaɗan a cikinsu sai ƙyallin maiƙo da ruwa ruwa haka, kuma maimakon black eye lens irin na mutane nasa sai ya kasance aque blue mai burgewa, ga wani kwantaccen saje da ya shimfiɗu a fuskarsa tamkar an zana masa, ƙananun kaya ne a jikinsa, black jeans da black T-shirt mai ƙaramin hannu, a gaban rigar da bayanta an rubuta *S.JADDA* da manyan baƙi, haka ma a p-cap ɗin da ke kansa ita ma kalar baƙa, sosai shigar kayan su ka ƙara fidda ainihin kyan surarsa, halittar da idan kayi mata kallo na farko ba zaka so idanuwanka su ƙara ƙiftawa akanta ba, haka kuma gabanka sai ya yanke ya faɗi saboda girma na kwarjini, cikar haiba da zati da cikar kamala da natsuwa da yake da ita, ƙamshin da ke fita daga jikinsa kaɗai ya isa ya shaida maka shi ɗin na musamman ne, kuma da gani ɗan masu ƙumbar susa ne a ƙasar Najeriya, irin su ne dukiya an tara an ajiye musu kuma ana kan ganiyar ajiyewar, ko basu nemi na kansu ba ba zasu taɓa sanin wani abu wai shi Babu ba, ba ga su kaɗai ba hatta ga jikokin da za su haifa. Tun fitowansa a motar yana tsaye ne jingine da jikin motar ya harɗe ƙafafunsa yana fuskantar entrance ɗin da zai shigar da kai cikin gidan gaba ɗaya, ƙwayar idonsa ta cikin baƙin glass da ya kewaye idanuwansa tayi ƙyam tamkar ba zata ƙifta ba. idonsa ba akan agogo yake ba, amma kuma da bugun zuciyarsa yake lissafin adadin mintuna goma sha biyar ɗin da suka rage masa ya shiga ciki ya shirya sannan ya fito ya nufa wurin mahaifiyarsa. A hankali ya kai kyawawan hannayensa masu cike da gargasa ya cire hular p-cap da ke saman kwantacciyar sumarsa wadda ta cika ta sha gyara sai ƙyalli take yi, ga ta a nannaɗe gwanin burgewa da sha'awar taɓawa, kana ganinta ka san sumar buzayen asali ce ta ƴan ƙasar Gabon mai ɗaukar ido. fatabarakallu ahsanal kaliqin, ai asalin bayyanuwar kyansa sai yanzu da ya cire p-cap ɗin, kamilalliyar fuskarsa ta fito gaba ɗaya ta bayyana tarr, sumar kansa har gaban goshi kamar wanda yasa gashin indiyawa, fuskarsa kuwa da ka kalla zaka shaida shi ɗin mutum ne mara hayaniya da kuma rashin son hayaniyar haka a gefe guda kana iya shaida shi ɗin ba mai girman kai ba ne. Muryar da ya jiyo na sababi yay sanadin lumshe idanuwansa, wanda hakan yay nasarar bayyanar da zara-zaran gashin idonsa da kuma motsawar pink lips nasa tare da sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, yay saurin mayar da p-cap ɗinsa haɗi da daidaita zaman baƙin gilashin fuskarsa, sai fuskan ya ƙara ɓoyuwa ta yanda ba zaka yi saurin shaida shi ba. bugawar sakan ɗaya, biyu, uku ya buɗe idanuwan nasa daga lumshen da suke tare ɗan juyasu yana jin wani sanyayyan abu na biyowa ta babban yatsansa yana shiga jikinsa, kafin sannu a hankali ya ɗaga ƙafafunsa ya fara takawa zuwa ciki. "Kuma fa ba gidan Ubansa ba ne amma ya ke wannan fiffiƙar kya ce da shi za'a raba gado. Ko da ya ke haka ɗan talaka ya ke bai iya shiga rigar arziƙi ba, kuma fa ni nasa Uwassa ta kawowa Dr shi saboda tausayinsa da na ke shi ɗaya a cikin ƴan uba, to fisabillah da ace na kirki ne ai sai ya kwanta ma yace in bi ta kansa in wuce tunda nayi masa rana". Marfu'a taja ɗan gajeren tsaki na takaicin mita da sababi irin na Kakarta sannan ta ce,"Madam na ba ki jakarki ne nayi gaba kya taho?". Madam ta juyo tayi mata wani kallo ta ce,"ki tafi in bi wa? Ba ki kallon wulaƙancin da wancan wargajajjen yaron yay min ne, in sama da ƙasa zata haɗe ai ba zai kaini ba, ki jira ni mu wuce kawai". "To don Allah ki zo mu tafi tun da dai duk maganar da kike bai san kina yi ba, kinsa muna ta ɓata lokaci". Ta faɗa tana yin gaba, Madam ta bi bayanta tana ci gaba da faɗin,"yanzu in ba don kinga na zo gidan ubanki ba ai ba kya na bani Umarni haka ba, kamar dai ba ki san ni na haifi wanda yayi silar zuwanki duniyar ba". "To ni me na ce kuma". Ta faɗa tana ɗaga wayar hannunta, magana tayi na tsawon mintuna uku ta sauke kana ta miƙawa Madam wayar. "Abla ce". Da sauri Madam ta karɓi wayar ta saka a kunne tana faɗin,"Kar ki harhaɗo wasu kalaman ƙaryarki ki faɗa min saboda kare kai, ki baro gidanki kawai ki taho kima mutanen gidan nan da suke riƙe da ɗanki jaje, tsakani da Allah a faɗa miki abu tun daren jiya ki kasa ƙoƙarin bugo asubahi ki taho kije ki duba matacciyar yari
🏠