NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 90 of 97

anyan botikan da ake wanke kalwar yin daddawa, shima babu haske sai na farin wata da ya ratso ta ƙatuwar ɓular langa langar soron, duk da cewar dare ne a lokacin kuma babu hasken fitila amma kana iya ganin ƴan tsirarrun ƙudaje sun yi yaɗo a saman bokitan kalwar. Daga cikin gidan kuwa tsakar gidan yay ƙal, ko'ina fes fes, duk kuwa da rabi da kwatan simin ƙasa ya farfashe. kai da ganin yanda komai yake a killace a tsabtace kasan ba gidan ƙazamai ba ne duk da cewar gidan talakawa ne sosai, ba zaka taɓa cewa gida ne da ya tara iyali da yawa ba saboda tsananin tsabtarsa, kuma da zarar ka zuƙi kyakykyawar iska zaka zuƙo ƙamshin turare ɗan tsinke sama-sama. "Kambun-baka gaskiya ne domin yana faruwa kuma yana iya kai mutum ga mahallaka (mutuwa) saboda tsabar tasirinsa a jikin mutum, saboda haka ya zama wajibi mu nemi kariyar ALLAH Shi kaɗai, sai riƙo da hanyoyin samun waraka ko riga-kafi wadanda suka inganta a shari'ar Allah wajan kare kanmu da iyalanmu daga sharrin Kambun-baka da hassada. Kambun-baka ko Kambun-Ido, Nassi ya yi bayaninsa kamar yadda itama Hassada akayi bayaninta, kuma duk an bayyana mana irin illar da Kambun-baka yake yi ga lafiyar mutane domin yana iya hallakar da mutum ko kaga mutum yayita fama da rashin lafiya mai tsanani. Addini ya koyar da mu hanyoyin da za mu nemi ALLAH ya kare mu daga sharrin dukkanninsu da ma masu yin su gaba ɗaya, mu nemarwa kanmu, iyalanmu, dukiyarmu da duk wata ni'imar da mu kasan muna da ita kariya da tsarin ALLAH Ubangijin kowa da komai kuma mai iko akan kowa. yana da kyau muyi Riga-kafi akan kambun baka, wato (neman kariyar Allah kafin abin ya faru da mutum har yayi tasiri akansa), da kuma yin maganin da bai saɓawa Shari'ar Allah ba idan abin ya faru har yayi tasiri akan mutum. saboda haka mu yawaita karanta Ayatul Kursiyyu da Surorin Falaqi da Nasi musmaman a lokacin da za mu kwanta bacci saboda neman Allah ya kare mu daga sharrin Kambun-baka da na hassada, saboda tasirin sharrinsu a jikkunan mutane ya zarce wanda shafar jinnu ke haddasarwa, ga naci da ƙalata wajen son dauwama a jikin mutum da sanya cututtuka iri-iri, ubangiji ya kare mu da kariyarsa". Maganar da ke fitowa kenan daga cikin ɗaya daga ƙananun ɗakuna biyar ɗin gidan, Kowa a cikin ɗakin zaune yake bisa ƙatuwar tabarmar da ke malale a tsakar ɗakin, kamar dai yanda suka saba kullum a gidan duk bayan sallar isha'i, sun kasa kunnuwa cikin natsuwa suna sauraron karatun da mahaifin su Malam ke musu. Ummaa kishingiɗe a kusa da Malam, sai Iyam kwance gefen Malam ɓangaren damansa Gwaggoje mahaifiyarta na yi mata firfita, Amarya daga bakin ƙofa riƙe da tourchlight mara haske dalilin sanyin batir, sai yaran su a kusa da juna rabin hankalin su akan Malam sauran rabin akan Iyam da bata da lafiya tana fama da ciwon ƙafa da ko takawa bata yi, yayin da duk wani rai zuciyarsa kema Iyam adu'ar samun lafiya domin kusan ita ce garkuwar iyalan Malam Bala Mai Kalwa. Jummai(Iyam) ita ce matar Malam ta farko wadda aka yi aure tun ƙuruciya, tana da bala'in kishin mijinta ga fafutukar sana'a don kusan ita ce jigon kasuwancin kalwar da Malam ke yi a ƙauyuka da birni, ita ce take dafawa tayi aikinta tas shi kuma ya fita da ita kasuwa a siyar. Ƴaƴanta goma banda waɗanda su ka rasu, Hashimu(Yaya Babba) Maijidda(Yaya), Najibu, Aisha(Anti), Rabilu(Yayan Shago), Nazifi(Yaya Ƙarami), Adamu, Lubabatu, Basira, sai auta Fati. Asiya(Ummaa) ita ce ta biyu yaranta bakwai; Basiru, Sadiya, Zubaida, Habiba, Musa, Jabiru sai Garzali. Fauziyya(Amarya) ita ce ta uku yaranta biyar; Radiya, Musbahu, Naziru, Sumayya, Sharifa. "Salamu Alaikum". sallamar da akayi daga tsakar gida taja hankalin su, Amarya ta ɗaga labule ta leƙa bayan ta amsa sallamar. "Nazifi". ta kira yi sunan nasa idonta a kansa. "Na'am, ya naji ku a ɗaki kuma". "ummm yau bamu zauna a tsakar gidan ba saboda sauro". "kuma kinga na sha'afa ban taho da magani ba". yay maganar a sa'ilin da yake ɗiban ruwa a buta yana kaɓe sumar kansa da ƙasan wandonsa. Ta sake cewa,"Ka kira wani a cikin su ya taho da shi, a haɗo da battery wannan yayi sanyi neman mutuwa ma yake gaba ɗaya". "Ai na ma siyo sabuwar tocilayit ɗazu ta caji, na barta ne a gidan su Muntari anjima zan karɓo". "Ciniki aka yi ne naji fa ana ta cajin da tsada". "Wallahi yau kasuwar rake kam Alhamdulillah anyi ciniki dan duka wanda na fita da shi sai da ya ƙare, shine ina tahowa naga fitar na siya dubu ɗaya amma ƴar ƙarama ce". "To masha'Allah, Allah ƙaro kasuwa me albarka, an gode". Ya amsa da amin sannan ya bankaɗa labulen ɗakin ya shiga, ya nemi gefe ɗaya ya zauna yana gaishe da mahaifinsa tare da Gwaggoje da Ummaa, sannan yabi mahaifiyarsa da ido itama yana yi mata sannu da jiki, duk sai sanya masa albarka suke yi shi kuma yana amsawa cike da jin daɗi da farin cikin alfaharin da ahalinsa suke da shi. Kamar ba shine na ɗazu d
🏠