da shi amma duk da haka sautin kukana bai Éuya ba. Lokaci Éaya jikina ya Éauki zafi na kama kyarma dama ni ban iya zazzaÉi ba. A wannan lokacin duk wani mai imani ya ganni sai zuciyarsa ta motsa da tausayina. Haka na ke ta faman zubar da hawaye, ban isa na goge su ba don ina gogewa wasu na sakkowa.
Na daÉe ina kuka don har wajen sha Éaya da rabi, zuwa wannan lokacin kam na fidda ran dawowar Hubbi, banga alamun yau zai kwana a gidan ba. saboda haka na miÆe na shiga banÉaki na wanko fuskata ina hana kaina ci gaba da kukan da baida amfani gare ni, adu'a maganin annoba ita ya kamata in riÆe ba wai damuwa da kuka ba. Ina fitowa na wuce nasa key na kulle Æofa duk da zuciyata na faÉa min komin dare zai dawo, bai da wani wajen kwana a daren nan sama da nan Éin dai da yake Æauracewa, tsakin Æasan maÆoshi nayi, to ina ruwana da dawowarsa, raina Éace na fita falo na bi duk Æofofi shigowa na saka musu maÆulli, zanga ta in da zai shigo, ai sai dai yay kwanan Éakin mai gadi, ba abar banza ba ce ni, auroni yay don yana so ba cusa masa aka yi ba, kuma a gidan iyayena ya Éauko ni ba gidan marayu ba. kamar ma in koma Éakina amma sai na dawo Éakin nasa, na murza key na kashe fitila me haske na bar mara hasken wacce ke kan durowar gefen gado.
Bacci nake ta so nayi amma gaba Éaya na kasa, sai juyi da nake ta faman yi, zuciyata kuma cike da saÆe saÆe, kaina kuwa ya cika fal da tunani daban daban. Ni dai lafiya Æalau muke da mijina, sai dai tun bayan dawowarmu nan gidan da wata bai fi biyar ba komai ya canja na daga yanda muka saba rayuwa, ni da shi kamar abokai haka muke, amma yanzu ya zamar min wani horo har tsoronsa nake yi, magana ma shakkar masa na ke, komai nayi ban iya ba, saÉanin a baya duk abin da nayi ko da bai masa ba zai yaba min kuma yace nafi kowacce mace iyawa, yanzu abu kaÉan zan yi ya zama laifi, zama da shi ban isa ba in ba haka ba ya dinÆa Æunci kenan ni kuma bana son Æuncinsa, hatta makarantar tahfeez Éin da nake zuwa yanzu nema yake ya kashe zuwanta, don duk san da zan tafi sai yayi Æorafi akai, sai yace ai tunda na iya karatun sallah na san wankan tsarki na kuma san zaman aure ya ishe ni, da nayi magana sai yace ai shi ke biyan kuÉin ba wani ba saboda haka yana da ikon ya hana zuwan.
Na kau da tunanin matsalata da mijina, na koma tunanin furucin Yaya na za su sa ya Æara aure, tabbas na sani Æarin aurensa tozarcin da nake sha sai ya ninku, don sai na Æwammaci ina ma ban auresa ba, Allah Éaya ya san irin wulaÆancin da matarsa zata dinga min, balle ta san don manufar da aka aurota, zata goranta min fiye da yanda dangin miji za su min, kuma daga zarar ance ta sami ciki ta haihu shikenan tawa ta Æare, zaman auren sai ya ishe ni, takaicin da zan sha ba daga wurinta ba kaÉai har da shi uban gayyar. ni kaina na sani Hubbi yayi ÆoÆari, ba kowanne namiji ne za'a kai wannan lokacin ace bai yi Æorafi ba, kamar yanda Yaya ta faÉa shekara takwas ban taÉa Éatan wata ba balle azo ga maganar Éari, kuma ko da wasa Hubbi bai taÉa min magana ba, balle ya nuna min damuwarsa ko Æorafi, ni ce Éin ma na ke damuwa, don sau tari har kuka na kan yi, sai yay ta min nasiha yana Æara faÉa min lokaci da rabo ne, idan na Éata masa rai akan nuna masa kar a fara cewa bana haihuwa ya dinÆi faÉa kenan, yace min duk wanda ya fasa faÉar hakan ba ya Æaunar Allah, kai duk wanda ma yay min gorin haihuwa in sanar masa hukuma ce zata raba su, watarana kuwa da nace masa muje asibiti a duba ni bai ci abincina ba. yanzu kuwa yanda muke zaman babu daÉi da shi ai nayi kaÉan in kai masa Æarar Yaya akan cin mutuncin da tazo ta min, kuma ko da ace shima wannan ne dalilin samun matsalarmu ba zanga laifinsa ba, a yanzu kam yana da buÆatar magajinsa, wanda zai Éora akan kasuwancinsa ya kuma mallakawa kadarorinsa. sai dai fa ya tuna ana barin halak don kunya, ko mai zai yi min banda wulaÆanci, don ni na sha gaban ya wulaÆanta ni a rayuwa, domin na masa abin da ko Æ´an uwansa basu masa ba, ya kuma san hakan, sai dai in ya butulce, kuma shi butulci dama ai ba sabon abu ba ne a wajen Éan adam musamman wanda ka yiwa rana.
Haka dai a wannan dare nayi ta tunane tunane, in raya wancan in saÆa wancan, in lissafa wancan, sai dai na kasa warware komai, haka duk na Æosa gari ya waye, ni ba sallah ba balle in yi nafilfili, a haka dai har Éarawon bacci ya Éauke ni a lokacin da ban san ko Æarfe nawa ba.
Washegari ban farka ba sai wajen Æarfe tara da rabi na safe dalilin bacci da wuri da ban samu nayi ba, sai dai Alhamdulillahi isassan baccin da na samu yau Éin da ya kaini har wannan lokacin sai ya zamana ban tashi da ciwon kai da zazzaÉi kamar yanda na saba tashi da su ba a Æ´an kwanakin nan. Sai da na gyara Éakinsa tukunna na fita na wuce Éakina, kafin na haura saman kuma sai da na tsaya na buÉe Æofa saboda zuwan mai yi min wa