NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 89 of 97

inta na matuƙar ɗaukar ido. Waya ce kare a kunnenta ƙirar Iphone 6plus a lokacin ita ake ganiyar tashe, hankalinta ya tattara gaba ɗaya ga maganar da ake yi ta cikin wayar, da dukkan alama waya ce take yi da mutum me muhimmanci a rayuwarta, saboda yanayin tsantsar farin cikin da ya nuna a tare da ita, tun fara wayar bata furta komai ba, sauraren shi kawai take yi cike da annashuwa, a karo na barkatai fuskarta ta ƙara washewa da sanyayyan murmushi me faɗin gaske, take kuwa haƙoran makka guda huɗu dake a bakinta sama da ƙasa suka bayyana, inda asalin kyawun fuskarta ya ƙara fitowa. "Tom shikenan, amma ka sani ina kewarka sosai ya kamata kaji tausayina ka dawo haka". Shiru ya gimla na ƴan sakanni tana ci gaba da sauraron maganar cikin wayar kafin ta sake cewa,"ni dai ba na son wayo". Siririyar dariya ta maye gurbin murmushin da take yi sannan ta ƙara cewa,"To ya zanyi da kai, yanda kaso haka zan so, fatana shi ne ka dinƙa kulawa kaji ko, a tsare mutunci ka kuma ji tsoron Allah a duk inda kake". Ta numfasa tana lumshe idanuwanta tare da cewa,"Allah yay maka albarka, Allah ya kiyaye min kai. Ka kira Madam ku gaisa tana ta min sababi baka ganinta da gashin ido". "Oak to bye bye, i love you so much my son". Wayar ta yanke sa'ilin da take sauke gwauron numfashi tare da kwantar da kanta jikin kujera still idanunta a rufe, yanayinta kuma na canjawa, kamar dai tana ɗauke da wata ɓoyayyar damuwa da ke maƙale can ƙasan zuciyarta, yayinda a gefe ɗaya ta ɗan takure hannunta cikin mayafi kamar me jin sanyi. Kuma kamar a mafarki Mrs Abubakar Jadda taji tayar motar su ta bada sautin ƙara ƙuuuuuuu, ƙarar da ta shiga har can cikin dodon kunnenta, lumsassun idanuwanta suka buɗe a sanda Driver ke furta kalmar Innalillahi wa'inna ilihi raji'un. "Me ya faru Muntaƙa?". tayi tambayar a ruɗe idanuwanta na firfitowa waje, tashin hankali na farat ɗaya na bijiro mata. "Ranki ya daɗe mutum na buge...". Bai ƙarasa maganar ba Mrs Jadda ta ƙwalla ƙara sakamakon tozalin da idanuwanta suka yi akan uban jinin da ya wanke rabin gilashin motar, bata san lokacin da ta fiddo da hannuwanta da ke ɓoye cikin mayafinta ba ta ɗora su aka tana biyo kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Tun driver bai ƙarasa bayaninsa ba ta buɗe murfin motar ta fita a sukwane, lokacin jama'a har sunyi cincirundo a wurin, cike da tsantsar tashin hankali ta raɓa ta tsakaninsu, ganin yarinya kwance cikin jini yasa ta ɗora hannu aka tana salati tare da zube gwiyoyinta a ƙasa. "Wayyo Allah na, jama'a ku taimaka min mu shiga da ita cikin mota". maganar take cikin bala'in tashin hankali mara misaltuwa. "Muntaƙa mu wuce asibiti". ta ƙara faɗa tana kamo yarinyar jikinta. "You are under arrest". taji sautin muryar wani babban mutum a saman kanta, tana ɗaga ido taga ƴan sanda guda biyu suna ƙoƙarin sanyawa Driver ankwa. hankalinta ya kuma kaiwa ƙololuwar tashi, nan da nan ta shiga roƙonsu akan su yi haƙuri su bari tukunna a isa asibiti koma meke da akwai sai ayi. Kuma take anan hannu na rawa ta ɗauko waya ta kira mijinta ta sanar masa halin da ake ciki wanda ta mance da ya ba ya ƙasar ma, da kanta ta ɗauki Sa'ida da ke kwance cikin jini ta sanya a mota, har lokacin salati kawai take yi ganin kamar yarinyar ta rasa ranta, driver yaja motar a miliyan yayin da motar ƴan sanda ta mara musu baya. Babu wanda ya lura da Safiyya da ke ta ruzgar kuka sai a yanzu, tsoro da fargaba da tashin hankalin da ya risketa yasa ta duƙe a wuri ɗaya ta ɓoye kanta a tsakanin cinyoyinta, jikinta gaba ɗaya rawa yake yi tana kiran sunan Sa'ida, ba ita kaɗai ba duk wani me zuciyar imani in yaga mummunan haɗarin sai hankalinsa ya nemi ya gushe. Wani dattijon mutum ya ƙaraso wajenta, yana taɓata ta ɗago a furgice, idanuwanta har sun yi luhu-luhu, bakinta na rawa tace masa,"Sa'ida tah kar ta mutu Baba don Allah kar ta tafi ta barni". Sai kuma tayi shiru tana ƙara fashewa da sabon kuka. "Ya Allah? Ya Allah". iyakar abunda take faɗa kenan ta kasa yin aduar da take son yi. "Kinga kwantar da hankalinki ina ne gidan ku?". Sai ta miƙe a rikice tana girgiza kanta,"ba zani gida ba, ba zani ba hankalin Abbaa zai tashi Ummani zata yi kuka". Kai da kaga yanda take maganar kasan ba'a hayyacinta take ba, tsohon ya riƙeta da kau aka tari me napep suka shiga don nufar gidansu ko na su Sa'ida *YAKASAI B, LAYIN KWALE-KWALE.* Ƙarfe takwas na dare a lokacin, unguwar ta ɗan yi tsit ba kamar da rana ba, gajiyayyen gida ne madaidaici daga ɓarin dama cikin tsakiyar gidaje biyar ɗin da ke jere, irin ginin gidan daga waje jar ƙasa ce sai ciki kuma aka yi ɗan gyare-gyare da bulo sai dai babu filasta, da zarar ka shigo dogon soron gidan guda biyu zaka ji warin daddawa na tashi, soron farkon duhu dunɗum baka iya ganin ko da yatsanka, a soro na biyu kuma zaka yi karo da m
🏠