NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 88 of 97

za'a je da mu Kaduna ba, kinga yanzu na sami dama tun da dai monday ba makaranta". Tayi maganar cike da farin ciki. Haka suka yi ta maganganunsu har sanda muka fito bakin gate. Maimuna na kallona tace,"Yau me zamu siya?". Sanyayyan murmushi me faɗi nayi kafin na ce,"abin da aka saba mana". "Mayyar rake, to ni kam yau siyan rake ba da kuɗina ba, sai dai kowa ya siya abin da ransa ke so". cewar Safiyya tana min harar wasa. Na harareta da manyan fararen idanuwana, ban ce mata komai ba naja hannunta muka nufi titi muka tsallaka. Sai da muka je daidai wajen me rake tukunna muka tsaya, sallama muka masa ya amsa mana, daga yanayin yanda mu ke gaisawa da shi zaka fahimci mun saba da cinikayyar yau da gobe, yana zuba mana raken a leda Safiyya na ta zuba masa zance, shi kuma yana ta biyeta da yake yana da baki kamarta, irin hirar ta su ba zaka ce a wajen siyan raken suka saba ba, Ni da Maimuna dai sai um da um da ke itama irina ce wajen rashin son magana. "Ka biyewa zancenta kana ta zuba raken da yafi ƙarfin na kuɗin da aka baka". Maimuna tayi maganar tana ɗora hannunta a kafaɗata. "Ƙila sai ya kwashe raken gaba ɗaya kafin ya ankare". cewata wadda nayi maganar da zolaya kuma lokacin ya ɗago ya kalle ni. Dariyar da Safiyya ta saki yasa muka zuba mata ido, raken ne a hannunta tana kaiwa baki tana ce masa,"Yaya Nazifi kaga waɗannan ƙawayen nawa haushi su ke ji saboda ina sha su basa sha, kuma fa daga yau kafin na ƙara samun rake me kyau da zaƙinsa har sai nan da kwana huɗu. Don haka Yaya Nazifi rabu da su ka cika mana leda". Na girgiza kai nace da ita,"ke dai ba ki da tausayi".. Kallona tayi tana ɗaga gira irin eehh taji ɗin. Maimuna tace da me raken,"Yaya Nazifi to kaji mara ƙaunarka da rashin tausayinka". Ba tare da ya ɗago ya kalle mu ba yaci gaba da zuba raken fuskarsa na washewa da murmushi. gaba ɗaya yaran jinsu yake tamkar ƙannensa, shiyasa sau tari idan sun zo siya baya basu da wuri sai yay ta laƙai-laƙai don yana jin daɗin hira da su, akwai tarbiya, kama kai da girmama manya. Sai bayan ya ɗaure ledar tukunna ya ɗago duk ya kalle mu kana yace,"ga shi ƙannena asha rake lafiya, yau na san har dalalar yawu za'ai saboda zaƙinsa na daban ne, ai dai sha a hankali kar zaƙin yaywa haƙori illa". Yay maganar da ƙawataccen murmushi kuma cike da zolaya. Ina kallonsa sosai na ɗan waro ido waje na ce,"Naira sittin fa muka baka, wannan kuma ai ya kusan na dubu ko ma yafi". Maimuna ta ce,"wannan sudar ce ai duk taja, ka rage don Allah". Annuri ya ƙara wadatuwa a saman fuskarsa sannan yace,"kar ku damu ƙannena, idan ban baku ba zai zama asara ne, saboda dama da makarantar taku na ke ciniki, ga shi kuma kunyi hutu, kuna ta murna abinku ni kam ina ta fargaba domin zan rasa kasuwa, ko cinikin kwana guda bana so na rasa". Tausayinsa yay matuƙar kama mu, tun ma daga yanayin yanda maganar tasa da ke tattare da damuwa tsantsa. Safiyya tasa hannu ta karɓi ledar tana ta zuba masa godiya. Maimuna ta warce ledan daga hannunta tana faɗin,"ke ba ki da tausayi sam wallahi, hankalin ma ba shi ne da ke ba". Sannan ta dubi me raken ta ƙara cewa,"gaskiya ba za'a yi haka ba, idan ka barsa za'a samu masu siya ko ba'a nan ba". Haka muka yi ta fama da shi akan ko yane ya rage amma sam yaƙi, dole muka haƙura muna zuba masa adu'a da godiya. san da muka juya za mu tafi muka ce ya gaida Antin mu ya amsa mana da tabbacin zai isar da saƙonmu. Tare da ƙara cewa,"Mahaifiyata bata da lafiya don Allah ku sakata a adu'arku ta kullum". "Subhanallah Allah ya bata lafiya yasa kaffara, Allah ya tashi kafaɗunta nan kusa, Allah yasa zakkar jiki ne". Muka haɗa baki wajen faɗar hakan, yaji daɗin adu'ar na mu sosai, ni dai sarkin tausayi har da ƙwalla ta taru a idona, muka masa sallama muka wuce, yayin da shi kuma ya ɗaga bindi(jelar saniya da ake kore ƙuda) yana kore ƙudajen da ke neman kawowa raken hari, gefe guda kuma yana ƙara ɗaga murya da faɗin,"Asai rake, azo a siya rake me zaƙi, ga arha ga daɗi". Cikin waƙa yake ta faɗin hakan domin janyo hankalin abokan ciniki. Ai kuwa abin kamar almara, nan da nan sai ga sauran ƴan makaranta sun zo sun siye shi tas, a lokacin babu abin da ya tuna sai maganar Sa'ida da tace za'a siya insha'Allah, murya a hankali ya ce,"Na gode da adu'arki". Ya faɗa kamar a gabanta, bayan ya gama tattara kuɗin cinikinsa ya tura baron raken ya tafi. *MANDAWARI ROAD, KANO.* Daga cikin baƙar mota ƙirar Rolls-Royce, wata dattijuwar mata ce fara ƙal zaune a bayan kujera yayin da driver ke tuƙata, kallo ɗaya zaka yi mata ka gano tsantsar hutu, natsuwa, kwanciyar hankali da jin daɗi a jikinta, ka kuma san lallai naira ta samu wuri ta zauna. kunnenta zuwa wuyanta da tsintsiyar hannunta da ƙafarta sanye su ke da gwalagwalai na gasken gaske, ga walwalin adon stones na tsadadden less ɗin jik
🏠