NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 87 of 97

surutun da ake yi, wannan dalilin ne yasa wasu ke cewa ina da girman kai wasu kuma su ce saboda ƴar gidan masu kuɗi ce, basu san ni ɗin ƴar masu rufin asiri ba ce, kuma ba komai yasa ake min kallon ɗiyar masu ƙumba ba sai dan zubina da irin shigata ta uniform da jakar makaranta da yanda na ke fesfes, da Yayana da ya ke kawo ni a motar uban gidansa idan ya kai yaransa makaranta, wannan yasa da yawa ke tunanin Abbaana wani Alhajin Neran ne. Sunan Mahaifina Malam Salman, Asalinmu ƴan ƙauyen Madobi ne daga baya kuma karayar arziƙi da mahaifin su Abbaanmu ya samu yasa muka dawo nan cikin kano da zama, tun lokacin ina cikin zani. Abbaana yana kasuwancinsa anan kasuwar kurmi shi da ƙaninsa Baba Sabi'u in da su ke siyar da citta da kayan ƙamshi na abinci, yanzu haka kuma sun koma ƴan tebura anan bakin asibitin Murtala suna siyar da atamfofin leda turmi da falle falle. Mutane da yawa sun shaidi Mahaifina akan kirkinsa da dattakonsa, duk wanda ya san Malam Salman Madobi zai buɗi baki ya ce maka mutum ne na gari wanda ya san darajar ɗan Adam da kyautatawa, ba a taɓa jin kansa da kowa rayuwarsa kawai yake yi shi da iyalansa da ƴanuwansa, ga shi da ƙoƙarin taimako. Mahaifiyata ita ɗaya ce matarsa Sa'adatu muna kiranta da Ummani, ita kanta jama'a na shaidarta da halin kirki da sanin yakamatarta, kowa kuma zai ce maka Ummani bata da wani farin ciki sama da taga ta taimaki wani da ke cikin tsananin buƙata duk da itama ɗin ba shi ne da ita ba, akwai ta da halin kawaici da kauda kai gami da masifaffan haƙuri da ka iya hallakar da ita, amma banda idan aka taɓa ƴaƴanta, duk haƙurinta da shirunta ajiye shi take a wannan fannin ko da za su samu saɓani da mahaifina, akwai soyayya me ƙarfi tsakanin iyayena da kuma fahimtar juna, kyautatawa da rufawa juna asiri. Mu biyar ne a wurin iyayenmu, maza huɗu sai ni ƴar autarsu mace, Sa'id shine Babba wanda mu ke kira da Yashaik saboda tsantsar uztazancinsa amma mutum ne me zafi don shi ya gaji Kakanmu Zakariyya mahaifin Abbaanmu da mu ke kira Kaka, sai Yaya Imam da ke bi masa shima ɗin yana da zafi kamar Yashaik, sai Yaya Al'ameen shi kuma irin Abbaa ne kaifi ɗaya mara magana sosai, Yaya Salman me sunan Abbaa shine na huɗu muna ce masa Abbayo, shi kuma ba gidanmu yake zaune ba a gidan babban wan su Ummani yake, sai ni Autarsu wadda tazararmu da Yaya Abbayo shekaru bakwai ne. Ba masu kuɗi ba ne mu sai dai muna da rufin asiri, Mahaifinmu jajirtaccen uba ne wajen ganin ya tsaya akan dukkan buƙatun iyalansa da kuma ganin ya gina ƴaƴansa kan tarbiya me kyau da kuma basu ilimin arabi da boko gwargwadon iyawarsa, mahaifina bai boko ba amma mutum ne shi me son ganin ɗa na karatun boko shiyasa ya tsaya mana tsayin dka a wannan ɓangaren. Duk Yayyuna maza sun kammala makarantarsu, Yashaik shine me degree da ya kammala BUK in da ya karanci law, sai sauran masu diploma duk polytechnic suka yi, Ya Imam pharmcy Ya Al'amin Science lab, sai dai cikinsu har yanzu babu wanda ya sami aiki. Ya shaik driver ne a wani gida yana kai yara makaranta da kai iyalan gidan unguwa, Yaya Imam kuma ɗinki ya ke yi kuma yana samu sosai, Yaya Al'amin kuma su Abbaa yake bi kasuwa, sai ni yanzu da nake kan karatuna wacca iyaye suka ci burin karatun akaina kamar ni ɗaya ce na fara boko a gidan, duk wani gata ina samu, duk abin da nace ayi min sai an yi min shi duk domin ƙarfafa min gwiwa nayi karatu sosai, domin fatansu da burinsu shine na karanci aikin likita dan tun yanzu mafi yawan lokuta Abbaana da likita yake kirana, ni kuma domin farin cikin mahaifana nasa a raina cewar in sha Allahu zan yi duk iya ƙoƙarina na dage nayi karatu don wanzar da farin ciki bisa fuskar iyayena wanda kuma nasan ta hakanne zan biyasu da kaso babu cikin kaso ɗari na ɗawainiyar da suka yi da ni. Yanzu haka duk wata jarabawa da za'ai ni ke zuwa ta biyu bayan ƙawata Safiyya da ke ɗaukan ta ɗaya. Ina maida hankali sosai a karatuna matsalata ɗaya yaren turanci wato english bai zama akaina balle bakina, ƙila don Malamai ba da turancin suke mana karatu ba ne ko da zasu yi magana da mu, hakan na ɗaya daga dalilin da yasa turanci yay min ƙaranci, kuma shine kawai matsalata a karatun boko, iyayena duk ba su yi karatun boko ba balle na sami taimakonsu, Yayyuna ba zaman gidan suke ba, amma a hakan ma ina ɗan ƙoƙartawa wajen kwaɓawa. Ɓangaren islamifa kuwa nayi saukar ƙur'ani na makarantar allo tun ina shekara tara, yanzu haka kuma na kusa yin sabuwar sauka a islamiyarmu, banda tarin littafan addini da na sauke na haddace su, fagen larabci a bakina kuwa ba'a magana. "Wallahi nayi mugun jin daɗin hutun nan". Safiyya ɗaya daga cikin ƴan mata mu ukun ƙarshe da muka fito daga aji ta faɗa tana gyara goyon jakarta. Maimuna da ke daga gefen hannun hagunta ta ce,"ba ki kai ni jin daɗi ba, saboda dama duk na rasa yanda zanyi da bikin Anty Samira, Baba yace ba
🏠