na fuskanci Nazifi cikin tsananin murna da jin daÉi gami da fashewar kukan tsantsar farin ciki ina miÆa masa kuÉin da cewa,"Hubbi ga shi na ka ne halak malak, Allah ya amsa adu'armu Hubbi yaji kukanmu, Allah yasa Æarshen wahalarka kenan yasa kuma silar Éumbin arziÆinka ne mara yankewa".
Tunanin da na ke ya katse sanda Nazifi ya dawo yana cewa da ni,"me kika yanke? Ko na Æara miki lokaci nan da anjima?. Dubu Éari biyar Sa'ida zata iya isarki taimakawa Æ´an uwanki, idan ba haka ba kuma na Æara miki wata dubu Éari biyar Éin kinga har Umra za ki iya zuwa abinki".
Hannu na saka na goge hawayena da babu su, dan ban san ma sun Æafe ba. Ina kallonsa fuskata a washe na ce,"Na amince, na baka kwanakina na tsawon wata guda bisa yardata da amincewata, ka kula da matarka yanda ya kamata, ubangiji Allah ya bata lafiya".
Murmushi yay na nuna jin daÉi ya ce,"Na gode. sannan ki nemo sabuwar me aiki don Allah saboda kinga Zahra'u ma'aikaciya ce ba zama take yi ba, kinga akwai yiwuwar a sami me tayata aiki a ranakunta".
Nayi shiru ban ce masa komai ba kaina na kan cinyata ina kallon kuÉaÉen, na dakatar da shi daga fitar da yake ÆoÆarin yi, na miÆe na isa gabansa na kama hannunsa na damÆa masa kuÉin na ce,"ba na da buÆatarsu ka Æara a jarinka".
Kallona ya tsaya yi ya buÉe baki zai magana na Éaga masa hannu. "Don girman Allah kar ka ce da ni komai, kaje kawai raina fess ya ke. Daidai ne dai wanda yay ya sani, haka kuma ranar tsayuwa gaban ubangiji na nan tafe".
Dogon numfashi yaja ya sauke idonsa akan kuÉin kafin ya juya ya fita ya bar Éakin hankalinsa kwance. Hawaye ne suka shiga kwaranya a fuskata, sai na duÆe a wajen ina dukan goshina a jikin gado, kafin na Éago kaina na kalli sama na ce,"Ya Allah dukkan abubuwan da suke wakana kana ji kuma kuna gani, ka fini sanin dalilin da yasa rayuwa ke ta Æwallo da ni haka, na sani ba don baka sona ba ne, amma ya ubangijina ka sama min mafita nan kusa, ka sawwaÆe min wannan ÆasÆantacciyar rayuwar da na ke ciki, Ya Hayyu Ya Qayyum ka dube ni saboda tsarkakan sunayenka".
Sannu a hankali naji ina samun salama a raina, kaina har lokacin ina kallon saman Éakin na fara tunano rayuwar baya.
*WAIWAYE, SHEKARU TARA DA SUKA GABATA.*
*MAFARI...*
Ta dabo ci gari, garin da ba kano ba dajin Allah, jalla babbar hausa, yaro ko da me kazo anfika, tabbas a duk inda kaji anyi irin wannan kirarin a kaf faÉin duniya, kasan ba da kowanne gari ake ba face garin kano da ake yiwa laÆabi da tumbin giwa, garin da ya amsa wan nan sunan, musamman idan aka yi duba da yawan al'ummar da ke cikin garin, Æ´an asali da kuma zuwo daga Æabilu daban daban, garin da ya tara manyan Malamai, Æ´an kasuwa, Attajirai, Æ´an siyasa, Dattawan arziÆi, Sarakai, Makarantun boko da na addini, garin da yay shura wajen haÉÉakar kasuwanci da kamfanunuwa.
A tarin unguwannin da ke cikin garin kano, unguwar yakasai na daga cikin manyan anguwanni wadda ake kira da Yakasai rabin birnin kano, idan muka tattara zuwa makarantun da suke cikin garin kano da bamu san iyaka adadin su ba, Shekara secondry school na Éaya daga cikin makarantun sakandire ta gwamnati da ke a cikin anguwar ta yakasai, me Éauke da Éalibai maza da mata. Æaya ga watan octoba ita ce ranar da duniya ta shaida a matsayin ranar murnar samun Æ´anci na Æasa najeriya, a bisa girman ranar ga Æ´an Æasa yasa hutu ke ta'allaÆa ga dalibai, ma'aikatan gwamnati, kamfanunuwa masu zaman kansu, har ma da wasu daga cikin Æ´an kasuwa.
A yau da ya kasance talatin ga watan Satumba, daga cikin harabar makarantar sakandire ta shekara, Éalibai ne ke ta dabdalar shigewa cikin ajujuwa bayan kammala taron asambili da akayi, mafi yawanci fuskokin su Éauke da farin ciki saboda murnar hutun da aka basu na tsawon kwanaki biyu sakamakon murnar zagayowar ranar Æ´anci na Æasa. tun bayan komawa aji kowanne Éalibi ka kalla zaka ga zaÆuwa a fuskarsa na son a buga Æararrawar tashi domin tafiya gida. Æarfe Éaya da rabi dai-dai aka buga Æararrawar tashi, kuma a wannan lokacin ajinmu SS2 mune muka fara fitowa.
Sunana Sa'ida Salman Madobi, shekaruna goma sha biyar a duniya, ina Éaya daga cikin sabbin Éaliban da aka kawo watan da ya wuce da na baro makarantar Aisami na dawo nan ta shekara. Ni Éin ba doguwa ba ce haka kuma ba gajeriya ba ce ina da matsaikacin tsayi me kyau gami da dirarran jiki na jan hankali, ina da cikar halitta ta ko'ina, doguwar fuskata na Éauke da dogon hanci da madaidaicin baki da kuma irin idanun da ake kira da sexy eyes, ba zan ce ni kyakykyawa ba ce can amma dai ba na cikin sahun munana ina da kyawuna daidai misali, hasken fatata ba irin hasken nan ba ne sosai kuma ba baÆa ba ce ni, sai dai na Éauko Éabi'ar mahaifiyata na bala'in haÆuri da sanyi. ban da yawan magana ina son shiru a rayuwata ni kam, dan ina iya zaman minti talatin a wuri ban magana ba duk kuwa irin