fi cikin hankalinsa ya ke? Me ya ke nufi da wannan maganar da ya zo min da ita? Idan ni ce bai buÆata mene dalilin da yasa yake zaman dole da ni? Ina tarin ilimin addinin da na sani a ÆoÆon kan Nazifi?
Dukkan tunanina ya tsaya cak lokacin da Atika ta faÉo Éakin tana haki, Éago idona itama Rumana ta shigo kamar an jefota, kafin nayi tambayar lafiya saboda yanayinsu da ke shaida akwai matsala, sai ji nayi Atika na cewa da shi,"Abba ka je Iyam ta faÉi". Maganar Rumana ta kutsa cikin tata itama tana cewa,"Abba Anti Amarya ce ta mari Anti Fati kuma Iyam taje wucewa hannun Anti Amarya ya bigeta ta faÉi a Æasa tana can ta kasa tashi, Abba ka taso da sauri Anti Fati tana cewa sai sun yi rigima da Anti Amarya ita kuma Anti Amarya ta ce sai ta faffasa mata baki".
Da saurinsa ya miÆe ya fita yaran suka mara masa baya, ni dai idona ya maÆale akan Æofar Éakin ina tunanin na tashi na bi bayansu ko nayi zamana?. Zuciyata ta hane ni da tashi na fita, na zauna cikin girgizar lamarin da Nazifi ya zo min da shi, siyan kwanana! bai damu da nawa hakkin ba!
Jiyo sautin muryar Zahra'u a sama na miÆe na fita, har zan sauka na fasa na leÆa ta saman ina kallonsu. ta na tsaye tasa hannu ta matse bakin Fati wacce ke tsaye a gabanta tana faman matsutsun Æwacewa.
Shi kuma yana tambayar ba'asin abin da ya faru. Ran Zahra'un a Éace babu sauÆi ta ce,"Honey waÉanna irin gidadawan mutane ka ke bari suna shigo maka gida anyhow? Kawai fa na sakko ne zan je wurin Iyam sai na isketa bisa gaban dining tana buÉe flask na abinci, to ni ban san wacece ba tunda ban san face Éin nata ba dalilin da yasa na dakata na iskota ina tambayanta, daga tambaya kuma saboda fitsararriya ce unguwar zoma bata mata gashin baki ba shine take da zarran yi min tsaki tana faÉin na raina mata hankali, Honey can you just imagine Æanwata ta kusan huÉu na min tsaki? Impossible i must teach her a lesson ba na tolerating raini ko kaÉan".
Iyam wadda ta miÆe da Æyar ta ce,"To Zahra'u yi haÆuri ki cikata ai rashin sani ne. kinga kwana biyu bata gidan shiyasa ba ki shaidata ba Amma daga yanzu ki shaida fuskarta Æanwarki ce ita ce Æ´ar Autata, nan take tare da mu ai, ranar biki ne ta koma can gida".
Iyam na yin shiru Zahra'u ta kaÉa kai tace,"Am so sorry to say Iyam amma wannan ba magana kika yi me kyau ba, ba hanyar gyara kuma a ciki, kamata yay ki dubeta kiyi mata faÉa kice ta bani haÆuri before then na saketa, amma ba in Æyaleta ba gobe taji daÉin repeating ma wani, ban sani ba ko halinta ne haka kuma wataÆila tana yiwa matar gidan tana Éauka sai dai ni ba me Éauka ba ce".
Sai tayi shiru tana mayar da kallonta ga Fatin ta ce,"yanzu za ki iyama Yayanki Nazifi tsakin da kika min ko za ki iya yiwa Maijidda(Yaya)? To ki sani ba sa'arki ba ce ni, ke imfact ko da shekaru guda muke da ke tunda har Yayanki ya auro ni na wuci ki min rashin kunya biyayyarki dole garen".
Ta Æyasta yatsu da Æara cewa,"And just for today zan Éaga miki Æafa amma for the next time idan kika Æara wallahi sai na saÉa miki kamanni".
Ta saki bakin Fatin da ke aikin zare ido don da alama ruÆon bakin da aka mata ba na daÉi ba ne. Kana ta koma ga Nazifin tana ce masa,"you just kept silent ka Æi cewa komai. Anyway ka gargaÉi Æanwarka, idan ma akwai wasu irinta to ka tara su kaja musu kunne, ba Æ´ar iska ka auro ba so they have to respect me kaman yanda su ke respecting na ka. Kuma zai fi kyau ku yi shari'a da wadda tayi muku rainonta domin bata yi mata tarbiya me kyau ba ta cuceku".
Ta kalli Iyam ta ce,"ki yi haÆuri bana sane na bigeki ban san da zuwanki wajen ba ne".
Ta na gama faÉin hakan ta bar wajen, kuma yanayinta kawai zai shaida maka zuciya ta kai nesa, ganin tayo saman nayi saurin komawa Éaki. Abin da ya dameni shi ya damen balle na tsaya fassara yanayin da naji akan abin da ya faru tskninsu. Na zauna na saka kuÉin da Nazifi ya bani a gaba ina kallonsu, kallon da yay sanadin haska min hoton wani lokaci can baya shekaru uku da suka gabata wanda ya haska tarrr a cikin kaina, ina hasko lokacin da na fita na bar gida kafin sallar asubahi Nazifi na kwance yana bacci, na fita cikin mamakon ruwan saman da ake narkawa ina me bara gurin ubangiji yasa na zama ta farko a layin da zanje na kamawa mijina, nayi tafiyar Æasa tun daga Yakasai har Nasarawa GRA a Æafa ba tare da na tsaya ko hutawa ba balle tunanin abun sakawa a baki. Na Æara hasko lokacin da na ke tsugune gaban Alhaji Fari ina zubar da hawaye ina shaida masa halin tsananin da muke ciki na rashin cin yau balle na gobe, ina mai roÆonsa arziÆi da ya taimakawa mijina da jari ko da na dubu goma ne ko kuma idan da aikatau cikin gidansa ya taimaka min. Na Æara hasko zuwan Nazifi a lokacin da kuma sanda Alhaji Fari ya Éauko tsabar kuÉi naira dubu Éari biyar ya damÆa su a hannuna ya ce ga shi yayi mana domin Allah. Na Æara hasko lokacin da na juya