o Éakina.
Ita kuwa mun haÉu sau biyu ranar ina kicin ta shigo muka gaisa da fara'arta, tayi min sannu da aiki tana cewa zata tayani na ce mata a'a ba na saka amarya aiki ba ta bari ta gama shan amarcinta, taÆi tafiya ta zauna muna hira da ita jefi jefi babu laifi dai tana da kirki a yanda na fahimta duk da ba lokaci guda ake gane halin mutum ba, har da cewarta yanayina na burgeta ita kam, sai kuma take tambayana ya yanayin cin abinci a gidan ya ke saboda ta san yanda zata tsara lokacinta, hutun sati biyu aka bata a wurin aiki ga shi aikinsu fitar Æarfe bakwai ne kuma sai huÉu ta ke baro office, na faÉa mata duk lokacin da na ke girkina ta jinjina kai cikin harshen turanci tayi wata magana da ban shaida me tace ba haka kuma ban nuna mata ban gane me tace ba Éin.
Rana ta biyu kuwa da ta yini a Éakin Iyam ranar ina yiwa Iyam gugar kaya, suna ta hira da ita akan wata mata da ita Zahra'un tace tana yi musu aiki ita kuma Iyam na cewa ai Æ´ar garinsu ce, shine har ta Éauko dutsen gugarta ta zo muka Æarasa gugar tare duk da Iyam na ta ce mata ta Æyale mini na yi amma tace babu damuwa taga ai na sha aiki.
Haka dai rayuwar taci gaba da tafiyar min zaman gidan Nazifi haÆuri kawai na ke yi domin ba daÉinsa na ke ji ba, duk wasu ayyuka da Éawainiyar masu zama ÆarÆashinsa ni ce, idan na yi kuma kullum a ban iya ba nake a wajen Iyam, wulaÆanci kuwa ban fasa shansa ba sai wanda ya Æaru ita ta min Æ´an uwan idan sun zo suyi min duk da sun rage zuwa yanzu ina ga ko sun bari a gama cin amarci ne. Yawan kuka da sanya damuwa a rai kawai na ragewa kaina saboda gudun kamuwa da wani ciwon, amma haÆurin duk da na ke kam ina yinsa ne saboda abu guda biyu zuwa uku, na farko ina tunawa da rantsuwar Kaka na cewa idan har na fito to ba zan zauna a gida ba sai in ya mutu, da kuma tunanin shin idan auren ya mutu to wa zai auri bazawara irina wacce ke da naÆasun haihuwa? Kuma idan ma auren zan yi wanne kalar mijin zan Æara aura? don ni tun daga kan Nazifi na sare da duk wani namiji da ita kanta rayuwar auren, ga mahaifiyata da na ke ta son gani amma har wa yanzu Abbaa bai sauka akan bakansa ba.
Ranar cikar sati guda da yamma lis ina Éaki muna chart da Safiyya, Nazifi ya shigo, shigowar tasa kuma ta matuÆar bani mamaki da Éaure kai gami da tunanin me ya kawo shi, domin rabonsa da Éakina yau kwana biyar, ni sai naji gabana ma ya faÉi da zuwan nasa. Na gaida shi ya amsa fuska babu yabo babu fallasa, ya ce na tashi na Éauko masa kujerar madubi zai zauna, na bisa da kallo na Æ´an sakanni kamar dai lamarinsa babu lafiya ko kuma yana rashin lafiyar rabuwa da amaryarsa ne oho, na Éauko na ajiye masa ya zauna ni kuma na ci gaba da danna wayata.
Tsakanin mata da miji sai Allah, duk irin yanda na ke matuÆar jin haushinsa da fushi da shi sai yanayin shirun nasa ya dame ni duk da hakan ba sabon abu ba ne, to amma yanayin yanda ya sakani a gaba ne kamar akwai damuwa babba, wani abu da na tuna yasa na Éago na dubesa na ce,"Baka da lafiya ne?". Na tambaya cike da tsantsar kulawa har ina kai hannu na taÉa wuyansa sai dai naji jikin nasa sanyi Æalau.
Ya ce,"Lafiya lau na ke. Ya ÆoÆarinki? na gode".
A hankali na ce,"babu godiya a tsakaninmu. Amma sai dai ban yarda da babu komai Éin ba, ka faÉa min don Allah akwai wata damuwar ne?".
Sai da ya gama Æ´an kamekamensa kana ya ce,"ina so zamu yi magana ne da ke sai dai ban san ta yanda za ki karÉeta ba".
Ina kallonsa sosai da nazari nace,"ka faÉa kanka tsaye ba matsala zan fahimce ka".
Zamansa ya sake gyarawa kana ya miÆo min baÆar leda nasa hannu na karÉa. na buÉe ledar idona ya sauka akan bandir Éin kuÉi Æ´an dubu dubu sabbi masu uban yawa, na Éaga kai na kalle shi ina jiran Æarin bayani.
Ya murza hannunsa kafin ya ce,"Zahra'u ce bata da lafiya don yauma a asibiti mu ka yini, to likita dai yace tana da buÆatar kulawa, kinga Æ´an uwanta duk ba anan su ke ba balle a samu wanda zai zo ya zauna da ita. Na san ba ki da matsala Sa'ida shiyasa na ce zamu yi magana da ke ta fahimta ki faÉi farashin da za ki siyar min da kwanakinki na tsawon lokacin da zata ji sauÆi".
Yay shiru yana kallona, ni kam har ya gama maganarsa kallonsa kawai na ke yi idona waje tamkar za su faÉo, yayin da a wannan lokacin hawaye sun gama wanke min fuska. Murmushi na yi me ciwo sai dai daga ni har shi zamu iya rantsewa tunda muke tare da juna irin wannan murmushin bai taÉa fita a fuskata ba, cikin wani irin murya da ban san ina da shi ba na ce,"uhmm sai kuma me?". Na faÉa ina haÉiye Æullutun wani abu me masifar Éaci.
"Nan dubu Éari biyar ne, idan kinga kina da buÆatar Æari ki faÉa ko nawa ne a shirye na ke da na Æara miki muddin kin amincewa buÆatar da na zo miki da ita".
Na kaÉu da maganar Nazifi sosai, na rasa me zan ma ce da shi kamar yanda na rasa a wanne sahu zan sanya Nazifi, tunani na ke anya kuwa Nazi