ujerar da ke fuskantarmu ni da ita, salati yace muyi ga shugabanmu fiyayyan halitta kafin nan yay bismillah tare da koro adu'oi kana yay gyaran murya ya shiga magana.
"Na san kun san dalilin da ya taramu anan ko da ban faÉa ba. Sa'ida da ina zaune da ke Éaya matsayin matata yanzu kuma na kawo miki abokiyar zama gata nan Zahra'u, bani da wata manufa ta cin mutunci ko tozarci ga Éayanku, Allah ne yay lamarinsa, ya Æaddara cewa zan zauna da ku biyun matsayin matana, haÆiÆa zan kwatanta adalci a tsakaninku iyakar iyawata bisa yanda addini ya ce, sai fatan ku bani haÉin kai".
Ya numfasa kana ya sake cewa,"Sa'ida ke ce Babba wato uwar gida amma a shekaru ke ce Æarama".
Ya dubeta ya ce,"Zahra'u ke ce Æarama a zaman gidan nan amma a shekaru ke ce Babba. Saboda haka kowacce ta kama matsayinta, kuma ina roÆonku da ku kama mutuncinku ku girmama juna ku zauna lafiya, ba na son fitina ba na son tashin hankali, a son raina idan da zaku haÉa kanku ku zama tamkar Æ´an uwan juna zanyi matuÆar farin ciki da hakan, duk da ina ji a jikina ba za ku bani kunya ba".
Kaina a Æasa ina wasa da yatsuna na ce,"in sha Allah ta Éangarena ba ka da matsala na san kai kanka kana da wannan yaÆinin, na maka alÆawarin zama lafiya tare da kai da matarka, zan kuma iya shugabancina matsayina na uwar gida, ina fata itama daga gareta matsayin wacca ta fini shekaru ".
Itama ta ce,"nima ba zaka ji wata matsala ta kunno kai daga gare ni ba. fatana ka zama adalin miji".
Ina kallonsa ya gyara zama ya ce,"sai maganar kwana, Sa'ida ke ce Babba me za ki ce akan hakan?".
Shiru nayi ina ÆoÆarin daidaita natsuwata don kar su fahimci halin da na ke ciki, ya maimaita maganar daidai da buÉe bakina da yawun cikinsa ya bushe sannu a hankali na ce.
"To ni duk yanda ka yanke ba ni da ja akai daidai ne a wurina".
Ya kalleta ya ce,"Zahra'u ke fa?".
Tayi shiru na Æ´an sakanni kamin ta ce,"ba kwana biyu ne ake yi ba dama? amma dai kai ne shugaba kai ya kamata ka yanke".
Numfasawa yay yana dubanmu ya ce,"na yanke kwana bibbiyu na san hakan ba zai sa wata ta cutu cikinku ba. Sannan ke Sa'ida tsawon sati guda za ki kasance a kitchen, kuma idan kinyi girki za ki ke haÉawa ne gaba Éaya har da Æ´ar uwarki. Zata karÉi girki a washegarin rana ita yau wato asabar me zuwa kenan".
Æwalla ta cika idona nayi Æarfin halin maida ita na ce masa,"tom babu matsala, asha amarci lafiya. Allah kuma ya bada ikon yin adalci a tsakani".
Jiki a saÉule na miÆe na fita bayan mun shafa adu'a. Ai fa tun da na shiga Éaki kuma sai kuka haka na dinÆa jin zuciyata kamar zata buga, karo na biyu da na raya dare yanda naga rana don sam bacci yay Æaura a idona, wani azababben kishi na ke ji yana neman haukatar da ni musamman idan na tuna cewa yanzu fa Nazifi tare yake da wata wacca zai yi mata dukkanin abubuwan da yake yi min. da nanata salatin Annabi a raina na samu zuciyata ta fara sanyi har na kwanta bacci lokacin ma gari ya waye.
Kuma da safen shi ya zo ya tashe ni a bacci yana tambayata paracetamol, na ce masa banda shi duk kuwa da ina da shi Éin. zan koma baccin ya ce na tashi inje in Éora abincin kari ko ban duba lokaci ba ne, Zahra'u na da ulcer kuma shima ai na san Æa'idar lokacin cin abincinsa, yara kuma za su tafi makaranta don haka tun muna daÉi da shi kar na tsiri abin da zai zo yana mana babu kyau. sai da ya tabbatar na tashi kana ya fita a Éakin bayan ya kora min kashedin kar na bari Iyam ta buÉe Éaki ban kammala haÉa abincin safe ba.
Cikin kwanakin da suke ta shuÉewa Nazifi da Amaryarsa amarci su ke ta sha na ban mamaki, tun ranar da aka kawota ba ya fita ko'ina idan ba masallaci ba, kullum suna Éaki maÆale da juna, ko masallaci zai je sai ta raka shi har gate, haka duk lokacin da na fito zan sauka sai na jiyo sautin dariyarsu nuni da cewar suna cikin jin daÉin duniyar, dariyar Nazifi da zan ce na kusa shekara ban jita ba, shi yasa na ke baÆin cikin tarewarsu anan saman domin abin da matuÆar ciwo amma haka na ke shanyewa, sai dai dole ya raba mana ko na koma Æasa gaba Éaya ita ta dawo saman ko ni na dawo sama ita ta koma Æasa, don na lura da gayya su ke abin na su.
Rabon da na saka shi a idona tun washegarin kawo masa amaryarsa da ya zo ya bani dubu ashirin ya ce ko da zan buÆaci wani abu da kuma kuÉin makarantar yara idan sun buÆata saboda ba ya son damu kar suke zuwa can wurinsa, tun daga wannan ranar ko abinci na gama zai ce na barsa a dining za su sakko su ci, duk wata magana ta waya mu ke yinta, da kansa zai kira ni da safe mu gaisa, idan bai kira ba kuma shikenan ba dai zan gansa ba ko da inuwarsa tunda aiki ke fitar da ni, da na sauka na gama na dawo Éaki shikenan yanzu sam bana zaman falo gudun Éacin rai, shi kuwa yana Éakin amaryarsa ko da zai fito ma ba sani zan ba, Éakin yaran ya mayar musu Æasa kusa da na Iyam da wataÆila in ke cin darajarsu idan ya zo dubasu ya leÆ