Amarya su ka fara cika gida, ashe a al'adarsu ana zuwa gidan Amarya kafin a kawota yin wasu shagulgulan. lokacin ne nayi sabuwar kwalliya irin ta burgewa nasa danÆareren less Éin wajen Safiyya, kwalliyar Éaukar hankali da shaidawa miji da duk me farin ciki da auren ba gabana aurensu yake ba, har sai da nayi hoto na turawa Maman Yasmin na ce ta aika a nunawa Ummani.
Haka na kame kaina natsuwa ta shige ni, babu alamar damuwa tare da ni, ga wani daÉi da naji duk ramata sai ta Éoye a kwalliyar da nayi, Éangarensu kam sunata shagalinsu na rawar kiÉan Æwarya da guÉe-guÉe da rawar al'adunsu. Da Æarfe shida aka kawo Amarya, kamar yanda al'ada take na kai Amarya ga Uwargida don bada amana haka aka buÆaci da naje na ce da wadda suka aiko a hayo sama nan ne Éakina, Iyam ta Æara dawo da me aiken in sauka na ce da Æ´ar aiken kar ta Æara zuwar min, haka aka kaÉa aka raya naÆi sauka sai gasu don kansu sun hayo anata faman guÉa, dama na san Iyam ce zata ce dole sai dai ni na sauka na samesu tunda ai su sun san abin da ya dace duk da ban san waÉanna kalar mutane ba ne. Aka shigo da ita Éakin ina daga zaune kan gado su kuma suka zauna Æasan carpet. ganin duk iyaye ne na gaida su cikin ladabi suma kuma suka amsa min fuska a sake, ganin da arziÆi da mutunci su ka zo na ba su fuska, nan wata dattijuwa ina ga ita ce Yayar Babanta suka shiga mana nasiha suna cewa ga amanarsu.
Cikin sanyi jiki na miÆa mata hannu muka yi musabaha ina cewa,"ina fatan za ki bani haÉin kai wajen ganin mun zauna lafiya tare da zama kan huÉubar da aka mana yanzu ni da ke".
Ta bani hannu muka gaisa tana shaida min zata ba ni haÉin kai. Da haka su ka yi sallama kuma suka tafi.
Kafin wani lokaci kuma gida yay tsit kowa ya kama gabansa sai bayan isha'i da abokansa da Æawayenta suka wuce bayan an gama siyan baki.
*Æarfe tara na dare.*
Yayan Shago shi Malam ya wakilta a madadinsa na uba akan ya zo yay mana nasiha ni da abokiyar zamana. Haka kuma a gabanmu Malam Éin ya kira Nazifi yay masa faÉa sosai akan ya kwatanta adalci kar yay saken da ranar lahira zai tashi sahun maza masu shanyewar Éarin jiki.
Bayan tafiyar Yayan Shago ni da ita da Nazifi muka shiga Éakin Iyam inda itama tayi nata daidai gwargwado duk da yawancin maganganunta togaciya ne ake yi min. sai dai fa anan na gane tabbas za su janyota jikinsu su mayarta da ita Æ´ar lele ta gaban goshi, don haka sai abin da na ji na gani kawai amma zan jure sai dai ba zan Éauka komai ba kamar a baya.
Sanda na koma Éaki Ina shirin kwanciyar bacci wayata ta Éauki Æara, ban waiwayi kanta ba sanin me kiran daga sautin ringtone, bayan wasu mintuna sai ga shi da kansa ya shigo.
Kallo Éaya na masa na mayar da kaina Æasa ina ci gaba da cire yari da sarÆar jikina. ganin yanda na bawa iska a jiyarsa a Æufule ya kama masifa yana faÉin,"Wanne irin wulaÆanci ne kina jin kirana ba za ki Éaga ba?".
Na kalle shi na ce,"ikon lillahi to ai ban sani ba wayar na silent".
Ya Æara hawa,"to ban hanaki saka waya a silent ba, kika san wa zai nemeki ko abin da za'a faÉa miki".
Nayi shiru ban ce komai ba, don na Æudirci ni kam na daina basa haÆuri akan wani laifi dan na lura hakan ne ke basa damar Æara cin mutuncina son ransa, ya gama faÉan kana yace,"ki fito ki sameni a Éaki".
Yana juyawa zai fita na ce,"zan kwanta ne fa".
Wani wawan kallo ya yarfe min tare da cewa,"ranki zai yi mugun Éaci".
"to wanne Éakin?".
"zan kai sabuwar matata ne tsohon Éaki? Malama nan Éakin sama za ki sameni".
Æasa da murya na ce,"Daga baya kenan anyi sadaÆa da karuwa, baka ajeta sabon Éaki ba ai ka ajeta tsohon gida ko".
Ya jini sarai don ina kallon yacca ya watsa min mugun kallo, na harari bayansa kafin na mayar da Éan kunnayen na yafa gyalena na bi bayansa. Bakina Éauke da sallama na shiga, na samesu kan kujera Éaya ita tana daga gefen hagunsa, na wuce na zauna kan kujerar da ke gefen damansa. lokacin ta Éago kai muka haÉa ido da ita, sai sannan naga fuskarta don Éazu da aka kaita wurina fuskarta na lulluÉe cikin lafaya, ba laifi kam tana da kyau amma ba yabon kai ba tabbas na fita kamar yanda Safiyya ta ce. kallon kusan minti guda tayi min kafin Éauke ido daga kaina, in da na kasa gane manufar kallon nata don har motsa baki tayi ina ga gaisawa zamu yi sai kuma ta fasa, nayi ta kallonta ta gefen ido ina so na karanci yanayin da ke saman fuskarta, a raina na ce Allah ya tura miki aniyarki in har bada nufin alkhairi kika min wannan kallon ba.
Shima ina kallonsa yay min wani kallo, ni na kasa gane musu ko kwalliyar da ke jikina ne ya janyo hakan oho, tunda dai ya san ba shi ya siya min abin da yake jikina ba tun daga sama har Æasa, ko kuma yanda na watsar da shi da lamarin bikin ne ya dame shi ohon masa dai, ga yaga kwana biyu yana faÉa ina mayar masa babu kuma tsoronsa ko shakkarsa tare da ni.
Ya tashi ya koma kan k