NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 81 of 97

da aikin yi kuma ilimina ba na kawo azo aji a gani ba. ga shi yau ina jin na gama karaya akan zan haihu duk da ƙarfafa zuciyata da na ke yi da ƙwarin gwiwar da kowa ke bani, amma ji na ke kaman na tsinke da lamarin don sai na ke ganin binciken likitocin ba haka ba ne. Ta dafa kafaɗata ta shiga kwantar min da hankali akan na daina damuwa sam, shi duk abin da ya faɗa min ya faɗa ne kawai don son ransa da kuma cin zarafi, haihuwa kuma zan haihu lokaci ne. Turo ƙofar ɗakin yasa muka kai dubanmu ga wajen, Nazifi ya shigo cikin kwalliyarsa da alama fita zai yi, kuma da shigowan nasa kamar dama Safiyya a shirye take sai gani nayi ta ɗauki waya ta kara a kunne tana wayar ƙarya da juya baya karma ta nuna ta san ya shigo, shi kuma ya ƙame kamar an danna masa pause idonsa ko ƙifce babu akaina yana kallona tamkar bai taɓa sanina ba ko kamar yaga sabuwar halitta. Murya a hankali na ce da shi,"ina kwana". Maimakon amsa gaisuwar sai ce yay,"baƙuwa muka yi?". Ya faɗa da sigar zolaya saboda adon da yaga na ci. Na kalle shi naga still kallona ya ke ya kasa sauke idonsa, ba sai ya fito fili ya faɗa ba amma har cikin ransa na yi masa kyau ta yanda ko bai faɗa ba fuskarsa ta faɗa. "Kin yi kyau sosai, ashe kin iya kwalliya haka". Hmm kawai na ce ina ce masa,"akwai wani abun ne?". buɗar bakinsa zai yi magana sai ta maƙale, idonsa ya koma kan Safiyya yana kallonta da matuƙar mamaki kamar yanda nima mamakin ya cika ni ina dubanta laɓɓa a sake, na kasa gane wayar gaske take yi ko dai ta ƙaryan ce. "Maimuna kema kin girgiza ashe, ni fa sai da na zo na ganewa idona sannan na tabbatar. Ke banda ma dai jaraba irin ta ɗa namiji banga abun da ya gani ya liƙewa wannan abar ba, ina ga farin bleaching ne ya ruɗe shi abinki da ɗan ƙauye da babu wayewa, ko kuma kuɗinta kin san butulu akwai son abin duniya. amma wallahi ba wai don Sa'ida tawa ba ce na rantse da Allah tafi Amaryar komai, indai fagen tsarin kyan halitta ne da cikar surar da namiji zai so to Sa'ida ta mata fintinkau. Sai dai kawai na gaya mata ta dage da adu'a Allah kawai zai saka mata tsakaninta da Nazifi, ke ni na taɓa ganin mutum mara halacci ma irinsa, baiwar Allahn nan ta aureka tun baka da anini kana yawon tura baro haka ta zauna da kai cikin tsanani amma da ya ke dai namiji ƙanin ajali ne kinga ai da yay kuɗi ya juya mata baya har yana ƙaro aure kuma yana faɗa mata haihuwa yake so na ce bar baƙin munafuki ƙarya yake yi algungumi, banda ma zanen ƙaddara ai wallahi Sa'ida ba ajin aurensa ba ce, matar manya ce ba ta ƙanan ƙauyawa da su ka fito gari kwanan ba shima ya sani, sai dai son zuciya irin nasa na butulalle...". Nazifi yay mutuwar tsaye kawai yana kallon Safiyya da adadin mamakin da ba zai ƙirgu ba, ya sani dama ita tun farkon haɗuwarsa da Sa'ida ƴar adawarsa ce, amma bai tunanin ƙiyayar da take masa har tayi tsamarin da zata dinƙa faɗar maganganu irin haka akansa ba, shi kaɗai ya san me yake ji a game da kalaman nata kamar yanda bai san me zai iya cewa ba don baya da wani kalami a baki. Ita kam hankalinta kwance take ci gaba da wayarta, tana kallon yanda Sa'ida ta haɗe rai tana hararta ta gefen ido tare da zungurinta amma tayi fiƙi taci gaba da maganarta ba zata yi shiru ba kam sai Nazifi ya harzuƙa ya nemi magana da ita tayi masa da hujja ko kuma ya bar ɗakin. "Bari ke dai Maimuna ai ganin Allah ya haɗa shi da mace me haƙuri ne banda haka wannan iskancin ai bai isa yayi shi ba, to ita ɗin ce haƙurinta yay yawa, wallah ba ki ga duk yanda baƙin cikinsa da na ƴan uwansa yasa tabi ta rame ba, shi kuwa wannan shafaffen tumjin nasa ya ɗago, ni so na ke ma zuciya ta zugata ta tayar da aljanun ƙarya ta rufe butulalle a ɗaki tayi masa shegen dukan da ba zai kuma moruwa ba, kuma ta tursasa ya saketa sai ta barwa ɗaya matar ta zo tayi zaman jinya....". Ransa ɓace ya juya ya fita fuuu kamar tashin iska, sai bayan fitarsa kiransa ya shigo wayata da cewar inje in sameshi, ban sami damar maganar da zanwa Safiyya ba na fita cikin hanzari cike da tsoron abin da zai faru. lokacin da na sakko Yaya da su Iyam na falo a zaune ganina yasa suka bini da ido hirarsu ta tsaya, Ko ba su faɗa ba na san sun kaɗu da yanda su ka ganni cikin kwalliya ta kece raini ga shi kuma shi ya sauko daga wajena dole lamarin ya jijjiga su. ina shiga ɗakinsa ya kama balbaleni da faɗa yana cewa in yi gaggawar sallamar Safiyya ta tafi ta bar masa gida idan ba haka ba kuwa ba zai kaffara ba minti goma ta ƙara sai dai na bita mu tafi tare. Ko da na dawo ɗaki na iske har ta miƙe tana ta dariya ranta fess ta ce ba sai na gaya mata saƙonsa ba ta tafi sai wani jiƙon kuma, nima dai na nuna mata bana son ta na magana irin haka akansa tace yanzu ta fara har sai Nazifi ya ɗaiɗaice zata sarara, haka ta wuce ta bar ni raina babu daɗi kuma cike da kewarta. Da la'asar ƴan uwan
🏠