NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 80 of 97

a bi maganar Safiyya da ban tarar da wannan wulaƙanci da cin fuskar ba, dama ai ba wata tsiyar naje yay min ba bangajiya zan masa na kuma tayasa murna, daren nan kam duk iya satar bacci bai yi nasara a kaina ba, haka nayi ta faman juyi da saƙe saƙe cikin raina har aka yi asuba, kuma sai bayan sallar bacci me nauyi ya kwashe ni. Bani na farka ba sai ƙarfe goma da rabi, ina tashi nayi wanka na shirya cikin shiga me kyau, sai dai ko mai ban shafa a fuskata ba. Fita nayi na je ɗakin Iyam na gaisheta, ƴaƴan nata duk sun wuce sai Yaya kawai da sauran baƙinta na ƙauye don ko Ummaa ban gani ba, shi kuwa dama ban ma nufi hanyar ɗakinsa ba don gwara na kama kaina kafin ya kuma yaga ni. Yauma kamar jiya ni na gyara falon da yay mugun kaca kaca ka rantse bai taɓa ganin tsintsiya ba, a kaɗan ɗin lokaci wuri yay fes fes, na shiga kitchen dan ɗora abun kari shima nan na taradda shi an kaca kaca da shi an ɓata uban kwanuka, Allah ya gani sam ban iya ƙazanta ba balle na ɗauke kai na ce zan barwa waɗanda suka ɓata su gyara, balle na san ba gyarawar za su yi ba. Na tattara su duka na wanke su, sai bayan na gama na ɗora jallof na cous cous yanda zai isa har dare ban ɗora wani abincin ba, dan ba lallai idan na hau sama ba na sakko yau za su kawo amaryarsu bana son abunda zai ja min ɓacin rai. Kammala aikina yay daidai da zuwan Safiyya kamar yanda tayi min alƙawari jiya cewar zata dawo yauma ta ɗebe min kewa. Tana ta hararata saboda na sakko nayi aiki muka hau sama, murnar ganinta a yau kam sai yafi min na jiya, saboda tafe take da takardar sakamakon gwajin da aka yi min jiya, wanda ya tabbatar da cewa lafiya ƙalau na ke bani da wata matsala, haihuwa lokacinta ne kawai bai zo ba. Wannan albishir yasa naji kamar anyi min bushara da aljannah, sai lokacin hankalina ya kwanta don ko sanda Nazifi ya faɗa min cewar lafiya na ke ban yarda ba. Ai kuwa take na kira Ummani na shaida mata itama tayi murna tayi murna tare da adua to Allah ya kawo nan kusa. Safiyya ce ta zaunar da ni gaban madubi tayi min kwalliya irin ta zamanin nan da ake yi, kasancewar ban taɓa shafa irin su foundation ɗin ba sai nayi wani kyau na masifa hancina ya ƙara tsayi, kayan da ta siya jiya ta damƙa min tace nawa ne, ba rasa suttura nayi ba haka ba rasa suttura masu tsada nayi ba amma sai naji kyautar ta zamar min ta musamman kuma tafi min dukkan sutturun da na ke da, nayi murna sosai, shaddar na saka wadda ta min masifar kyau, tayi min ɗauri na ture kaga tsiya, ni dai duk sai na rasa ma bakin magana don dawowa nayi tamkar bani ba, ashe ban sani ba haka na ke da masifar kyau, dama an ce in kana da kyau ka ƙara da wanka, ai kam adu'a iya adu'a nata zambaɗawa Safiyya tare da fatan ɗorewar amintarmu. Ta kira min Ummansu mu ka gaisa wacca itama ta ɗauki lokaci tana ce min,"Sa'ida kina jina". Na ce,"Ehh Umma". Ta ce,"Yauwa to ki buɗe kunne da kyau kiji ni, zama da kishiya ya banbanta da zamanki ke ɗaya da mijinki, duk yanda ki ka kai da danne kishinki wataran sai ranki ya sosu kin bayyana shi, haka sai kin matuƙar kauda kai daga kan rawar kansa, abin da zan ƙara maimaita miki shine ki riƙe adua, kyautatawa, girmamawa, ladabi da biyayya tsakaninki da mijinki da mahaifiyarsa. tsafta da caɓa ado gami da iya narka soyayya kar ki bar wata tayi miki zarra, idan kika riƙe waɗannan abubuwan ba boka babu Malam Sa'ida za ki kama miji a tafin hannu ki bar wata ta sakakken baki. Ina kuma shawartarki da yin tsafatataccen kishi bisa sunna ba tare da kin bi hanyar saɓawa mahallicinki ba, zaman kishi zaman gasa ne don kowaccenku so take tayi abin da zata fifita a wajen miji, don haka ki zauna ki karanta hanyar tattaro hankalin mijinku gare ki a ko da yaushe. Tsakaninki da kishiya gaisawa banda zaƙewar shiga lamuranta ko bata fuskar shiga naki lamuran, da zarar kin bada fuskar hakan rainin wayo zai samu mafaka, Ki kama mutuncinki da darajarki ta yadda cacar baki ko faɗa ba zai haɗaku ba don ba ajin mace da kimarta ba ne yin faɗa da kishiya, faɗa da kishiya shine babban abun kunya ga mace ki kuma janyo miji ya ke miki kallon mara wayewa. iya abin da zan ce miki kenan Allah ba ku zaman lafiya kema kuma ya azurtaki da haihuwa me albarka, ki kwantar da hankalinki komai lokaci ne, kar ki saka damuwa tunda har bincike ya tabbatar da baki da matsalar komai kina da lafiyar da zaki ɗau ciki har ki haife". Na ce,"in sha Allah Umma za ku sameni mai aiki da nasiharku ba zan bada kunya ba, Na gode Allah ƙara muku lafiya da tsawancin kwana". Na faɗa ina share hawayena. Ta ce,"amin yasa na ɗauki jikina wataran. Idan kunyi waya da Mamar taki kyace ina gaisheta". Muna zaune da Safiyya tana bani labarin irin wahalar da ta sha a karatu ban san ya akai ba kuka ya ƙwace min ba tare da na shirya masa ba, ina faɗa mata ni yanzu ban san ya zan ƙare ba a cikin gidan nan idan har Amaryar ta zo tunda har yana min gorin ban
🏠