don Allah kar ku saka ya Æara aure, ba don bana sonsa naÆi haihuwa ba, Allah ne bai kawo lokacinta ba ki duba min Yaya, nayi Æaranta ace za'a min kishiya yanzu".
"Mtswwww". Taja wani dogon tsaki mai muni wanda yay duka har tsakiyar ÆwaÆwalwata. tasa Æafa tayi fatali da teburin gabanta, lemu da ruwan da suke kai suka zube akan carpet.
"Sa'ida kici min mutunci ki tsammaci za ki ci gaba da rayuwa ke Éaya a wannan tamfatsetsen gidan, kice ke Éaya za ki mori dukiyar Nazifi?, Bayan kin tauye masa hakki kin hana shi Æ´aÆ´a kice ba zai auro mace mai lafiya ba, ai Æarya kike wallahi...ni bani hanya na wuce ko in bi ta kanki, banza juya kawai marar amfani".
Juya! Kalmar tayi wani tsallen maimaituwa a ÆoÆon kaina, na Éaga idanuwana nabi ta da kallo har ta fice ta bar parlon. Juya! Juya! Juya!, kalma mafi ciwo da raÉaÉi a duk cikin kalaman da ta gaggaya min, wannan hanyar da suka Éullo da ita tabbas zata zama hanyar karayata, bana jin zan jurewa gorin haihuwa, duk haÆurina ba zan Éauki wannan Éangaren ba.
Idanuwana naji su na zugi, duk da ban kallesu ba na san sunyi jajur, sai dai ko kusa ko alama hawaye sun kasa zuba daga cikinsu. Plate da kofunan da ta kifar na tattara na kai kitchen, na dawo Éauke da tsumma na goge lemun da ya zube kan carpet, ac na Æaro saboda wurin yay saurin bushewa gudun kar yay Éoyi.
Cikin Æarfafawa kaina gwiwa na wuce Éakin barcin Hubbi, ina shiga na gyara Éakin kaman ko da yaushe da na saba. na hau sama na kwaso kayan abincinsa na sakko da su, akan tebir na ajiye, haka kuma ban canjawa warm coolers Éin da na tarar ba waje. Ayyuka na daban na tsira duk dan in mance da cin zarafin Yaya, ina ji aka fara kirayen sallar isha'i, ban tsaya da aikina ba naci gaba kasancewar ina cikin jinin al'ada, gyara na musamman na yiwa bedroom Éin nasa a wannan daren, duk wani kai komo da nake maganganun Yaya ba su bar haska min a cikin kaina ba, sai dai ina ta ÆoÆarin kawar da komai Éin domin bana son hakan ya tsaya min a rai, don ko Hubbi ba zai san da wannan labarin ba, shiru shiru har Æarfe tara Hubbi bai dawo ba, kuma bai kirani ba bai tura min saÆo ba.
Æakina na koma na sake wanka don idan ina cikin jini sam bana sakewa, sai in ta jin kaman jikina duk ya Éaci, haka kuma kaman ina ta Æarni.
Murmushin takaici nayi da na kalli kaina a madubi, me yasa nayi wannan saken?, ta ya zan bari jikina yay wannan lalacewar?, dududu shekarata nawa?, ni akaran kaina Æirjina ya daina burgeni balle kuma miji da kansa, ba komai ya lalata ni ba irin saka damuwa a rai, ni da ban taÉa shayarwa ba ai bai kamata ace na bar nonuwana sun zube ba yaraf, bayan na san Hubbi na matuÆar son su, to dole na miÆe tsaye, zan dawo asalina mai cikakkiyar sura ta ko'ina, in kuma fita daga cikin sahun mata masu dugun kai a gidajen aurensu ta Éangaren shimfiÉa soyayyar aure. Sai da na gama kimtsa jikina tsab tukunna na fito Éakin na kulle duk Éakunan sama da kitchen, na sakko Æasa na kashe fitilun falo tare da kunna karatun Æur'ani wanda dama da shi muke kwana kullu yaumin. Agogo na kalla naga har Æarfe goma daidai, tsammanina zuwa lokacin Hubbi ya dawo tun da na jima a Éakina, sai dai ina shiga Éakinsa naga babu alamarsa, kenan har yanzu bai dawo ba, take zuciyata tayi zullo na fara jin tsoro, ban san me yake faruwa ba, fatana Éaya Allah yasa lafiya.
Kasa tsaye nayi na kasa zaune, in kai mari in kai gauro saboda kiran lambarsa da nake yi bata ko tafiya. Tunanin in kira office Éinsa yazo min, sai dai ko da na kira aka tabbatar min da cewa ai tun biyar ya bar office. nan fa hankalina ya tashi, na rasa wa zan kira tun da shi ba wasu abokai gare shi ba, haka yake kamar mace mara son Æawaye.
laluben lambar Æaninsa na shiga yi, ko da ya Éaga bamu wani tsaya gaisawa ba na tambayi ko Hubbi yaje gida, yace ba ya gidan tun da rana da yazo gaida Iyam. muna gama wayar na Æara gwada kiransa, wani sanyi naji a raina da ta fara ringing, sai da nayi kira har sau goma bai Éaga ba sai daga ba ya message Éinsa ya shigo.
"Ba na son damu akwai abin da nake yi".
abin da ya rubuto min kenan, kuma ina gama karantawa na aje wayar jiki a sanyaye, ko ba komai naji dama-dama tun da lafiya yake, sai dai naji babu daÉi sosai, domin kamata yay ace in akwai adalci ya Éaga wayan ya faÉa min uzurinsa, ko kuma ya rubuta min idan babu daman Éaga wayar, amma saboda rashin sanin hakkina da girmama aure yana can lafiya ya barni anan cikin damuwa da tashin hankalin halin da yake ciki, ko abinci na kasa ci haka cikina yake fayau tun ruwan safe da na sha.
gudun tunanin da ka iya rufe ni na miÆe na kwanta akan gadon. Sai dai me? daga kwanciyar tawa na saki marayan kukan da nayi ta dauriyar riÆewa tun tafiyar Yaya, sautin kukan ya cika Éakin, kuka nake kamar wadda aka yowa aiken mutuwa don kawai in samu in fitar da baÆin cikin da ke raina. na janyo filo na toshe bakina