bakin Safiyya zata yi magana nayi saurin saka hannu na rufe bakinta dan na san magana zata yaÉa daidai da tambayar da Iyam tayi. Nayi Æasa da kaina ina cewa,"zamu je dubiya ne Iyam amma babu jimawa zamu dawo".
"To ba za ki je ba dawo".
Safiyya ta juya ta fuskanceta tace,"Algungumin mijin da take Aure ya bata izinin fita bai kuma ba ta umarnin idan wani ya hanata tafiya ta hanu ba".
Raina ya Éaci na ce,"wai mene haka Safiyya".
Ta ce,"ba ta haife ni ba haka kuma ba auren Éanta na ke ba".
Kafin na Æara wata maganar ta figeni mun yi waje, tunda muka fito bata tanka min ba har muka hau napep tace masa jan bulo second gate, Æofar S Fari Beauty Saloon ya ajemu, mu ka shiga ciki, wajen ya mtuÆar haÉuwa don sune lamba Éaya na wajen masu gyaran jikin mata, babban wuri ne na gani na faÉa don suna da reshika wuri wuri a faÉin nigeria, farashinsu kaÉai zai shaida maka ba wajen zuwan Æanan mata ba ne, sai dai fa duk rashin kuÉinki aka miki gyara sau Éaya a wurin ba za ki Æara sha'awar zuwa wani wajen ba gwara kike tarin kuÉi ko da ashirin ashirin ne, wurin na su ba Éoyayye ba ne kana sauka second gate zaka hasko shagon nasu na kallo Hayfa Furnitures.
Da hannu Safiyya ta tankaÉani gaban me wankin kan tace,"don Allah wanke min kan shashashar nan ya fita kiyi masa desng me kyau irin wanda zai gigita miji".
Me wankewar na dariya ta ce to an gama ranki ya daÉe, ni kaina sai da na yaba da gyaran da akawa kaina ashe gashina haka yake da kyau ban sani ba, bayan an gama gyaran gashin aka yarfa min jan lalle da baÆi, hannayena da Æafata suka fito shar da su. duk wannan abun da ake fuskar Safiyya a Éaure don har muka je wani shago a rijiyar zaki ta siya danÆareren less da yaji uban aiki a jikinsa irin wanda ake siyarwa a Éinke da kuma shadda. Da mamakina naga mun wuce asibiti sai da muka je take gaya min za'a min gwajin haihuwa ne, ai ba Æaramin daÉi naji ba don dama tuni na ke so naje asibiti a duba ni to amma ban san me zan ce wa Nazifi ba idan zanje ga shi sam bana son masa Æarya.
Barowarmu asibitin gidan wata Antinta muka wuce, nan ta zaunar da mu da yake sun jima ba su haÉu ba, kuma ni kaina sai naji daÉin zuwan sosai don gaba Éaya ma sai na mance da batun wani biki a gidana balle kishiyar da za'a min. A wannan zaman ne muka yi hirar yaushe gamo da Safiyya har take shaida min ta fara aiki a babban asibiti, na tayata murna sosai na kuma ji ina ma ni ce a matsayin da take, sai dai ni na riga nayi watsi da damata na tarwatsa mafarkin Abbaana. ina mata maganar aure ta harzuÆa tana cewa ita da aure ai sai yanda taga rayuwa ta Æarewa Nazifi, ta yanda ta san Allah zai ci uban nata mijin tun anan duniya kafin aje ga lahira, Anti ta shiga mata faÉan cewa ba duka aka taru aka zama Éaya ba, amma Æ´ar nan furrr taÆi tace ai tunda Nazifi ya zama Éan bantan uba to kowa ma zai zama. Ni dai hmm kawai na ke cewa don na rasa abun faÉa kam, sai gabanin magriba kana muka yi haramar tafiya shima sai da na yi mata da gaske da ta ga na miÆe zanyi tafiyata. Sanda muka koma gida Æ´an taron biki duk an watse sai iya gayyarsu, mutan Abuja ma da su ka je Éaurin aure an dawo don su muka sama a falon, kuma Safiyya bata bani damar tsayawa ba ta figen muka yi sama duk da ina ce mata bari naje Éakinsa na duba ko ya dawo na masa sannu da zuwa.
Bayan munyi sallar magriba ta buÉe mana ledar gasashshiyar kazar da ta siya a hanya da gurasa da tsire, haka ta tilasta min ci da yawa, ba Safiyya ta tafi ba sai bayan sallar isha'i direban gidan Antinta ya zo ya Éauketa, ta tafi tana ta roÆona da Allah akan kar na taka Æafata zuwa Éakin Nazifi a daren yau sai in har shi ya kawo kansa gare ni. Na so na yi yanda ta ce amma saina kasa natsuwa kwata kwata, haka na sakko jiki a sanyaye cikin raina ina tuna shi fa yanzu ba nawa ba ne ni kaÉai mijin mata biyu ne.
Ko da na shiga Éakin nasa na same shi kan gado ya miÆe Æafafu kunnensa maÆale da waya fuskarsa sai washewa take da wani irin murmushi me faÉin gaske, murmushin da ya bayyanar da dukkan hakoransa waje yana ayyana ainihin farin cikin da ruhi da gangar jikinsa su ke ciki. Zama nayi kan kujera daidai da saukar Æwayar idona akan manya manyan kulolin abinci na gani na faÉa sama da guda biyar, sai kuma farantan da ke shaida har anci abinci tunda ga saura nan da aka bari har da su roman ganda manya manya, ba sai an faÉa ba wannan kam daga gidansu Amaryarsa ya taho da shi. Nayi saurin Éauke idona a wajen na mayar kansa ina ji zuciyata na tafarfasa, ya ji sallamata haka kuma ya san da shigowar tawa amma tun duba Éaya da yay min a wulaÆance sai ya watsar, nayi shiru sai a sannan ne na fahimci da wanda yake wayar, Amaryarsa ce tunda gashi nan har yana faÉa mata ba ita kaÉai ce a matse da wayewar gari ba shi kansa ya matsu, hakan yasa na kasa jurewa na miÆe na fita a sanyaye ina mai takaicin rashin zuciya irin tawa, da n